← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 93

Sashe 81

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan kwashe kayan, munyi maganar da Ayya, ka bar shi karshen makon nan da yardar Allah zan shigo Zaria din"

Numfashin Rayyan ya sake saukewa

"Kar ka bayar da komai, duka komai da komai"

Duk da baya gani yasan kai Haris din yake daga mishi

"Babu abinda zan bayar, duka zaka zo gida ka samu kayan. Ka dai fito daga gidan idan kana can, kana jina, ka fito ka tafi...zaka iya ai ko?"

Dan murmushi ya kwacewa Rayyan

"Ba yaro bane ni Hamma..."

Yanajin dariyar Haris din, bai jira yace wani abu ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana katse kiran kafin ya mayar da ita aljihun shi. Da gaske kirjin shi zafi yakeyi, kasancewa a cikin dakin ya dawo mishi da abubuwan daya dauka ya rabu da su. Kasancewar shi a dakin ta saka mishi wasi-wasin da bayason zurfafa tunanin shi a kai sam. Shisa ya dauki shawarar Haris din ya fice daga dakin ya mayar da shi ya kulle yana fita daga gidan. Ko daya karasa ya shiga motar da ta mayar da shi Kaduna bai daina jin kirjin shi na zafi ba.

"Magana fa nake tayi maka"

Muryar Bappa ta daki kunnen shi tana dawo da shi daga tunanin daya zurfafa ciki. Mikewa yayi yana fadin

"Dole dai saika fitar da ni..."

Bappa bai kula shi ba ya juya, shima bayan Bappa yabi har suka fita daga gidan zuwa inda motar Bappan take suna shiga.

*

Ba zatace duka duniyar ta daina yi mata dadi ba, saboda yanzun duniyarta ta tattaru ta dawo cikin dakinta. Anan take gudanar da rayuwarta ta yau da kullum, ko da safe ba kullum take samun karfin zuwa su gaisa da Mami din ba. Sai dai ita ta shigo ta dubata, saboda cikinta daya fara fitowa sosai, bata son Mami na ganinta, kowa ma na gidan bataso yana ganin ta. Sai taga kamar basa ganin komai a tare da ita, kamar hatta da sunanta ya bace, banda cikinta babu wani abu da kowa yake gani a tattare da ita yanzun. Jafar ne kadai yakan fito da ita falo wasu lokuttan.

"Malama fito kiga wani abu"

Yakan ce, duk iya kokarin shi na ganin bai nuna cikin jikinta ya dame shi ba, a muryar shi takan ji canjin da ya faru da rayuwar su gabaki daya. Ta kan biye Jafar din suyi kallo tare har su danyi hirar film din, amman gabaki daya babu wani abu da take jin dadin shi. Ba dai ta iya cin wani abu sai mai manja, in dai ba girkinta ita kadai Mami takeyi mata ba to duka dakin su an koma cin abinci ne da manja. Shima kawai wasu lokuttan takan ji idan bataci ba kamar zata mutu, sai kuma yoghurt da baya yanke musu a cikin fridge.

Lokutta kamar irin yau da take zaune dafe da cikinta, hawaye ne masu ciwo suke zubar mata, tun tana daukar zasu kare har ta daina yanzun. Takan yi kukan halin da take ciki, takan kuma yi kukan rashin Bilal ba kadan ba, a hankali a hankali mutuwar ta dinga tabata kamar ciwonta ba zaiyi mata sauki ba. Anisa kuwa yanzun ba sosai suke magana ba, tunda Layla ta fada mata anwa Abbu transfer ne zuwa kudu, shine suka koma gabaki dayan su, sukan gaisa lokaci zuwa lokaci ne. Zuwa yanzun makaranta ce karshen abinda yake ranta, ta rigada ta cire karatun daga zuciyarta.

Rayyan na kokarin kiranta, shima batasan me zatace mishi ba a yanzun. Ko wanka ta shiga bata tsayawa kallon kanta, saboda bata son ganin yanda gabaki daya jikinta ya canza. Jiya ma sai taga kamar har fuskarta ta canza, bata san ko dan ta jima bata kallo mudubi bane ba. Yau ma sam batayi marmarin kallo ba, da ta sau wata doguwar riga ta zira a jikinta sai ta koma kan gadonta. Idan har bata son ganin kanta, tana da yakinin Rayyan ma ba zaiso ganinta ba, ita da kanta ba zataso yaga canjin da yake tare da ita ba.

Zatayi karya idan tace zuciyarta bata mata zafi, amman a cikin abubuwan da ta nisanta zuciyarta da su, samun Rayyan na daya daga cikin su. Ba abu bane mai sauki, amman da duk ranar da zata wayi gari da yanda take kokarin yin wani tunani na daban, tana hasaso dirowar abin da yake cikinta. Tana kuma tunanin yanda rayuwa zata kasance mata bayan hakan, duk ta yanda ta hasaso abin ba mai sauki bane, tsoro da zullumi sun bata taimako wajen danne Rayyan can kasan zuciyarta.

Alamun shigowar sako take ta ji, hawayenta ta share tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta dauki wayar tana budewa ta duba. Sai da taji zuciyarta tayo wani tsalle kamar zata baro kirjinta, mamaki na dirar mata ganin Rayyan ne yayi mata magana a manhajar whatsapp

"Layla"

Sakon shi na farko kenan

"Na siya waya"

Ta sake karantawa

"Bakya magana dani kwana biyu ko?"

