← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 93

Sashe 15

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karasa maganar yana ficewa daga dakin. Kan shi tsaye bangaren Maryama ya nufa, ita da Jabir ya samu zaune a falon suna cin abinci. Jabir suna gaisawa ya dauki filet din shi yana ficewa

"Sannu da dawowa...kayi zuru-zuru"

Maryama tai maganar cike da kulawa, yar dariya Ahmadi yayi

"Yanzun nan? Ko dan ba zama mukayi waje daya ba, kinsan ni da nayi zirga-zirga sai fuskata ta nuna"

Murmushi tayi

"Hutu ne yai maka yawa"

Ta karasa maganar da sigar tsokana tana mikewa, tana jin dariyar da yakeyi. Ruwa taje ta kawo mishi, bata ma gwada mishi tayin abinci ba tunda girkin Maimuna ne, tasan ko yana so ba zai taba ci ba. Wani lokacin ita kadai takan yi tunanin ko duka maza haka suke da adalci irin Ahmadi, sosai yake duk wani kokarin shi na ganin yayi adalci a tsakanin ta da Maimunar

"Ya kuke? Fatan dai kowa lafiyar shi kalau... Na shiga in duba yaran a daku nan su dana shigo, ina jin basu dawo daga sallar isha'i ba"

Kallon shi takeyi

"Anya kuwa? An idar da sallah, sai dai ko in sun tsaya wajen abokai ana hira. Duka lafiyar su kalau. Alhamdulillah"

Kai ya jinjina

"Alhamdulillah, ina Layla?"

Murmushin ta Maryama ta fadada

"Fushi take mun dan na mata fada kan saka kananun kaya"

Dariya yayi

"Layla manya... Yaran ne basajin magana, ni da ina yaro abinda za ayi mun magana ma bana farawa, idan akayi sau daya kam bazan bari a maimaita ba..."

Numfashi Maryama ta sauke, zata ce duk wani abu da ta saka Layla tanayi, bangaren aiki kuwa in ba tana makarantar boko ko ta islamiyya ba cokali bata bari ta daga. Girki tun tana koya mata har yanzun babu wani abu da bata iya girkawa ba. Tana da rigima, sosai tana da rikici, amman idan ba tabata kayi ba babu ruwanta da kai, ga fadanta baya rabuwa da wuri saboda mita da take da ita, kusan Maryama zatace duka yaranta sun biyo sanyin hali irin nata, kau da kai da sanin ya kamata irin na baban su. Jabir ne ma bashi da hakuri idan ka tabo shi.

Sai Layla tayi wani abin sannan take tuna cewa ba daga jikinta yarinyar ta fito ba. Matsalar da suka cika samu da Layla bai wuce yanda a rayuwarta take bala'in son kananun kaya ba, idan zata wuni da dogon wando da yar riga yafi mata dadi, gara ma ranakun asabar da Ahmadi ya ware yana zama a gida. Shine zaka ga tana yini yawo da hijabi, kamar duk gidan shi kadai ne take jin nauyi ko shakka kar yai mata magana. Amman da yan shekarunta ko atamfa ce skirt din sai tace a sha mata shi, ga kirar jiki da Allah yayi mata, wasu lokuttan Maryama kan jinjina kalar jikin da Layla take da shi, shisa take tsoron shigar da takeyi.

Bataso, amman da duk rana da take kokarin ganin ta rabata da kananun kaya, da ta daina sai mata, kudinta duk idan ta tara akwai gidan su Farida, nan cikin unguwa, islamiyyar su daya da Layla din, kuma ajin su daya, sana'ar gwanjo mahaifin Farida yakeyi, dila-dila yake kawowa daga kwatano, hakan yasa matar kan bude itama tana siyarwa cikin gida. Sai dai Maryama taga Layla ta shigo da abinta, duk yawancin kudadenta yanzun a can suke karewa, kuma sukan mata saukin kayan saboda sanayya. Idan ma tayi mata fada sosai, kwana biyu tana saka atamfa haka zakaga dakyar take motsawa saboda matsewar siket din da yake jikinta.

