← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 93

Sashe 57

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bacci ta sake komawa bayan tayi sallah, babu ciwon kan, sai zazzabi kadan da kuma duniyar da batajin dadin ta. Ta so ta dan watsa ruwa amman batajin karfin jikinta. Sai kuma lokacin Anisa tace zataje ta dawo, sanda ta dawo ta soyo mata kwai ta taho da ruwan zafi da kayan shayi data kullo su a ledoji. Sai kofi da cokali. Layla ta san tana da lakca shisa ta matsa mata ta tafi

"Baki ga naji sauki ba, kinga an fara test, ana iya yin wani babu tsammani, kuma idan akwai wani abin zan kira wayar ki ai"

Bataso tafiya ba

"Dan Allah ki tafi, ni bacci ma zan koma"

Sai da ta ga Layla din ta juya kwanciya da yake tun wajen karfe hudu da aka cire mata ruwan daya kare sai suka barta ta huta. Tafiya Anisa tayi don tayi shirin tafiya aji. Lokacin ne wayarta ta soma ruri, ganin Abbu a rubuce yasa cikinta hautsinawa, sabon zazzabi na dirar mata, amman idan taci gaba dakin daukar kiran su hankalin su zai tashi fiye da yanda tasan ya tashi. Batayi magana da Bilal ba, amman idan yaji zabinta na barin komai daya faru a tsakanin su tasan zai amince. Ta san boye komai shine saukin su, in ma sunce zasu fada ta ina zasu fara?

Kuma jiya Rayyan yace yana son ta, shi ya saukar da zazzabinta ya rage ciwon kan da takeji, ya rage kusan rabin damuwarta, shi ya bata kwarin gwiwar daga wayar Abbu har tana amsa sallamar shi

"Layla... Ya jikin naki?"

Numfashi ta sauke, kenan sun san bata da lafiya, tana da tabbacin Rayyan ne ya fada musu

"Da sauki Abbu, ina Mami?"

Ta tambaya

"Gata nan tana jinki, yanzun zamu karaso ma, muna Zaria"

Mikewa zaune tayi wata irin zufa na karyo mata, kanta take kallo tana neman alamun da zasu iya nunawa Mami wani abu ya faru da kuma yanda zatayi ta boye

"Hello..."

Abbu ya fadi jin tayi shiru

"Sai kun karaso Abbu"

Tayi maganar tana mamakin yanda akayi muryarta bata rawa. Sauke wayar tayi daga kunnenta, tabbas idan bata saita nutsuwarta ba Mami zata gane akwai wani abu, karyar da zatayi take nema amman gabaki daya kanta ya kulle, tana nan zaune tana tunani sai ganin su tayi sun shigo. Wani kukane yake neman taso mata da ta hango Mami, saboda a tsayin rayuwarta Mami ce komai nata, duk da Abbu ya zame mata mahaifin da ta rasa, Mami daban take, ko da tana cikin damuwar da bata taka kara ta karya ba haka takan shige jikin Mami tana mata sangarta, Mamin kuma zata biyeta ta lallasheta a wasu lokuttan in ta kula da gaske akwai damuwa a tattare da ita.

Yanzun ma kasa daurewa tayi, suna karasowa ta zagaya hannuwanta tana rike Mami, hawaye masu dumi na zubo mata, numfashi sosai Mami ta sauke tana samun natsuwa da taga Layla din, dagota tayi daga jikinta tana zama gefen gadon

"Menene na kukan kuma? Ai gamu mun zo"

Mami ta fadi muryarta na rawa, har cikin ranta take godewa Allah da yasa babu abinda ya sami yarinyarta. Jikinta ta taba tanajin da zazzabi

"Kin ci abinci?"

Kai Layla ta girgiza tana share hawayen da yake fuskarta

"Gashi Anisa ta kawomun shayi"

Abbu ta kalla

"Abbu"

Murmushi yayi

"Sai yanzun kika ganni?"

Dariyar karfin hali Layla tayi, amman tanajin yanda wani abu yake budewa a cikin kirjinta. A lokutta da dama na rayuwarta ta saka kafa tayi fatali da duk wata tarbiya da suke dorata a kai, saboda tana ganin a kasan kaunar su akwai rashin wayewa, akwai dogon bambancin da take gani tsakanin yanda sukayi tasu rayuwar a baya da kuma yanda rayuwa take tafiya yanzun.

"Babu wani abu zamani Jabir, duniya bata canzawa, mutanen cikinta ne kawai suke canzawa, bambancin yanda mukayi tamu rayuwar da yanda ku kukeyin taku yanzun shine zabi..."

Mami ta taba cewa Jabir sanda yake mata maganar cewa zamanin su da kuma na yanzun daban ne, sun jima suna dariya bayan Mami din ta tashi, a ganinsu ba zata taba fahimta ba, ashe sune basu fahimceta ba, akwai tarin ma'anoni a kalamanta, ko kan maganar kaya da take yawan yiwa Layla din, ta dauki shekaru tana mata fada da nasiha a kai sai yanzun take kallon abin da kalar idanuwan da Mami ta ke taso ta duba. Abubuwa da damane suke ta mata yawo. A cikin abinda ya faru a kwanakin nan biyu ta daina kokarin gane ya akayi abinda ya faru ya faru, saboda bata da wannan amsar, ta dai san babu tirsasawa a al'amarin saboda rudanin da take ciki shi Bilal yake ciki.

