← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 93

Sashe 69

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta furta a fili wani kukan na kwace mata. Ayya ma duk yanda take saka hannu tana share hawayenta basu daina zuba ba. Na Abbu sun tsaya daga idanuwan shi, a zuciyar shi suke zuba da ciwo na gaske, da kuma tunanin ta inda zai fara bullowa abinda yake faruwa dan bai sani ba, yaran shine karfin zuciyar shi, sune kuma raunin shi.

*

Iyaye
Iyayen riko
Jinjina da lokuttan da baccin ku baya tsawaita saboda tunanin tashin hankalin da yake tare da amanar da take karkashin kulawar ku
Fatan alkhairi da tarin sadaukarwar ku
Addu'ar karfin gwiwar ci gaba da kular da kuke
Ta yau tafi ta jiya
Ta gobe ta dara ta
Kuna kokari mun sani
Idan bamu yaba yau ba zamu yaba gobe, kar tunanin rashin jin dadin mu na kankanin lokaci ya rufe idanuwan ku da hango gaba
Rabbi ya tayaku, Ubangijin da ya baku amana ya tayaku rike ta.
Amin thumma amin

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Dec 30, 2020.

26

Ba idanuwan shi ba, har fuskar shi a kumbure take, yayi kuka har wani yaji-yaji idanuwan shi sukeyi. Duka sallolin shi yau a gida yayi su, abinda ya manta ranar karshe da yayi. Ko bashi da lafiya saiya fita masallaci, ruwa kam banda yanzun da Yaya Ayuba ya tsare shi bai shiga cikin shi ba. Duk yanda Ayya tayi fama da shi kuwa, kai kawai ya dinga girgiza mata, da yake tasan halin shi, ta kuma san bashida wani abokin shawara a wannan yanayin daya wuce Yaya Ayuba shisa ta kira mishi shi, dan tana tunanin ko bai san damuwar su ba, zai ma Abbun fada yasa shi yaci wani abu kar ciwo ya hadar mishi biyu.

Fuskar Yaya Ayuba yake kallo dan tun da ya gama magana Yaya Ayuban yayi shiru baice komai ba. Ji yake kamar Abbu ya watsa mishi ruwan kankara, ya rasa mamaki zaiyi, bacin rai ko tashin hankali. Saboda maganar yake ji tana amsawa a cikin kunnuwan shi har yanzun

"Layla ciki gareta, cikin Rayyan"

Lokutta da dama har ran shi yana mantawa Layla da Bilal ba daga jikin Abbu suka fito ba. Shisa maganar ta dake shi ba kadan ba, tana tuna mishi da cewar Layla yar amana ce a hannun Abbu, yar riko ce, marainiya gaba da baya. Baisan wacce irin kwamacala bace wannan da yanda zasu fara bullowa lamarin.

"Kayi shiru..."

Abbu ya fadi zuciyar shi na tafasa

"Hmm"

Yaya Ayuba ya iya furtawa yana sake gyara zaman shi, sosai maganar ke yawata mishi, amman duk yanda ta kai cikin kan shi sai yaji wani irin tashin hankali ya tsirga mishi

"Nayi shiru ne ina so kace mun abinda naji ba dai-dai bane Ahmadi"

Numfashi mai nauyi Abbu ya sauke, shima tun dazun yake jira, tunda ya dawo dakin shi yake so wani ya same shi yace mishi komai daya faru wasa ne, an gwada shine kawai kuma anga yanda yaran shine raunin shi, amman shiru. Duk dakika da zai wuce saiya kara tabbatar mishi da cewa komai da ya faru da gaske ne.

