← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 93

Sashe 56

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan juyawa Ayya tayi ta kalli Abbu, sannan ta sake mayar da dubanta kan Bilal. Bata zaton akwai wani abu da zai faru wanda zai saka zuciyarta taso Layla, yarinyar batayi mata ba tun daga ranar farko da ta dora idanuwanta a kanta. Ta kara girmama tsanar da take mata daga lokacin da Bilal ya fara raba lokuttan shi tare da yarinyar da kuma Mami, har yana shiga bangaren su. Sai kuma take kara ganin yanda Rayyan yake bata lokacin shi cikin yanayin da ko ita bata samun shi. Babu wani abu da zai sa taji yarinyar a ranta, bata sonta, in zata iya nisantata da duka yaranta zatayi. Amman rashin lafiya ce, batama san dan ance Layla bata da lafiya zataji wani abu ba.

Ganin yanda take tunani yasa Abbu fadin

"Ki zauna tare da Bilal din muje mu dawo"

Kai ta jinjina ma Abbu da ya saka hannu a aljihun shi, dubu hamsin ce ya cire ya taho da ita ko da zasu bukaci wani abin, talatin ya kirga ya bawa Ayya da fadin

"Ko da za'a bukaci wani abu"

Zuciyar shi a jagule take, ba zai kara jagula yanayinta ba ta hanyar bawa Rayyan kudin da yasan da wahala ya motsa daga inda yake ballantana ya saka hannu ya karba, sai yaga Rayyan yake tuna yanda yake son sakawa a tayashi a addu'a akan matsalar Rayyan din, ko da Nasiru ne yayiwa zancen, amman kamar wanda ake shafarwa kwakwalwa sai ya shirirance, sai ya sake ganin Rayyan din tunanin maganar ya dawo mishi, numfashi mai nauyi ya sauke yana juyawa, Mami na fadin

"Allah ya kara sauqi ya bashi lafiya"

Kafin ta juya tabi bayan Abbu suka fice daga dakin. Ayya kuwa Rayyan ta kalla, idanuwan shi duk sun shige ciki, bata ga sunyi ja ba balle ta alakanta abinda take gani a cikin su da rashin bacci, amman yayi duhu ya kuma fada da alamun rama

"Yaushe rabon da kaci abinci?"

Numfashi ya sauke

"Na ci abu jiya da rana..."

Mikewa Ayya tayi, bai tambayeta in da zataje ba, ya gaji, a gajiye yake jin shi. Kan shi da kirjin shi kamar akwai wani a cikin su daya danne. Ga son ganin Layla da kewarta da suke nukurkusar shi. Ba zaice ga mintina nawa Ayya tayi a waje ba, amman da leda ta dawo, lemukane ta siyo na robobi sai kuma biskit.

"Ka zo ka dauka"

Tace mishi, tsaye yayi yana kallon lemukan, kafin ya kalli Ayya, kamar yana son sanin lokacin da ta kula, ko ya akayi ta sani

"Ka zo ka dauka Rayyan, na san bakacin abinda baka san inda ya fito ba, Bilal ya fadamun"

Ta karasa maganar da wani yanayi a muryarta, duk wani kusanci da yake tsakaninta da Rayyan, wanda ya kamata ace yana tsakanin uwa da danta, ta same shine a sandin Bilal. A cikin labaran shi yakan fada mata abubuwan da Rayyan yake so da wanda bayaso, yanayin shi da duk wani babba da karamin abu da yake tunanin zata bukaci ta sani, ko kuma zata so ta sani din. Ko waya sukayi saiya fara bata labarin yanda ranar Rayyan din ta kasance, sannan zai bata labarin ta shi ranar

"Rayyan ma yau yayi lakca..."