Murmushi tayi me ciwo, ta fara rubutu yafi a kirga tana gogewa cikin rashin sanin abinda ya kamata tace, kafin ta yanke hukuncin fadin gaskiya, abubuwan da suka rage mata basu da yawa, ba zata bari gaskiyarta ta kwace mata ba, musamman ma a wajen shi

"Komai ne baya mun dadi Hamma, duniyar duka ta tsaya mun waje daya"

Kallon shi tayi yanata rubutu

"Zai wuce wata rana, ki daure"

Kai ta jinjina kawai, har zata ajiye wayar saboda bata san me zatace mishi ba ya sake fadin

"Ki turomun duka hotunan mu"

Bata san me yasa taji cewa harda na Bilal yake nufi ba, duk da bai ambaci suna ba. Jikinta har bari yakeyi lokacin da ta shiga gallery din, tana binciko hotunan da ta kasa dubawa duk yanda taso yin hakan. Idanuwanta cike taf da hawayen da batayi kokarin hanasu zubowa ba ta fara tura mishi duk wani hoto na Bilal da taci karo da shi, kafin ta tura mishi nashi da take da shi, sai na shi shida Bilal wanda idan Bilal ya saka takan ce ya tura mata. Kuka takeyi sosai lokacin da ta gama tura mishi dan harda hotunan Aisha da Bilal din da yawan gaske a wayarta. Hotunan da suka sakata tunanin Aisha da halin da take ciki a yanzun.

Bataji shigowar Mami da ta juya a hankali ba, dan Abbu yace ta dinga barin Layla tanayin kukan, dan akwai sauki a cikin shi. Yana nufin tana fito da abinda yake damunta bata barshi a cikinta ba. Amman da wahala, batasan ba cikin Layla bane kawai jarabawa harda damuwar da take gani shimfide a fuskarta a duk rana. Shi kadai yakan jijjiga zuciyarta. Amman ta bar komai a hannun Allah, shi daya kadarta musu ya san yanda zaiyi dasu. Sharar da take kitchen ta dauka dan ta fita da ita can harabar gidan ta zuba a babban wajen da suke zubawa sai a fita da ita duk sati.

Ta dawo ne taci karo da Ayya, zasu iya haduwa irin wannan fiye da goma basu cewa juna komai ba, shisa abin yayi mata wani iri yau da taji tace

"Maryama"

Mamakine bayyane a fuskar Mami sanda ta juya, saboda yanayin da taji a muryar Ayya bana tashin hankali bane ba

"Ya Layla?"

Ayya ta tambaya tana kallon Mami din, ba abinda taso fadi bane ba, a kwanakin nan da suka wuce mata da wani irin yanayi, baccin kirki bata samu. Saboda tana tunanin makomarta, tana kuma tunanin abinda zata cewa Allah idan mutuwa ta risketa da hakkin mutane da yawa a kanta. Idan ana maganar lahira bata tunanin wani girman kai na da amfani, ta sha fitowa da nufin samun Mami har cikin daki ta roki gafararta amman sai ta tsinci kanta da kasawa. Yau dinma na zatace ga abinda ya fito da ita ba, kuma sai ta hadu da Mami din, ta dauki hakan a matsayin wata ishara ta samun sauki, ba saita taka kafarata zuwa dakinta ba.

"Tana lafiya. Alhamdulillah"

Mami ta fadi tana shirin raba Ayya ta wuce

"Maryama..."

Ayya ta sake kira tana saka Mami tsayawa a karo na biyu

"Ban san ta ina zan fara ba"

Cewar Ayya da muryarta take rawa

"Cutar da nayi miki wanda kika sani da wanda baki sani ba..."

Kafin ta karasa Mami ta katseta da fadin

"Dan Allah Maimuna... Idan kin taba cutar dani ko kokarin hakan Allah ya zama shaida yau na yafe miki. A zaman mu ba zance ko a tunani ban soki da abinki ba, ki yafe mun nima"

Numfashi mai nauyin gaske Ayya ta sauke tana jin kamar an dauke mata dutse a kirjinta

"Nagode... Ba zan miki karya ba, hakan baya nufin ba zan neme ki da rigima ko ba zanyi tashin hankali ba"

Murmushi Mami tayi, murmushin da ta kwana biyu batayi kalar shi ba. Batace komai ba ta raba Ayya ta wuce, in dai wannan ne ta saba da shi, mai hali baya barin halin shi akace. Kishi da rigima halayen Ayya ne, batajin kuma wani abu zai taba canza hakan, bata tsammaci maganar da sukayi yanzun ta saka su zauna kamar aminan juna ba, ko su fara hira da mutuncin da basayi a da. Idan akwai abinda ya fara sakawa take ganin girman Ayya shine matar bata iya munafunci ba, abinda yake ranta ne zata nuna maka, idan kaji haushi ma bai dame ka ba.

Ko da wasa bata taba nuna tana sonta ba tun shigowarta, tana kula da yanda taso ta ture har yaranta, sai Haris yayi nasara a kanta, duk da batajin tana son sauran kamar Haris. Da zama da munafiki da zai nuna yana sonka a gabanka a bayanka ba haka ba, gara ka zauna da wanda zai kalli fuskarka ya fada maka baya yinka, hakan ba zaisa ka daga burinka a zaman ku ba. Rigimar Ayya ta jima da sabawa da ita, kamar yanzun yanda take jin wata rana zata zo da zasu saba da wannan yanayin da suke ciki, ranar da komai zaiyi musu sauki. Ayya ma dakinta ta wuce tana jin wani sauki ya saukar mata, tana jin yanda ta rage kadan daga cikin hakkin mutanen da take ji ya shake mata wuya.

*
Chapter 81 · 0% Book details