Sashe 47
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta furta da wani yanayi a muryarta, watakila Rayyan din daya tafine yasa zuciyarta bugawa haka. Sosai ta so ganin shi, gashi tasan magana da sassafe wahala takeyi mishi fiye da kowanne lokaci, idan ta kirama ba dauka zaiyi ba shisa bata kwatanta ba. Haka kawai sai taji kanta ya fara mata nauyi, kamar wadda rashin lafiya ke son kamawa, takalmanta da ta shiga dasu cikin dakin sosai ta cire tana turawa gefe wajen tebir din. Kwanciya tayi sosai, a hankali ta zame dan mayafinta ta ajiye a gefenta. Wani irin yanayine daya hade mata da wanda ta shigo da shi da karatun wani labari a group ya taso mata da shi harya darsa mata son ko da ganin Rayyan ne.
Tunda take a duniya bata taba jinta a irin yanayin nan ba, kamar wadda take yawo a wata duniya ta daban, kamar tana cikin mafarkin da idanuwanta suke a bude haka take ji, shisa ta lumshe idanuwanta tana tunanin yanda akayi su Bilal din suka saka gado a maimakon katifa kawai a dakin nasu. Tana kuma tunanin yanda suka kyauta saboda taji dadin kwanciyar sosai. Kamar a cikin mafarki haka taji shigowar Bilal da harya kusa makaranta aka kira shi aka fada mishi Malamin ba zai sami damar zuwa ba, yaji dadin hakan saboda bashi da natsuwar daukar darasin ko da anyi.
Hankalin shi baya tare da shi sam, har sanda ya shiga dakin, ya kuma mayar da shi ya tura kamar babu kowa a ciki, shisa ko kadan bai hangi Layla da take kwance can karshen gadon su ba, ga kuma net da ya tattare ya kai can karshen, ga duhun dakin dan ma sun saba, kamar ta mirgina ne tana nade kanta da shi, da wahala kayi zaton akwai mutum a wajen. Balle kuma Bilal din da hankalin shi na tare da kalaman Rayyan din da suke ta fadar mishi da gaba tunda ya fade su, lafiya kalau ya sauke shi ta sha, sai dai yanata kallon shi, kallo da yake cike da tarin ma'anoni har saida ya saka shi tambayar
"Hamma... Lafiya kuwa?"
Da alamun damuwa da Bilal din zaice bai taba ganin kalarta ba a fuskar Rayyan din yace
"Zuciyata namun wani irin Bilal"
Tsoro Bilal yaji ya baibaye ta shi zuciyar, Rayyan bai cika fadar abubuwa irin hakan ba
"Ko dai zaka hakura da tafiyar ne? Idan zuciyar ka bata natsu ba ka hakura"
Kai Rayyan ya girgiza mishi
"Bana jin ni ne"
Cike da rashin fahimta da kuma son karin bayani Bilal din yake kallon Rayyan, cikin idanuwa Rayyan din ya kalle shi wannan karin
"Ka kula da Layla, ka kula mun da Layla kaji Bilal, zuciyata na mun wani iri"
Kai ya daga mishi, saboda yanayin shi yasa ko kishin daya sabaji sam bai taso mishi ba
"Ta ce tana so na, jiya tace tana sona kamar bata san nasani ba tuntuni"
Cewar Rayyan, saboda saida suna kan hanya yake tunanin babu wani bakon abu a cikin kalaman Layla, abune daya riga ya sani tuntuni, ya riga yasan tana son shi, a cikin duk wani riko da zatayi mishi yasan hakan. A yanda take dawowa wajen shi bayan ya koreta ya karanci hakan, tana son shi duk tarin duhun da yake baibaye da shi bai hana zuciyarta doka mishi ba. Da sanyin murya Bilal yace
"Ni ma ta fadamun..."
Ganin kallon tashin hankalin da Rayyan yai mishi yasa shi yin murmushin da yakejin ya fito daga wani waje daya tsage a zuciyar shi yana dorawa da
"Tana son ka, ta fadamun tana son ka"
Kai Rayyan ya jinjina, damuwar da tabar fuskar shi tana dawowa sabuwa
"Shi sa zaka kula mun da ita, ban san meye nake ji ba, dan Allah Bilal"
A tsorace Bilal yace
"Zan kula da ita Hamma, kai dai ka kula da kan ka dan Allah. Ni duk ka tsoratani..."
Numfashi Rayyan ya sauke yana juyawa kawai. Maganganun shine suka yawaita a lokaci daya yau. Shisa suka tsorata Bilal din, sai juyawa su yake a ran shi. Yana jin kamar wani abu mai girma na shirin faruwa da su yau din nan. Shima ta shi zuciyar bugawa takeyi, ruwan daya gani a roba shiya dauka ya kwance yana kafa kai ya shanye, na karshen na sauka bakin shi da wani dandano daya kasa ganewa. Anan ya tsaya yana mayar da numfashi, wayar shi ya zaro daga aljihu ya ajiye akan tebir din, wani irin sama-sama yake jin shi, banda yanayin Rayyan babu abinda yake gani
"Allah ya sauke ka lafiya Hamma"
Ya furta jin zuciyar shi bata daina rawa ba. Agogon hannun shi ya kwance, kamar zazzabi yake son yi, da wahalar gaske gabaki dayan yau ya iya zuwa makaranta. Kayan jikin shi ya rage yana barin gajeran wando, shima wandon anan ya cire shi yana zare kafafuwan shi ya tsallake tunda Rayyan din da zai fada ya ajiye wando a kasa baya nan. Ya kama riga ya cire yaji kamar jiri zai dibe shi, babu shiri ya zauna a gefen gadon batare daya juya ba balle yaga Layla, kan shi ya dafe cikin hannuwan shi biyu. Da gaske duniyar shi ce take wasan kura da shi. Ya gwada mikewa yafi sau biyar yana kasawa saboda yanda jiri yake dibar shi, babu shiri ya kwanta ko zai samu sauki. Daga nan ba zai ce ga iya lokacin daya dauka baisan abinda yake faruwa a duniyar ba.
