← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 93

Sashe 90

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan hannun shi Bilal ya saka yana murza idanuwan shi kafin ya dan daga kafadun shi cikin alamar helplessness, bai san me zai fada ba, baisan ya zaice ba. Abu daya ya sani, har cikin motar Lagos ya shiga, har zama yayi ya kasa, bai zaice ga dalili guda daya ba, amman nisan awannin da suke tsakanin Kano da Lagos ne sukayi mishi yawa, nisa yake so yayi da gida, nisa yake so yayi da kowa saboda laifn shi da yake ji yafi karfin yafuwa. Nisa yaso yayi musu ko zai rage musu zafin laifin da yayi, amman ba nisa mai yawan wannan ba.

Yana bukatar ya bude idanuwan shi a duk lokacin da bacci ya dauke shi da sanin cewa suna kusa da shi duk da yayi musu nisa, ko kudin shi bai tsaya an mayar mishi ba, tunda zasu iya siyarwa da wani kujerar, lokacin ana ta saka kaya, jakar shi kawai ya dauka, daman dayar tana goye a bayan shi. Hotel ya kama, wayar shi kasheta yayi, satin shi biyu a hotel din batare daya fito ko ina ba, jinya yayi ba karama ba ta rashin su, ta nisa da gida, ta tunanin halin da kowa zai shiga. Ranar daya fita kuwa sabon sim ya siya ya saka a wayar shi ya adana wancen.

Yasan kudi zasu kare mishi, dole yana bukatar neman wata hanya ta samun kudi, sana'ar karfi ce karshen abinda zaiyi, ba zai karya ba in ba dole ta kama mishi ba ba zai iya ba. Bai saba wahala ba, baima san wani abu wahala ba tun tashin shi. Su Abbu sun tabbatar da hakan, unguwannin da ko da wasa bai tabajin su Ayya na kaiwa ziyara ba nan ya fara nufa yana shiga duk wata private school da yaci karo da ita, bai boye musu cewa shi din bashi da takardu ba, amman yayi karatu har zuwa shekarar shi ta karshe, ya dai ce musu matsala ce ta saka shi ajiyewa dole, fiye da makarantu biyar sun so rike shi, musamman bayan sunyi mishi gwaji, amman sai suka so yin amfani da wannan damar ta cewa ba shi da takardu wajen biyan shi kudin da basu taka kara sun karya ba, haka yaci gaba da yawo wajen sati daya, kafin ya samu wata makaranta a cikin rijiyar lemo can wajen layin masallacin espa.

Da yake shugaban makarantar musulmi ne, mutum mai matuqar kirki da sanin ya kamata. Har kara ma Bilal din kudi yayi daga baya ganin yana da sani ta bangaren addini, makarantar kuma boko ce hade da islamiyya, sai yake koyarwa a duka bangarorin biyu. Anan cikin rijiyar lemon ya samu karamin gida daki biyu ya kama. Watan daya duba account balance din shi yaje cire kudi yaga sun karu sosai, daga farko ya dauka ko wani yayi kuskuren tura mishi kudi, tunda layin da yake ganin alert yana kasa, amman yakan duba ta email din shi. Hakan yayi, yaga Rayyan ne

"Hamma, nauyin zai mun yawa....dan Allah Hamma"

Shine kalaman da ya dinga furtawa yana maimaitawa, yayi nisa da sune dan su sami sauki, ba dan ya kara dora musu wata wahala ba. Sai dai ba zaiyi karya ba, kudin suna taimaka mishi sosai da sosai. Ba zaice ya nemi wani abu ya rasa ba, iya cikin shi da abinda ba za'a rasa ba, kudin ya ishe shi har ma yayi mishi yawa. Watanni shidda ya dauka cir kafin mafarkan kowa na gidan ya fara damun shi, rana daya ya wayi gari yaji kewar su ta danne mishi kirji, numfashin kirki ma baya iyawa, shisa ya dauki sim din shi ya saka a wayar, hankalin shi rabi da rabine ko da yaje wajen aiki, ba zai manta uzurin rashin lafiya daya bayar ba ya kama hanyar gida, a hanya ya tsaya ya siyi kati ya saka a layin

"Watakila ko dan babu kudi shisa sako ko daya bai shigo ba"

Ya fadi a zuciyar shi, har wajen sha biyun dare yana kallon wayar

"Kirana kawai zakuyi, zan dawo gida"

Tunanin da yakeyi kenan a cikin kan shi har wayewar gari inda ya zare layin daga wayar shi, daga lokacin ne kuma ya sami karamar waya ya siya inda ya saka layin a ciki. Daga ranar kuma ya fara kunna wayar daga safiya zuwa karfe biyu na rana, wani lokacin ma yana kwana bai kashe ba, banda yan MTN babu wanda yake kiran shi, ko sako yaji ya shigo sai zuciyar shi ta doka, sai dai idan ya duba yaga ko bankin shi ko MTN din ne dai. Fushi sukeyi, ya san fushi sukeyi da shi shisa basu kira ba, laifin shi ya so wankewa da karin wani laifin na tafiya, amman bai taba cire rai ba, yasan zasu kira shi, komin dadewa zasu kira.

Ba zaice ga yanda yayi shekarun nan batare da su a kusa da shi ba, bai san me ya rike nutsuwar shi har haka ba. Yau din ma kamar kowacce ranar karshen mako, zaune yake bayan ya karya yana marking assignment din yara, sai wasu azuzuwan da test ne yayi musu kasancewar an kusan fara jarabawa yaji karamar wayar shi na ruri, karamin tsaki yaja kawai yana cigaba da abinda yake yi saboda yasan MTN ne, su kadai zasu fara kiran shi kamar suna bin shi bashi. Wutar da aka kawo yasa shi daukar babbar wayar shi da ba wani amfanin kirki yakeyi da ita ba, tunda ya koyi rayuwa babu kafar sada zumunta, abinda bai taba tunanin zai iya yakicewa ba.