Ya kan fara fadi bayan sun gaisa ko yace

"Sai da muka tsaya wani shago yau da muka fita da Rayyan ya siyi biskit, kin san halin shi ba cin wani abu yake a waje ba"

Ya kan karasa maganganu irin wannan da dariyar da kan sakata yin dariya itama. A fadin duniyar ta Bilal daban ne, Bilal ya kan fahimci damuwarta a lokuttan da Abbu bai gane ba. Shisa hankalinta ya tashi, ta kasa samun natsuwa duk yinin jiya har zuwa safiyar yau, bacci ma sai dai tace barawo, da kuma ya fisgeta take farkawa saboda mugayen mafarkan da bata tunawa da suke addabarta suna sake sakata jin kamar wani abu mai girma ya sami yaranta. Rayyan daya karaso ya saka hannu ya dauki coke tabi da kallo, biskit din kwara daya ya dauka. Bata ce mishi don me ba.

Tana ji da Bilal ba zata biye Rayyan ba, yana da girman da yasan cikin shi na bukatar abinci ko da bakin shi bayaso. Batayi mishi magana ya zauna ba, tana kallo yaja kujera ya zauna. Suna nan su Abdul suka biyo, sosai Ayya ta jinjina karamcin su, sun siyo su Maltina da ruwa sun taho da shi. Ta kuma yi mamakin ganin Rayyan ya gaishe su, yana kula da kallon da takeyi mishi, ko da yabar Zaria su Abdul na cikin jerin mutanen da ba zasu taba mantuwa a zuciyar shi ba, sun mishi kirkin da bai taba tsammani ba a lokacin da yake cikin tsananin bukatar taimako

"Ka gaisa da kowa a mutunce ko baka so Hamma, ko mutuwa kayi kafin a kira su Ayya su din nan da muke waje daya zasu fara sani"

Bilal kan fadi amman bayajin shi, saboda yana ganin gaisuwar kanta a matsayin takurar sosai, gashi sai su dinga gaisawa da kai da sassafe hannun su duk ruwan da baisan kona menene ba. Yanzun kam in sun gaishe shi zai amsa ko da bayaso din, in yaso ya wanke hannun shi da sabulu kamar yanda yakan yi. Sai bayan sun tafi Ayya tace

"Abokan ku suna da kirki"

Kai Rayyan ya girgiza mata

"Abokan Bilal ne, gida daya muke..."

Saboda shi yasan ba abokan shi bane ba, ya san ko da suka taimaka mishin dan Bilal sukayi. Kai kawai Ayya ta jinjina, ta dan gyara zamanta kenan taga Bilal ya motsa. Sake motsin yayi yana jin shi kamar wanda yayi tafiya mai nisan gaske zuwa wani waje, aka kuma dauke shi aka cillo da karfin gaske. Idanuwan shi da sukayi nauyi yake kokarin budewa a hankali saboda haske yayi mishi yawa. Yayi kokarin bude su yakai sau biyar kafin ya samu ya bude su gabaki daya

"Bilal..."

Yaji an kira cikin muryar da ta saka shi juyar da kan shi a hankali ya kalli Ayya, bakin shi yayi nauyi balle ya kira sunanta

"Bilal"

Ta sake fadi tana sauke numfashin da batasan tana rike da shi ba. Idanuwan shi ya mayar ya runtse, komai na dawo mishi cikin yanayin da y saka yan hanjin shi yamutsawa cike da sabon tashin hankalin daya dirar mishi. Ko su Ayya har sun sani ne shisa suka zo, da wanne ido zai kalle su, ta ina zai fara amsa tambayoyin su, dakyar ya iya sake bude idanuwan shi yana bin hannun shi da kallo, yaga karin ruwan da saura kadan ya kare, sosai yake karewa dakin kallo yana gane tabbas a asibiti yake, kamar sama-sama yaji muryar Rayyan, da ido ya lalubo Rayyan din da yake zaune kan kujera yana kallon shi

"Hamma"

Ya furta muryar shi a hankali, amman Rayyan din yaji, fuskar shi ya saka cikin hannuwan shi yana wani irin sauke numfashi. Allah kadai yasan halin da yake ciki tun shekaranjiya, musamman jiya kuma zuwa safiyar yau. Komai karfin hali yake, sanin Bilal na da rai baya nufin hankalin shi ya kwanta tunda bai ga ya motsa ba. Wata natsuwa ce take dawo mishi, ya kai dakika biyar kafin ya bude fuskar shi yana mikewa ya karasa in da Bilal din yake

"Bilal?"