Kamar a mafarki haka Layla ta bude idanuwanta tana ganin komai na rabe mata biyu
"Hamma..."
Ta kira a cikin kanta ganin Bilal din a kwance a gefenta, sai taga tazarar da take tsakanin su tayi mata nisa, ga yanda jikinta duka yai nauyi sanda taja shi tana matsawa sosai kusa da shi
"Hamma"
Ta sake kira tana jin ashe gara da tazo, ashe Rayyan bai tafi ba, watakila kuma daya daga cikin mafarkan da ta sabane na shi, saboda yanayin ta ya nuna haka, tana jinta kamar tana yawo a gajimare, hannunta ta dago tana dorawa akan fuskar shi, fuskar da take mata kyau a kowanne yanayi, duk da duhun dakin ya hana mata ganin shi sosai, sai tarin kasumbar da yake fuskar shi. Kamar yanda take jinta a mafarki hakama ya kasance a wajen Bilal, dumi yaji ta inda bai taba zato ba, dumi yake ji akan kirjin shi da wasu sassa na jikin shi inda Layla ta kwanto, sai kan fuskar shi da sam baisan meye a kai ba, har saida ya kai na shi hannun yana kama nata cikin na shi.
Ya sha ganin hannuwanta, ya sha hasaso yanda zasu kasance a cikin na shi, amman yau daya jisu a cikin nashin, a duniyar da yake suna dayane yazo mishi
"Aisha"
Ya furta iya kan shi yana kara rikota a jikin shi, yanajin yanda bugun zuciyar shi ya karu har cikin idanuwan shi da suke a rufe, yanda ta biye shi na kara tabbatar da mafarkin da yakeyi. A cikin su babu wanda ya dawo hayyacin shi har sai da Layla taji abinda yake faruwa ya girmi duniyar da take tunani ta mafarki ce, ya kuma girmi duniyar da take ciki gabaki dayanta, a dai-dai lokacin da Bilal ya rabata da Martabar da bata san haka take ba a duk lokuttan da Mami take kira mata ita sai yau da tashin hankalin rabuwa da ita ya wujijjigata yana fisgota daga duniyar da ta fada zuwa ta mutane, lokacin da ta bude idanuwanta tana son saka duk wani karfi da zata iya tattarowa ta ture Bilal din.
Tashin hankali yayi kadan a yanayin da take ciki, saboda taji muryar shi a kunnenta da wani irin yanayi yana furta
"Aisha... Aisha"
Muryar da yanayin bai hanata gane waye ba, sunan daya kira na sake tabbatar da firgicinta, azabar da take ratsa ruhinta ta girmi mafarki tabbas da ta fassara abinda yake faruwa din da mummunar mafarki, kuka da ihu take son tattarowa daga wani loko da tashin hankalinta yake faruwa, dakyar ta samu ta iya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
A matuqar wahalce tana jan numfashin da ta fitar da sauran natsuwar daya rage mata kafin azaba da tashin hankali su sake rabata da hankalinta...
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 9, 2020
18
Da wani irin ciwon kai ya sauka, ga alamun zazzabi yanaji. Ya kira wayar Layla yafi sau goma bata daga ba. A ranaku da ba irin na yau ba, kira daya idan yai mata bata daga ba shikenan. Ya san in tazo zata kira shi. Amman yau din wani irin tsoro yake ji da bai san dalilin shi ba, tsoron ma bai kara yawa ba sai da ya kira Bilal shima bai daga ba. Bilal da ko karatu yake sai ya mishi magana zai ajiye waya ya natsar da hankalin shi waje daya. Idan jarabawa akeyi ma, kamar yaro haka zai ce
"Ban wayar nan Bilal..."
Zai saka a key ya ajiye yana fadin
"Na ajiye Allah kuwa Hamma"
Sanin halin shi yake saka Rayyan din kin yarda, sako na shigowa zai sake dauka, shisa yakan mike ya dauki wayar ya ajiye a gefen shi
"Kayi abinda yafi danna wayar muhimmanci"
Yakan fada mishi, ya rasa dadin me suke ji shi da Layla kan danne-dannen wayar nan. Ji yake kamar ya tsaya a hanya ya samu wata motar da zata juya da shi Zaria saboda rashin natsuwar da yake tare da ita.
"Allah Ka san halin da nake ciki, Ka san damuwa ta, Ka san zuciyata ba zata iya daukar wani abin ba. Allah Ka sa lafiyar su"
Shine abinda yake fadi yana maimaitawa, duk inda network zai dawo mishi sai ya gwada lambar Bilal da ta Layla, amman duka tana shiga basa dauka ne. Yana sauka a tashar ya tsaya ya kira Bappa da bugu daya ya daga yana sallamar da bai jira Rayyan din ya amsa ba ya dora da
"Har ka karaso ne? Ka jirani a tashar in zo yanzun"
Rayyan din dan dakuna fuska yayi, saboda Bappa nayi kamar sun san juna, kamar sun saba ba yau bane farkon maganar su
"Eh, ok tam"