Sashe 87
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ga amanar 'yata nan Rayyan, kayi hakuri da ita a lokacin da zata kuskure maka, ka kauda kai a lokacin da nata idanuwan suka rufe ko da kuwa kaine da gaskiya. Zamana da Ayyar ka bai kawo mu yau ba sai da hakan, hakurin da ake jaddadawa mata mu ya kamata a jaddadawa shi, kayi hakuri, kayi hakuri da duka halayenta, karka cutar da ita, kanwar ka ce ita kafin yanzun ta zama matar ka, ka kula da ita kamar yanda kake so a kula da su Rukayya, ka kare martabar ta kamar yanda zaka so a kare ta yaranka wata rana, karka daga mata murya kamar yanda ba zaka so in dagawa Ayyar ka ba"
Idanuwan shi Rayyan ya saka cikin na Abbu kafin ya dan daga kan shi, yana jin nauyin maganganun Abbu din da girman amanar daya dora mishi.
"Zanyi magana da yarinyata Rayyan"
Abbu ya fadi yana saka Rayyan din mikewa ya fice daga dakin, zuwa lokacin idanuwan Layla cike suke taf da hawayen da suka fara zubo mata
"Abbu..."
Ta kira muryarta na karyewa, wannan karin ba da kukan da takeyi ba, da tarin kaunar da takeyi mishi, da godiyar da bata da kalaman da zata fara yi mishi ita, batama san ta inda zata fara ba, saboda akwai tarin abubuwa da suka fi karfin godiyar. Kallon ta Abbu yayi yana jin yanda zuciyar shi ta karye, su duka yaran yake kula da yanda girman daya fi shekarun su ya saukar musu, yanda tarbiyar da rayuwa take bawa dan adam ta saka sukayi wani irin laushi da kalaman shi zasu dauki wani lokaci basuyi musu wannan tasirin ba.
"Kar zamana da Mamin ki ya zama tsanin da zaki gina taki rayuwar auren, ba lallai tazo iri daya da tamu ba, sai kinyi hakuri Layla, kinji? Zaki iya kiran mu ko da yaushe, kin san haka ko?"
Kai ta daga ma Abbu wasu sababbin hawayen na kara zubar mata. Da kan shi ya mike yana kamata ta mike, kuka takeyi sosai dan zaka iya fahimta da yanda jikinta yake bari. Abbu ya rakata har wajen mota inda ta toge tana girgiza mishi kai, dan wajen shi aka fara kawota
"Mami... Abbu...Mami na"
Layla take fadi tana jin wani irin tsoro na ratsata. Zama matar Rayyan ne mafarkin ta, amman bata dauka haka zai kasance ba sai yanzun da zata bar gida, yanzun da bata san me rayuwa ta tanadar mata a cikin gidan shi ba, musamman yanda zataje mishi din, tana da yakinin shima ba haka ya hasaso auren shi ba, bai hango bayan mata harda yarinya za'a tafar mishi da ita ba, shine abinda ya kara gigita lissafinta. Kafin Abbu yayi wani motsi Layla ta kubce daga rikon shi tana bude lullubin da yake kanta saboda bata ganin hanya sam, da sauri gudu-gudu take nufar bangaren Mami, tun daga bakin kofa take kwala mata kira harta shiga can cikin dakin inda Mami take zaune a gefen gado tana sharar kwalla.
Tana daga cikin mutanen da suke ganin ranar da ka aurar da 'ya ya kamata ya zamana rana mai girman gaske a wajenka, bata ga dalilin da zai saka ta fara kuka da za a kai mata yarinya gidan aure ba, tunda abin farin cikine, sai da ta wayi gari safiyar yau ko giccin Layla ta gani sai taji idanuwanta sun cika da hawaye. Saima da Jafar ya shigo bayan an dawo daurin aure yana kamata ya jata dole akayi hotuna da ita. Ta ga da gaske dai auren Layla aka daura, da gasken tafiya zatayi, balle kuma da aka shigo aka fita da ita, tana zaune ne tana jiran su tasan za'a kawo Layla ace tayi mata nasiha.
Bata tsammaci ganin Laylar ta shigo a firgice haka ba
"Mami..."
Layla ta sake kira a karo na babu adadi ta karasa cikin dakin tana fadawa jikin Mami tare da sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya
"Ni bana son sakarci, ke baki san yanzun girma ya kamaki ba? Ki dagani karki karyamun kafada"
Mami take fadi cikin karfin hali, amman ta kasa raba Layla da jikinta, idan ma akwai abinda take sonyi bai wuce sake riko Layla din ba. Addu'a ce yi mata takeyi ba tun yau ba
"Allah ya saka miki albarka a gidan auren ki Layla. Allah kar ya saka hawayen ki su zuba a sanadin kaddara ta gidan aure"
Shi Mami take furtawa a ranta, har sai da matar Yaya Ayuba ta shigo dakin tana kama Layla dakyar ta fita da ita. Da kanta ta saka Layla a mota suna jiran Rayyan ya fito tunda su kadai zasu tafi abinsu, ba wani rakata za'ayi ba. Sai Bappa da zai kaisu, yana zaune a gaba cikin mota suna jiran Rayyan din. Shi kuma bangaren Ayya ya tafi yace mata sun wuce ya kuma karbo Nur da yasan tana can.
"Ayya zamu wuce ne... Ina Nur?"