Ya kira cike da alamar tambaya, duk da idanuwan shi a bude suke, yana son ya kara tabbatar da cewa da ya tashin

"Hamma"

Cewar Bilal, wani numfashin Rayyan ya sake fitarwa, da wani yanayi a fuskar shi ya ke kallon Bilal

"Karka sake tsoratani haka, Bilal karka sake tsoratani haka..."

Ya karashe maganar yana sake sauke numfashi, sai da yaga Bilal din ya dan daga mishi kai tukunna ya juya, hanyar kofa ya nufa yana budewa ya fita, hadi da ja musu kofar ya rufe. Anan bakin kofar ya tsugunna yana wani irin mayar da numfashi kamar yayi gudu. Godiya yakewa Allah da duk wani yare da yake fahimta, da zai iya kuka tabbas zaiyi na saukin da ya samu lokaci daya haka. Ya kusa mintina  biyar anan tsugunne kafin ya iya mikewa, kujerar da take ajiye irin na karfen nan ya zauna kan guda daya. Hutawa yakeyi yasan Ayya da Bilal labari zasu fara, yanda kan shi yayi nauyi sosai zai takura.

Yana nan zaune Abbu ya dawo

"Ya mai jikin? Har ya tashi?"

Abbu ya fadi, kai Rayyan ya jinjina mishi, harya karasa ya murza kofar Rayyan yace

"Ya Layla? Abbu ya take?"

Dan juyowa Abbu yayi

"Taji sauki, na barta da Maminta ma, abinci take ci sanda na fito"

Kai Rayyan din ya jinjina zafin da kirjin shi yakeyi yana yin sauki. Da Mami ta biyo Abbu sun dawo zaije wajen Layla. Amman yasan Mami batason shi a kusa da Layla, saboda haka zai jira sai ta tafi, zaiyi wannan hakuri. Wayar shi dai ya zaro daga aljihu yana tura mata sako

"Baki kirani ba da kika ta shi"

Yana shiga tana dawo mishi da amsa

"Sai da su Mami suka zo na tashi Hamma, naji sauki. Ya Hamma Bilal?"

Numfashi ya sauke

"Ya tashi yanzun shima. Allah ya baku lafiya. Ki kula da kanki, zan zo in ganki anjima"

Har yana shirin mayar da wayar aljihun shi yaji sako ya shigo

"Ina son ka Hamma"

Murmushi yayi, abinda ya kwana uku rabon da yaji ko alamun shi, sosai murmushi yayi har hakoran shi suka bayyana, a hankali wani sanyi yake sauka cikin kirjin shi, sake karanta sakon da ya zauna a kwakwalwar shi yayi saboda yana jin muryarta a cikin kan shi inya karanta daga wayar. Ya jima kafin ya iya mayar da wayar aljihun shi, ya kasa daina murmushi. Yanayin da yake ciki bayason ya bar shi, zaiso ace kullum yana cikin yanayin, kafin yayi mata magana tunanin fita ya nemi sigarin da zai sha yakeyi ko zuciyar shi zata kara rage zafi. Amman yanzun yaji baya bukata, dutsen da yake danne da kirjin shi ya daga da kalaman Layla.

Hamma yayi alamar baccin da yanzun yake jin alamun shi, amman bashi da halin kwanciya. Natsuwa ce ya samu shisa ma har baccin ya samu zuwar mishi.

*
Chapter 56 · 0% Book details