Zatayi karya idan tace abin baya damun ta, sai ta tuna zancen da mutane kanyi na cewar

"Dan riko wahalar sha'ani gare shi"

Wasu ma sukan ce

"Maraya akwai wahalar riko"

Duka biyun take gani akan Layla wasu lokuttan, amman duk wani abu da zaifi karfinta da addu'a take hada shi, Laylar ma addu'a takeyi mata, saboda girma take karayi, halittarta ta 'ya mace na kara fitowa, shisa yanzun Maryama ta numfasa kawai tana fadin

"Allah dai ya shirya mana, yaran yanzun magana har sai bakin ka yayi tsini"

Mikewa Ahmadi yayi

"Amin thumma amin. Abinda yafi tsini kam bakin ka zaiyi. Idan sun shigo nasan zangan su..."

Ya fadi yana dorawa da yi mata sallama, daman lafiyarta da ta yaran ya shiga dubawa kamar yanda ya saba ko aiki ya dawo, balle kuma tafiyar kwanaki hudu. Yayi kewar su ba kadan ba. Yana fita dakin Maimuna ya wuce, inda ya sameta ta fito falon tana zaune, yanayin fuskarta yake kallo, girma bai hana shi gane rigimar da take shimfide a kan fuskar ba

"Uwargidan Ahmadi..."

Kallon shi tayi tana kauda kai, tunda ta fito daga daki Huda ta fada mata ya shigo ya fita take kallon agogo, mintina sha ukun sai take ganin su kamar awanni sha ukku dan tasan yana wajen Maryama ne. Wani irin tuquqin kishi da shekaru basuyi komai wajen rage mata ba take jin yana taso mata

"Magana fa nake yi..."

Sake kallon shi tayi

"Ai na dauka a can zaka kwana"

Yanayin yanda tayi maganar ne yasa shi dariya

"Hmm..."

Ta furta, ba yau ya saba mayar da ita mahaukaciya ba daman

"Yi hakuri... Na shigo kina sallah, shine nace bari inje mu gaisa kafin ki idar"

Cike da rigima take kallon shi

"Ko dawafi nakeyi ai kasan na idar tun dazun dai. Sai kayi zaman ka kunata labari, kuma tunda girkina ne, kwana hudu bangan ka ba, ya kamata ace ka bari na fara sakaka a idanuwana tukunna kaje duk inda zakaje"

Murmushi Ahmadi yakeyi, zuwa yanzun indai rikicinta ya saba da shi

"Ba za'a kara ba Uwargida. Kiyi hakuri..."

Numfashi ta sauke

"An dawo lafiya?"

Ta fadi ciki-ciki har lokacin, sai da ya tabbatar ya jata da hira ta daina amsa shi dai-dai tukunna ya mike

"Da kaci abinci dai sai kayi wankan"

Kai ya girgiza mata

"Bari dai in watsa ruwan, kafin in fito kin hadamun abincin..."

Ahmadi ya karasa maganar yana soma tafiya. Mikewa tayi itama, so yayi ya wuce bangaren shi, amman yana son ganin su Rayyan, haka kawai ya kasa hakura, musamman da yasan in ba a hanya ya hadu da Rayyan din ba, ba zaije yayi mishi sannu da zuwa ba. Kowa zaije amman banda shi, yaso ya tambayi lafiyar yaran daya bayan daya, amman yana gudun jin ance Rayyan din yayi wani abu bayan tafiyar shi, Allah ne shaida da shi yake kwana a ran shi, da shi yake kuma tashi. Ko waya tayi kara sai gaban shi ya fadi, sai yayi zaton ko Rayyan ne ya dauko wata maganar da yayi nisa da gida.

Akan Rayyan ne yasan cewa zai yiwu ka haifi da ka dinga jin zuciyarka na rawa duk sanda zaka gan shi, yanzun da yake nufar dakin su Rayyan din sai yaga kamar yayi mishi nisa.