Sai dai ya iya karfin halin barin su Rayyan ma, ballantana wani whatsapp, hannu ya mika ya dauki karamar wayar ya duba yaga ko akwai sauran caji tunda ya kwana wajen hudu bai sakata a caji ba, latsawa yayi kawai dan sabo yana shiga yaga missed call din da yasaka shi mikewa babu shiri ganin lambar Rayyan da ko a bacci ya ganta zai ganeta. Mukulli kawai ya dauka yana saka takalma a kafafuwan shi, zai iya tuna ya kulle gidan, amman ko mai mashin daya sauke shi a kofar gidan su, hannu kawai ya saka a aljihun shi yana lalubawa ya kuwa samu dari biyu ya mika mishi, zuciyar shi yake ji a tafukan kafafuwan shi a duk takun da yakeyi, shisa yake jin kafafuwan sun mishi wani irin nauyi na ban mamaki.

Basu kara nauyin ba sai da ya hango Rayyan, wannan karin tsallen da zuciyar shi tayi a ko ina na jikin shi yake jin dokawar ta, shi da kan shi bai gane muryar shi ba lokacin daya kira Rayyan din, yanzun ma da suke tsaye ji yake kamar mafarki, kamar bashi bane tsaye a gaban Rayyan da yaga kamar bai canza ba a shekarun nan, yana nan yanda ya san shi, sai dai akwai wata natsuwa da yake gani a fuskae Rayyan da bai taba sanin yana da ita ba haka.

"Me zance Hamma?"

Wannan karin rashin madafar a muryar Bilal ya fito

"Baku kirani ba. Hamma kirana kawai zakuyi kamar yau..."

Da rashin fahimta Rayyan yake kallon shi, saboda baya gane abinda yake fadi, baya ma gane abinda yake ji balle kuma zantukan Bilal din, wayar shi Bilal ya daga duk da baya tunanin Rayyan yana ganin screen din saboda kankantar wayar

"Baku kira ni ba, kai ma baka kira ni ba, ni din mai laifi ne, ban san ya zan nuna fuskata ba baku neme ni ba Hamma"

Dariya Rayyan yayi mai sauti yana kallon Bilal din sosai, duk shekarun nan jira yake yi su kira shi kafin ya dawo, sau nawa yana daga wayar shi ya danna lambar Bilal din yayi ta kallon ta, saboda yasan koya kira a rufe zaiji ta, kiran ba zai mishi amfanin komai ba sai karin daga mishi burin cewa bai rasa Bilal din ba, daga baya ma daina dannawa yayi saboda yasan an siyarwa da wani daban lambar, balle harya gwada kira wani ya dauka ya tabbatar mishi da yanda ba Bilal kawai ya rasa ba har lambar wayar shi ma ta tafi.

"Ta ya zamu fara kiran ka idan duka muna tunanin ka rasu?"

Kallon shi Bilal yayi, saboda maganganun shi sun daki kunnuwan shi da wani yanayi mai wahalar misaltawa

"Motar da ka shiga, babu wanda ya fita a motar, da alama kai ka dai ka fita"

Kai Bilal yake girgizawa Rayyan

"Ta ina zamu kira ka Bilal? Ta ya zaka jira kiran da bamu san kana jira ba? Kiran da banda karfin zuciyar yin shi in sake jin wayarka a kashe..."

Kan dai Bilal yake girgiza mishi

"Na shiga motar da kuke tunani, amman ban zauna ba, na kasa yin nisa mai tsayin wannan... Ban zauna ba Hamma"

Bilal yake fadi cikin tashin hankali, yana jin zuciyar shi kamar zata tsaga kirjin shi ta fito da halin da yake hasaso sun shiga, sanin tafiya yayi daban, amman tunanin ya rasu? Tunanin sun rasa shi gabaki daya, baisan ta inda zai fara hasaso tashin hankalin su ba

"Ayya fa?"

Ya tambaya, kallon "Sai yanzun tunanin ta yazo maka? Sai yanzun kake tunanin halin da ta shiga? Me yasa kafin ka tafi bakayi tunanin ta ba?" Rayyan yake yi wa Bilal din. Kafin ya dora wasu tambayoyin akan harshen shi yana jifan Bilal da su

"Me yasa zaka tafi? Nace ba zan yafe maka ba na sani, amman me yasa zaka tafi? Idan baka duba ni ba, me yasa zaka bar Ayya? Me yasa ka tafi Bilal?"

Ba tambayoyin Rayyan bane suka saka hawayen shi zuba, yanayin yanda yayi mishi sune, muryar shi, yanayin da yake kan fuskar shi da cikin idanuwan shi

"Hamma..."

Kai kawai Rayyan ya girgiza mishi yana juyawa, komai ne yake dawo mishi sabo, duk wani ciwo da yake tunanin lokaci ya dishe mishi zafin shine yake budewa yana dawowa sabo fil, kiran duk da Bilal yake mishi baisa ya juya ba. Amman takun tafiyar Bilal din da yake bin shi a baya jinta yake har cikin zuciyar shi. Kan shi tsaye bangaren Ayya ya wuce, bata ma falon sai Huda da tana ganin shi tace

"Hamma, yanzun naga Nur, nace tare kuka zo tayi banza ta kyaleni, ko kallona fa batayi ba ta wuce tana neman Ayya....har..."
Chapter 90 · 0% Book details