"Ban san ya zanyi ba, wallahi ban sani ba"

Cewar Abbu, Yaya Ayuba na jinjina mishi kai

"Zubar da cikin ba mafita bane ba"

Wani bugawa zuciyar Abbu tayi, aiko mafita ne ma bai hango za ayi wannan danyen aikin da shi ba, zunuban zasuyi mishi yawa. Laifukan zasuyi mishi nauyin dauka matuqa, yana jin kuma da muryar da Yaya Ayuba yayi magana, bamai kwari bace ba, kamar yana son Abbu ya duba yiwuwar lamarin ne. Kuma hakanne a zuciyar Yaya Ayuba, so yake ya duba in zai yiwu a zubar da cikin, zai saukaka musu abubuwa da yawa, musamman maganganu da surutun mutane idan zancen ya fita, amman a fuskar Abbu yaga yanda babu wannan tsarin a cikin jerin mashalar da yake nema.

"Ina tsoron fitar maganar nan Ahmadi, wallahi ina tsoron ta, mutane zasu fadi komai, zasuyi surutai kala-kala... Ba akan Layla kawai zasu dora ayar tambaya ba, gabaki daya Martabar ahalin Dikko sai ta sami tangarda..."

Kai Abbu ya dafe da duka hannayen shi, a tarihin ahalin su gabaki daya, makamancin wannan bai taba faruwa ba. Ya fahimci tsoron Yaya Ayuba, sai dai maganar mutane mai wucewa ce, tunda gabaki daya rayuwar ma ba mai dorewa bace ba, komai zaizo karshe wata rana. Surutun zai taba zuciyar shine idan akayi shi akan Layla, idan aka dora ayar tambaya kan rikon da suke mata, sosai zuciyar shi take ciwo yanzun da tunanin hakan. Mutane zasu ce bai riketa da kyau ba, zasu ce yayi sakaci da tarbiyar ta, Ayya ma bata fito fili tace haka ba, amman ta fada mishi akwai raunin shi a cikin abinda ya faru.

Idan duk tarin kaunar da take mishi bai hanata fadin abinda ta fada ba, bashi da tabbas akan abinda mutanen da suke jiran kuskuren shi zasu fada, cike da matsananci tsoro Abbu yake kallon Yaya Ayuba

"Ya zanyi? Me zanyi?"

Dan jim Yaya Ayuba yayi, a cikin abin duka baiga wani zabi mai sauki ba, in dai cikin yana nan basu da tabbas akan tsayawar maganar a tsakanin su kawai. Amman yanzun bayason fadin wani abu da zai kara firgici da fargabar dan uwan nashi, shisa ya zabi fadin

"Shi Rayyan din ya kamata ya aure ta"

Kai Abbu ya jinjina cikin aminta da maganar da Yaya Ayuba yayi. Wayar shi da take kan kujera ya dauka yana kiran Ayya

"Ki kira Rayyan sai kuzo tare"

Ya fadi tana dagawa, bai jira amsarta ba ya kashe. Mami ma kiranta yayi yace ta taho da Layla

"Gara su san da maganar"

Ya fadi yana kallon Yaya Ayuba da baice komai ba, bayason ya tuna ma Abbu ko da za'ayi auren sai bayan ta haihu dole. Sosai yake kara jinjina lamarin. Ayya ce ta fara shigowa dakin da sallama, duk da gefe ta samu ta zauna. Ta kasan idanuwanta Abbu take kallo, yanda fuskar shi take a kumbure na taba zuciyar ta, zata dauke mishi duka wannan tashin hankalin in zata iya. Saida ta koma daki ta zauna ita kadai sannan tasan babu yanda za'ayi ta taba son Mami da Layla, saboda da bata dauko musu yarinyar ba da yanzun suna zaman su lafiya, da bata shigo musu da ita cikin gida ba, da mijinta bai shiga wannan yanayin ba.

