← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 93

Sashe 13

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baice komai ba ya shige abin shi, kai kawai Abbu ya jinjina. Da gaske ne jarabawa ta rayuwa takan zo ma bawa ta fanni daban-daban. Inda wani ya bashi labari tashi jarabawar zata so ta bangaren Rayyan ne ba zai taba yarda ba. Yana tuna kalar shakuwar shi da yaran a lokacin da yake dan karamin shi. Sai da ya dauka a cikin yaran shi gabaki daya mazan babu wanda zasu shaku dashi kamar shi da Haris, lokaci daya Rayyan ya sauya kamar wanda jinnu suka shafa.

Yanzun Rayyan ne zai nuna sam bayason magana da shi, zai karya idan yace abin baya mishi ciwo, yana kula da yanda idan ya nuna yana son abu to Rayyan din yaki abin kenan, kamar a duniya yana rayuwa ne dan ya bakanta mishi. Karatun shi ma sai da dabarar da Yaya Ayuba ya bashine da yai amfani da ita tukunna ya samu kan shi. Shisa ko da wasa yaki nuna mishi yana jin dadin yanda yake maida hankali. Yanzun ma ya kula sam ya daina jin ya Rayyan din yake ciki a makaranta. Ko wani abin akace su siya saidai Bilal yazo ya fada mishi.

Bai cika tashi tsayuwar dare ba, amman matsalar Rayyan tasa dare dai-dai ne baya tashi dan kawai yayi mishi addu'ar samun salama. Zuciyar da yake da ita tafi komai dagama Abbu a hankali, zuwa yanzun ko sallama akayi dashi a unguwa yasan ba zai wuce an kawo karar Rayyan din ba. Ko lokacin samartaka fada bai taba hadashi da wani ba, ammam sai gashi zuwan shi police station takwas duk akan Rayyan. Kuma ba yan waje kawai ya tsaya ba har cikin gida babu mai rabar shi, kusan kullum sai yayi ban hakuri cikin gidan akan Rayyan.

Yama daina mishi fada, nasiha ce wasu lokuttan, wasu lokuttan kuwa sai dai yabi shi da addu'a kawai, yanzun ma

"Allah ya shirya"

Ya fadi yana wucewa. Rayyan kuwa dakin Ayya ya shiga, idan kasan gidan su a baya, kazo yanzun zakayi mamakin yanda aka gyara ginin yayi dai-dai da zamani, saboda rufin asiri dai-dai misali Abbu yana da shi. Ya taka matakin Professor kamar yanda burin shi yake, ga kasuwancin shi da Allah yake saka mishi albarka saboda shi mutum ne mai yawan taimako da kyautatawa iyalan shi. Shisa sam baya kukan rashi, rayuwa sukeyi mai natsuwa. Duk da tsayin shekaru bai canza zaman da yake tsakanin Maimuna da duka yaran suke kira da Ayya sai kuma Maryama da suke kira da Mami.

"Rukayya babu ruwa ne a dakin?"

Rayyan daya shiga kitchen ya duba bai gani ba ya fito falon yake tambaya. Da saurinta ta mike, har ranta tana kaunar Yayan nata, haka ma sauran yan uwan nasu, amman baya shiga cikin su, baya shiga sabgogin su, zatayi karya idan tace batajin kishin Bilal wani lokacin, saboda kusancin da yake tsakanin shi da Rayyan din. Ayya ba fada takeyi ba, amman sunsan cewa ba daga jikinta Bilal ya fito ba, saboda ko a makaranta da asalin sunan Baban shi yake amfani. Sai take ganin kamar ya kamata ace sunfi shi kusanci da Rayyan din.

Fridge taje ta duba tana dauko mishi leda daya na ruwa ta fito ta kawo, tun kafin ya karba yace

"Ba mai sanyi ba Rukayya... Bana son ruwa mai sanyi"

Kai tadan rausayar, bai shiga cikin su bama balle su san me yake so ko meye baya so.

"Hamma duk an saka a fridge... Sai dai ko idan zaka ajiye ya huce..."

Karbar ruwan yazo yi

"Kabari in kai maka daki"

Kai ya girgiza yana karba

"Zaka karya in hada maka tea?"

Kai ya sake girgiza mata, saboda ya fara jin maganar da sukeyi tayi mishi tsayi. Bayason kananun surutai marassa dalili

"Ko zaka ci wani abin"

Daga idanuwan shi yayi yana mata wani irin kallo daya sata komawa ta zauna. Kusanci take nema a tsakanin su ko yayane, kamar ko da yaushe bai bata wannan damar ba, zai fita daga dakin kenan Ayya ta fito daga dakin baccin ta

"Rayyan..."

Ta kira tana saka shi runtsa idanuwan shi kafin ya budw su a hankali

"Ayya ina kwana..."

Ya fadi yana dan juyawa

"Kaci gidan ku... Daka shigo bakasan inda nake ba halan?"

Kai ya jinjina

"Ayya....ruwa kawai na zo dauka, ban san kin tashi ba kuma"

Kallon shi kawai tayi, tasan karya yake, da bata fito ba sam ba zaije su gaisa ba. Idan zaiyi yini biyu bai sakata a idanuwan shi ba baya damuwa, Bilal ne idan shigowa goma zaiyi gidan saiya zo ya nemota, wani lokacin sai taga kamar yana son rage mata damuwar Rayyan ne, musamman idan yasan Rayyan din yayi wani laifi. Haka zai wuni yana lallabata kamar shi yayi mata wani abu. Kuma da gaske yana rage mata damuwa ba kadan ba.

"Allah ya shirya mun kai"

Cewar Ayya, Rayyan na ficewa daga dakin. Kan shi tsaye dakin su ya wuce ya ajiye ruwan. Dai-dai shigowar Bilal

"Yaushe zaka daina cin zalin yarinyar can ne? Kai baka duba maraicin ta?"