Rayyan ya fadi bayan ya shiga dakin Ayya din, kallon shi takeyi cikin fararen kayan shi, ya sake wasu duk da na safen ma farare ne, amman da babbar riga. Wannan kuma babu babbar riga, yayi kyau. Sai taga yau fuskar shi tayi mata fayau, ana cewa yana kama da ita, amman akwai wani abu a fuskar shi da yake mata kamar Abbu yau din nan
"Rayyan"
Ta kira da wani irin yanayi, nauyin hakkin shi take ji a duk rana, ta kasa samun karfin zuciyar fada mishi balle ta roke shi ya yafe mata, ta samu damarmaki da yawa tana kasawa, batasan me yasa yau din bakinta ya subuce da fadin
"Laifina ne, komai daya faru laifina ne, ni nayi kuskuren da ku da Bilal kuka biya, Bilal ya biya fiye da kowa, alhakin Haris da naso cutarwa ne ya kamani Rayyan, alhakin shi ya sa ka dauki shayin daya kamata ya sha ka sha... Shine mafarin komai"
Kallon ta Rayyan yakeyi tunda ta fara magana saboda yanda kalamanta suke dukan kunnen shi da wata irin iska
"Me yasa?"
Ya bukata muryar shi na fitowa can kasa kafin ya dora da
"Ayya me yasa sai yau?"
Duk ranakun da zata iya fada mishi maganar da zata fada sai ta zabi yau da yake neman duk wata natsuwa da zai iya. Hannu Ayya ta kai tana share hawayen da suka zubar mata, itama ba zatace ga dalili ba, amman abin ne yake cinta, musamman shekaranjiya zuwa yau. A shekaranjiya da ta zabi ta biya gidan Hajiya Dije da kanta bayan ta dawo daga kasuwa ta gayyace ta bikin Rayyan din duk da tun cikin rasuwar Bilal rabon da suyi magana, ta gwada kiran wayarta taji ta a rufe shisa ta biya. Sai ta sha mamakin jin Hajiya Dije tana gidan iyayenta.
Gidan kuwa ta biya, ta sha mamakin ganin yanda rayuwa tayi da Hajiya Dije, wani irin hawan jini ne ya kamata, ta fadi, tashin da tayi a asibiti babu idanuwa, shine bayanin da Mamuda, dan uwan Hajiya Dijen da yake zaune a gidan su da shiya gada aka kuma bata daki daya ya fadama Ayya, amman data shiga wajen Hajiya Dije sai labarin ya banbanta dan kuka Hajiya Dije takeyi kamar zata tsiyayar da abinda ya rage cikin idanuwanta
"Kinga inda rayuwa ta kawoni ko Maimuna? Hawan jini sukace a asibiti, ni nasan ba hawan jini bane ba, hakkin Balaraba ne, sharadin magani na karya ya dawo kaina, dan Allah Maimuna ki taimaka mun, bansan wa zan fadawa ba ya fahimta sai ke, ki taimaka mun Alhaji saki dayan daya rage tsakanin mu yai mun, yanda nake tsugunnen nan suma wallahi sai sun tsugunna"
Ko sallama Ayya batayi mata ba ta tashi ta fice daga dakin, saboda tsoro Hajiya Dije ta bata, zame mata tayi kamar wata dodanniya. Makantar da take tare da ita bata zame mata ishara ba ita, neman hanyar da zata cutar da wasu take karayi maimakon neman yafiyar su, da gaske akwai mutanen da basu da rabo, tun daga ayyukan su a doron duniya zaka gane hakan, ba zatayi shisshigi ba shisa ba zata yankewa Hajiya Dije hukunci ba. Baccin kirki ma a ranar bata samu ba, ta gaji, sosai ta gaji da barin abin a cikinta shisa ta fadawa Rayyan din. Kallon shi tayi da nufin magana sai ga Huda ta shigo rike da Nur da take kuka, hannu Rayyan ya mika ya karbi yarinyar
"Na bata ruwa taki ta sha, banga Adda Layla ba..."
Kai Rayyan ya jinjina ma Huda yana cewa
"Ina jakar goyon ta? Ki dauko mun da feeding bottle din, kiyi sauri"
Ficewa kuwa tayi da sauri, baisan inda zai saka kalaman Ayya ba ko abinda yake ji, shisa ya kwantar da Nur a jikin shi yana kokarin ganin tayi shiru, dan jijjigata yakeyi a hankali.
"Rayyan..."
Ayya ta kira, amman bai kalleta ba, kirjin shi zafi yakeyi na gaske. Huda da ta dawo ta taimaka mishi yayi strapping Nur daya goya a ta gaba yana karba feeder din ya fice daga dakin batare daya cewa Ayya komai ba. Inda motar Bappa da aka saka Layla a ciki take ya karasa ya bude ta dayan bangaren ya shiga, yana jin addu'ar da mutane suke binsu da ita. Amman sam hankalin shi ba'a kan su yake ba lokacin daya ja murfin motar yana fadin
"Muje Bappa"
Ya sake tallabe Nur da ya dan kalla yaga tayi shiru, sumbatar gefen fuskar yarinyar yayi yana gyara zaman shi hadi da sauke numfashi. Addu'ar duk da tazo mishi ita yake karantawa ko zai samu natsuwa har suka karasa Hotoro inda gidan daya kama yake.
*
Da yake ba mai gadi gare su ba, sai da ya tsaya Bappa ya fita da motar, da suka hada ido da shi yace mishi
"Koma menene karka sauke a kanta"