Abu biyu zuwa ukku ta sani a yanzun, kafafuwanta ta dauka taje gidan su Bilal, da ta tura taga basa nan zata iya juyawa kamar yanda Rayyan ya taba balbaleta da fadan shi harda rankwashi da ta kai musu abinci taga basa nan ta zauna tana jiran su. Yana shiga ya ganta ya rankwasheta yana kama hannunta, dakyar ya bari ta saka takalma

"Idan kika ga bama nan karki kara zama, baki da hankali ke kam sam ko? Baki san maza bane kawai a gidan? Karki kara zuwa ki zauna idan ni ko Bilal bama nan, dakin tura dakin ki juya ki tafi gida, kina jina?"

Harya rakata bai daina fada ba, da tabi maganar shi, tunda ko suna nan din baya bari ta zauna. Tana shiga zai mike, shisa ta daina sallamar masu abin hawa. Ko a ranar dan tana tsammamin zata same sune, shisa ta sallami mai napep din. Tunda tana son taga tafiyar Rayyan din in yaso ita da Bilal sai su koma makaranta. Amman da ta juya da taga basa nan, da ta janyo dakin ta juya, sai ta zabi ta shiga ciki harta zauna. Idan Mami taji tana da yakinin tambayar farko da zatayi mata shine

"Me kikaje yi gidan su Rayyan?"

Kuma bata da amsar wannan tambayar, uzurin duk da zata bayar a cikin kanta ma bamai karbuwa bane ba. Akwai abubuwa da yawa da ta fahimta yanzun, abubuwan da take dauka a matsayin takura da batasan kariya bane a wajenta. Tun jiya take daukar alkawurra kala-kala, ciki harda sauraren duk wani abu sa Mami zata fadi da kuma yin aiki da shi, dan taga alama maganganun na da karfin kareta daga abubuwa da dama. Da ta saurare su da bata zo inda take yanzun ba, amman tana jin kamar lokaci bai kure mata ba. Ganin Mami din ya sa duk ta kara jin karfin ta ya karasa karewa.

Ita ta taimaka mata taje bandaki ta kara kuskure bakinta suka dawo, likita ne ya shigo yin round da yake dakin su hudune a ciki, akwai dai yar tazara tsakanin wani gadon zuwa wani, kuma akwai wasu gadajen da babu kowa, su Abbu fita sukayi sai da aka gama sannan suka dawo.

"Wai idan naci abinci sai a kara sakamun ruwa yace, zan kara kwana sannan su sallameni"

Kai Mami ta jinjina mata, tana daukar kofin da yake cikin kwandon da Anisa ta kawo. Shayin ta hada mata tana dauko yar kular ta bude mata wainar kwan, ta fara cine Abbu yace

"Bari in koma wajen su Bilal in kara ganin ya nashi jikin tun da ita ta samu"

Kai Mami ta jinjina

"Kayi mishi sannu"

Dubu sha biyar ya kirga ya bata yana barin biyar a jikin shi, karba tayi hadi da yin godiya, ita da Layla suna mishi addu'a da bada sakon yiwa Bilal din sannu da jiki. Daurewa Layla tayi ta shanye shayin tas, wainar kwance ta kasa cinyewa, karfin hali takeyi kar Mami ta fahimci wani abu, hira sukeyi a hankali, har akazo aka kara mayar ma da Layla ruwan, da yake an saka allurai a ciki, baccine ya dauketa. Mami na nan zaune Anisa ta dawo, gaisawa sukayi ta wuce da fadin zata dora girki

"Kina ta shan hidima, idan akwai waje me kyau ki siyo kawai Anisa"

Mami ta fadi tana bata dubu uku, tasan duk tsadar abincin dai nasu su uku ba zai wuce dubu dai-dai ba. Karba Anisa tayi dan kuwa da gasken a gajiye take jinta. Saida tayi sallar azahar sannan ta dawo, tana kawo musu nasu sallama ta kara yiwa Mami saboda tana da wata lakca har karfe hudu. Har tana saka Mami yin tunanin ya za'ayi yara ba zasuyi rashin lafiya ba da wannan zirga-zirgar da sukeyi. Ga shi saika dawo daga daukar darasi zaka fara neman abinda zakaci

"Kullum daman sai kun dawo sannan kuyi girki?"

Ta tambayi Layla cike da damuwa bayan ta tashi, dariya Layla tayi

"Muna ci a cikin makaranta, mun mafi yin abincin dare dai, ko da safe mu girka kafin mu fita idan babu lakcar safe"

Numfashi Mami ta sauke, babu wani abu a karatu nesa da gida banda wahala a nata ganin, saboda idan a gidane zakaje ka koma kuma ka sami abinci a girke, shisa duk in suka dawo sai taga sunyi zuru-zuru. Ayita maganar wahalar karatu ce, nan kuwa harda kujuba kujuba da rashin samun abinci akan lokaci

"Kinga da kinyi zamanki BUK kikaqi"

Murmushin Layla tayi mai ciwo, saboda a karo na farko maganganun Mami din sun zauna mata, da ta zauna a BUK din abin nan da bai faru ba, saboda ina taga Bilal din ma in ba hutu ya dawo ba? Batason tsaurara tunani a kai har mami ta fahimci akwai wani abu

"Kai Mami, baki ga su Hamma ba har sun gama, sauran fa sati uku a fara jarabawa...da an dawo an karayin wata nima aji uku zan shiga"

Kallonta Mami tayi

"Babu in shaa Allah kamar kece da rayuwar"

Dan murmushi ta sakeyi

"In shaa Allah"

Ta fadi tana saka Mami fadin

"Hmm..."
Chapter 57 · 0% Book details