Dan fitowa yayi yaga Layla na tsaye tana hawaye, ga yatsun Rayyan kwance a kan fuskarta. Bai tambayeta me ya faru ba, hakuri kawai ya bata dan yasan a gidan babu wanda zai daketa idan ba Rayyan din ba. Duk idan kaga hawaye a idanuwanta to shine.

"Karka kara batamun rai Bilal..."

Rayyan ya fadi, shiru Bilal din yayi ya kyale shi. Idan ma surutu yayi yana iya kara jama Layla wani dukan. Duk saurin hannun Rayyan saika shiga harkar shi tukunna. Amman banda Layla, da alama ko numfashi tayi kusa dashi laifine. Har mamaki Bilal yakeyi, kuma ko aike Rayyan din zaiyi, gashi tunda yasan idan ya aike shi ba zaiki zuwa ba, takanas zai leka ya kira wani yaro cikin gidan ya bashi kudin yace a kai Layla ta siyo mishi, kuma da wahala aiken ya kare da dadi, dan sai ya nemi wani dalilin da zai daketa.

Kuma na rana daya bata taba kin zuwa aiken shi ba, duk wasu kananun ayyukan shi ita din yake sakawa. Shirin makaranta ya karasa suna fita tare da Rayyan din, su duka sabon sune sai sunje makaranta suke karyawa. Gara Rayyan ya siyi biscuit a hanya

"Hamma kai da biscuit"

Bilal ya fadi yana dariya. Ba zaka taba raba aljihun Rayyan da biscuit ba, ko jakar makarantar shi ka duba zaka samu, kuma bayason mai zaki. Haka zai ta daukar abin shi dai-dai yana ci. Babu wanda baisan amanar da take tsakanin shi da biscuit ba, har Abbu wasu lokuttan yakan siyo sai ya baiwa Bilal din yace yaba Rayyan. Yanajin wani iri duk lokacin da Abbu ko Ayya zasu kyautatawa Rayyan din sai abin ya biyo ta hannun shi. Sai yake jin kamar suma zasuji ya kwace musu kusancin daya kamata ace yana tsakanin su da dan nasu.

"An hana ci ne?"

Kai Bilal ya girgiza mishi

"Kaima idan kana ci kasa hannu, ban hanaka ba ai"

Kai dai Bilal din ya sake girgizawa, shi bama komai yake ci ba. Babur suka tare suna hawa su biyun zuwa makaranta daya kamar yanda suka saba.

*

Bilal bai bude ledar da Aisha ta bashi ba sai da yazo gida. Harya natsu ma, duk gidan shi da Bilal ne suka fara makaranta daya daga firamari har yanzun suke sakandire a ALIC. Kuma yasan Aisha tun tana firamari, yana mata magana ne saboda tana mishi yanayi da Layla, daga rawar kanta har idan tayi dariya. Idan alewa yagani zai siya yakan siyi guda biyu ya bata daya. Aji dayane a tsakanin su, yanzun yana aji hudu ita kuma tana aji uku, kusan duk wanda yake ALIC yasan Aisha da Bilal. Danma shi wani lokacin yana tare da Rayyan, ita kuma tsoron Rayyan take ji, ba ita kadai bace, kusan duk wani wanda yake cikin makarantar tsoron Rayyan din yake ji.

Garama Aisha saboda Bilal yana dan mata magana wasu lokuttan. Amman idan baka ganshi da Rayyan ba zaka gan shi da Aisha. Wata irin shakuwa ce mai karfi a tsakanin su, zuwa yanzun har yan gidansu sun san Bilal, musamman wani lokaci da tayi rashin lafiya ta kwanta asibiti, yaje yafi sau biyar, hatta da Baban Aisha sai da yasan shi a lokacin. Da yake yana da wani irin shiga rai, haka cikin kankanin lokaci ya shiga ransu suma. Har wata Yayar Aisha din ta dinga tsokanar shi

"Bilal din Aisha..."

Murmushi ya dingayi saboda kunyar da ta dinga sakawa yanaji. Yanzun ma bude ledar yayi, biskit ne kala-kala da cin-cin, a cewarta bikin abokin wasanta akayi. Kayan bikin ne ta kawo mishi. Bayason kayan zaki haka, kawai dan Aisha ce shisa ya dauki cin-cin daya ya saka a bakin shi. Baiji shigowar Rayyan ba sai hannun shi da yagani cikin ledar yana daukar biskit guda biyu

"Kai ba zakai sallama ba"

Waje Rayyan ya samu ya zauna, kamar baiji maganar da Bilal din yayi ba

"Ina ka samo biskit kai kuma?"

Murmushi Bilal yayi

"Aisha ce sukayi biki, shine ta kawo mun"

Kai Rayyan ya jinjina

"Yara kanana daku wai soyayya. Allah ya shirya"

Yanayin yanda Rayyan din yai maganar ne ya ba Bilal dariya. Zaka rantse da Allah wata shekara goma ya bawa Bilal din ba daya da doriya ba

"Waye yace maka soyayya mukeyi?"

Tabe baki Rayyan yayi

"Zan fadama Ayya su fara shiri, ba zakai karatu ba, gara Abbu ya kaika kasuwa kawai a aurar da kai...ka kawo biskit din nan ko guda biyu a kai ma Ayya dan ta ga abinda surukarta ta bayar..."

Dariya Bilal din ya sakeyi yana fadin

"Hamma..."

Dariyar shima Rayyan yakeyi

"Jibi yanda idanuwanka suka cika da kunya. Bilal... Allah ya shiryeka to"
Chapter 13 · 0% Book details