Da ta dauko ta din, data riketa yanda ya kamata, da bata barta tabi mata yaro har Zaria ba duk wannan abin da sun kauce mishi. Sai dai in tayi magana yanzun za'a ce ita din bata san kaddara ba, kuma ba haka bane ba, tasan kaddara, ta dai san akwai wadda take tafiya da son zuciya, akwai kuma wadda take hade da sakaci irin wanda Mami tayi kuma Abbu na kallo ya biye mata. Da sun fada mata ita da tasan yanda zata nisanta yaronta daga Layla, watakila da duk basu zo nan ba. Yanzun da taje ta kirawo Rayyan din, zaune ta same shi ya hada kan shi da gwiwa, Bilal ma yana bakin kofar dakin a zaune ya hade na shi kan da gwiwa. Sai bayan ta fito ne ta dafa shi ya dago mata fuskar shi da take a kumbure kamar wanda yaci kuka

"Ka tashi daga nan Bilal, ko dakina ka koma"

Numfashi ya sauke, da wani yanayi yake kallonta

"Ki barni anan Ayya, dan Allah ki barni"

Bata da zuciyar tursasa shi, shisa ta kyale shi din tana tafiya. Yanzun ne tayi mamakin ganin shi ya biyo bayan Rayyan daya juya yana mishi wani irin kallo, yanda yayi tsaye na sanyaya wani abu a zuciyar Ayya, bata san meye take gani a tsakanin yaran nata ba, amman bata son shi, koma menene yana kara ma wutar tashin hankalinta fetur. Gefe Rayyan ya karasa yana tsayuwa, Bilal ne ma ya zauna a kasa kusa da Abbu. Yaji me Ayya tace, yaji tana fadama Rayyan din Abbu na kiran shi, sai da ya fito sannan shima ya mike da nufin rufa mishi baya

"Ina zaka je?"

Rayyan din ya tambaya, ya gwada shiga dakin bayan ya dawo sallar la'asar, ya sake yin magana da Rayyan, ko baice komai ba ya zauna a tare, amman yana daga labulen ya dago yayi mishi wani kallo da ya saka shi mayarwa ya saki. Bayason ganin shi, kamar yanda kowa na gidan yake gab da fara ji a kan shi ya sani, har karshen rayuwar shi zai kasance mai godiya da karamcin su, yanda suka karbe shi suka darajta shi. Ba kuma zai ga laifin su ba, yaci amanar sune shisa, yayi musu kuskuren da ko bakin da zai basu hakuri baida shi.

"Ba zaka dauki laifin da bakayi ba, ba zan bari ba Hamma"

Sai da Rayyan din ya dan dafe kan shi sannan ya saki yana kallon Bilal din

"Karka biyoni Bilal, karka fara biyoni..."

Kamar baiji kashedin Rayyan din ba, yana juyawa, inda ya saka kafar shi nan Bilal ya mayar da tashi, yana tsayawa shima ya tsaya, batare da ya juyo ba wannan karin yace

"Nace karka biyoni bakaji ko?"

Sun kusan minti daya a tsaye kafin Rayyan din ya sake cigaba da tafiya, wannan karin sai da ya sha kwana sannan Bilal yabi bayan shi. Ba zai zauna ya sake hada Rayyan din da su Abbu ba, bayan abinda yayi, ba zai bari ya kara wani ba. Ko yanzun da Rayyan din ya bishi da wani irin kallo, kan shi kawai ya sadda kasa, ya zauna kusa da Abbu ne saboda ya san damar yin hakan na gab da kwace mishi, zuciyar shi yake ji zaune cikin kirjin shi tana dokawa a hankali a hankali, kamar wadataccen jini baya zagaya mata, suna zaune Mami ta shigo, Layla na bin bayanta, har yanzun tun kayan dazun ne na jikinta, ko hijabin ma bata cire ba.

Inda suka barta bata tashi ba, anan rana ta sameta, anan kuma tabarta, ko sallah batayi ba sai da Magriba da Jabir yazo ya sameta tana zaune anan, shima har zai wuce saiya kasa, ya dawo baya

"Ki tashi daga nan"
Chapter 69 · 0% Book details