"Oh Allah..."

Ahmadi ya furta jin yanda zuciyar shi ke rawa

"Allah idan jarabta ce ka kadarta mu ta fado akan Rayyan, Allah ka bani karfin zuciyar daukar ta. Allah na yafe mishi duk wani laifi daya taba mun, wanda na tuna da wanda na manta. Rabbi ka shiryamun yarona, Kai ka bani amanar shi, kai ka sakamun kaunar shi, Allah karka sa ya zama rauni na"

Shine addu'ar da ya tsinci kan shi da yi, duk da ya kasa samun natsuwa, musamman daya tinkari dakin yaji wani irin wari da tashin hankali bai barshi fahimtar ko na meye ba farat daya, sai da ya kara kusantar dakin sannan ya gane warin sigari ne, badan cutarwar da takeyi ba, cutarwar da yagani da idanuwan shi akan abokin aikin su da bature ne dan kasar amurka, haka da wahala ka ganshi batare da sigari ba, kullum cikin buka ma cikin shi hayaqi yake, lokaci daya ya fara wani irin tari daya kwantar da shi, kafin ace kansar huhu ce tayi mishi muguwar illa a sanadin taba.

Ko sanda sukaje asibiti duba shi kafin a mayar da shi kasar shi inda ya mutu a can, yanda yake kokawa da numfashin shi Ahmadi zaiso duk wani mashayin sigari ace yana dakin asibitin dan yaga tashin hankali da illar da sigari takeyi ko zai yarda ya daina cutar da kan shi. Shi ko warin ma idan yaji sai zuciyar shi ta dinga tashi, tana daya daga cikin abubuwan da yaki jini

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Ya furta a fili yana kasa kwankwasa kofar dakin jin warin sigarin da zuciyar shi taki taya kwakwalwar shi karyata cewa ba daga cikin dakin su Rayyan warin sigarin yake kara fitowa ba. Wani irin bacin raine da yake shirin danne firgicin da yake ciki ya saka shi tura dakin batare da sallama ba, haske ne gauraye da dakin saboda akwai wutar lantarki. Rayyan na zaune akan kujera ya dora hannayen shi kan teburin da yake gaban shi, Bilal na tsaye, inda ya juyo saboda turo kofar da su duka suka ji anyi

"Abbu..."

Bilal ya kira da wani irin yanayi da yafi tashin hankali a muryar shi, Ahmadi kuwa kallon su yake, dan yanzun ya kara tabbatar da cewa daga dakin su warin sigarin yake fitowa. Tunda gashi nan cike da shi

"Sigari, Rayyan sigari kake sha yanzun kuma?"

Cewar Ahmadi da wani irin bacin rai da disappointment na gaske tattare da muryar shi, yanayin da ya saka Bilal fadin

"Ba shi bane Abbu, ba Hamma bane"

Da wani yanayi Ahmadi yake kallon Bilal, Rayyan kuwa yana zaune inda yake, ko motsi baiyi ba balle wani yai tunanin zai tanka, asalima idan ka shigo dakin zaka rantse da Allah abinda yake faruwa bai shafe shi ba, wani ma zai iya cewa bai taba sanin Bilal din da Ahmadi ba ballantana yabi takan abinda suke tattunawa

"Kar kaimun karya Bilal, warin sigari tun daga wajen dakin nan anaji, karka ce mun daga kofar gida ya taso ya zabi ya tattaru cikin dakin ku"

Kai Bilal ya girgiza

"Ba ina nufin ba'a sha sigari bane, ina nufin ba Hamma ya sha ba"

Duk da alamu sun nuna Ahmadi bai gama yarda da zantukan Bilal din ba, amman akwai wani hope daya cika idanuwan shi, da gaske so yake ko yane a karyata mishi zargin shi. Abin zai mishi yawa idan ya zamana Rayyan dinne.

"Bilal..."
Chapter 15 · 0% Book details