← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 93

Sashe 71

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawayen da suka zubo mishi Bilal ya share yana jin kalaman Ayya na saukar mishi, suna ratsa wajaje da yawa a cikin jikin shi, suna kuma sanyaya zuciyar shi da take matukar ciwo. Ayya kenan, Ayyar shi, uzuri take son mishi tun kafin taji bayanin shi, bata da wata tambaya, saboda a idanuwanta ba zaiyi laifi mai girma haka ba, wannan ce girman kaunar da takeyi mishi, kaunar da yake jin ya ha'inta yau, saboda kuka takeyi, shine sanadin kukan da takeyi. A muryarta yaji shisa ya kasa kallonta, Abbu yake kallo da baice komai ba

"Abbu..."

Bilal ya kira muryar shi na karyewa, Abbu ya kasa kallon shi, ya rasa abinda yake ji, amman so yake kowa yabar shi, ya dan zauna shi kadai, shisa yace

"Shikenan kai sai ka aure ta... Ku fita dan Allah, ku dan barni"

Rayyan da yake tsaye yana jin shigi da ficen duk maganganun su batare da sun taba zuciyar shi ba yaji maganganun Abbu sun shiga wajen da suka zauna daram suna kasa fitar mishi. Ya dauka babu wani abu da zasu fada da zai taba shi, ya gama jin su duka daga bakinta da na Bilal. Sai yanzun da yaji Abbu na kiran Bilal ya auri Layla, bayan cikin da yake jikinta da ba nashi ba, yanzun ita din ma ake so ace ba tashi bace ba.

"Abbu"

Rayyan ya kira sauran kalaman na makale mishi

"Dan Allah ku fita ku barni"

Abbu ya sake rokon su, saboda muryar Rayyan da yaji na kara saukar mishi da wani yanayi daban. Ganin duk suna mikewa yasa Rayyan sake kallon Abbu cikin tashin hankali, so yake ya fada mishi shifa baice ba zai auri Layla saboda wani abu ba, ya fadane dan shine hanya daya kawai da yake da ita da yasan zataji kalar ciwon da yake ji. Da yace baya son ta ya dauka su duka kamar zuciyar shi sunji karyar da yake yi. Mami ita ta fara barin dakin da Layla a jikinta tana wani irin kuka da yake ji a kasan zuciyar shi.

"Ahmadi"

Yaji Ayya ta kira, tana saka shi kallonta, da zuciyar shi yake rokonta da ta fadama Abbu ya janye kalaman da yayi, amman sai yaji tana fadin

"Dan Allah kar kaga laifin shi, ka tsaya yayi maka bayani... Bilal kayi mishi bayani kaji"

Kafin yayi magana Abbu ya kalli Ayya

"Dan Allah Maimuna, naji iya abinda zai tsaya dani har karshen rayuwata, dan Allah ku barni, kuje ku barni dan girman Allah"

Hawayenta Ayya ta goge tana mikewa, harta yi taku daya Bilal daya fara magana yana sakata taja ta tsaya cak

"Ban da uzurin da zan baka Abbu, bani da shi... Nayi laifi na sani. Ko bakin da zance ka yafe mun bani da shi"

Karasawa tayi ta kama hannun Bilal din tana jan shi, dole ya mike. Zasu dawo ita da Bilal suyiwa Abbu bayani yanda zai fahimta. Suna ficewa Yaya Ayuba ma ya mike, su duka suna bukatar yin bacci kan maganar, gobe ya dawo su kara sanin yanda zasuyi. Ko bankwana baiyi wa Abbu ba ya fice daga dakin. Rayyan ne yayi tsaye, ya kasa tafiya, yana kallon Abbu ya kai hannu ya share kwallar da ta zubo mishi

"Rayyan bakaji nace ka tafi ba?"

Kai Rayyan ya jinjina mishi, yaji shi, yaji me yace tun da farko, ya kasa tafiya ne saboda akwai tarin maganganu da yake son yi da Abbu, watakila yau ba ita bace ranar daya kamata, amman ya kasa tafiya

"Abbu baka mamakin ya akayi nake daki daya da kai?"

Dagowa Abbu yayi yana kallon Rayyan din, yau duka bashida wajen mamaki kuma

"Karka ce in tafi. Abbu karka koreni yau kawai da nake jin zan iya zama daki daya da kai na lokaci mai tsayi batare da iskar wajen ta mun kadan ba"

Kai Abbu ya jinjina ma Rayyan din. Shi kam zaman ma bashi da karfin yin shi, shisa ya kwanta, duniyar duka na mishi lilo, ya rasa kalar tunanin daya kamata yayi, ya kuma rasa abinda yake faruwa da su haka, abinda yake faruwa da yaran shi. Kafin kalaman Bilal su fara mishi yawo suna saukar mishi da zazzabi. Kuskure shine abinda Ayya ta kira komai da akalar lamarin ta juya kan Bilal, shima bashi da wasu kalamai da zaiyi amfani da su, kalmar iri daya ce da ta Ayya, kuskure. Idanuwan shi ya rufe yana son ya hada ya rufe tare da duk wani tunani amman abin ya faskara. Ya kasa rufe tunanin da yayi mishi cunkus.

Rayyan kam ba zaice ga lokacin daya dauka a tsaye ba, yasan dai kafafuwan shi da kansu suka gaji suna kaishi kasa, da yake akwai kafet cike da dakin nan ya kwanta shima. Ciwo yake ji, ciwon da yake bukatar lallashi ko ya yake, kuka yake nema watakila idan yayi irin wanda Layla takeyi zai samu sauki. Abu daya ne yake mishi yawo, dan yace ba zai auri Layla ba baya nufin yana son ta kusa da wani, balle ace wanin ya kasance Bilal, mutuwa kawai zaiyi ya tabbatar yanzun. Dan kirjin shi kamar an zauna a kai haka yake ji. Me yasa Bilal zai mishi haka? Ya kasa samun wannan amsar, idan kuskure zaiyi me yasa sai akan Layla?

Duk da dazun yana jin surutun da yake yi a bakin kofa, ya zabi yin kamar baiji shi bane ba. Shisa bayason juya kalaman, baya son yin wani tunani da zai hada da yiwa Bilal uzuri, abinda yayi mishi ba zai yafu ba, ba zai iya yafe musu ba daga shi har Layla. Har cikin kasusuwan jikin shi yake jin hakan, yana so suji ciwo kalar wanda shima yake ji. Amman hakan baya nufin yana son ganin Layla a tare da Bilal, yama Abbu zai fara cewa Bilal ya auri Layla. Yana tunanin baccine ya fara fisgar shi, dan kiran sallar farko da akayine ya saka shi bude idanuwan shi dakyar yana tunanin inda yake.

Kafin komai ya dawo mishi yana saka shi dafe kirjin shi da yake ciwo. Dakyar ya iya mikewa, ko ina na jikin shi ma ciwo yakeyi. Abbu da yake kwance ya kalla, sai da yaga ya juya kwanciya sannan ya fice daga dakin. Fitilun gidan duka a kunne suke yau. Dakin su ya nufa, yana shiga zuciyar shi tayi wata irin dokawa da yanayin yanda yaga an fiffido kaya, tun bai karasa cikin dakin ba kafafuwan shi suke rawa, kan tebir din shi yaga takarda a ajiye, ya dauka yana budewa, da daya daga cikin fensiran zanen shi akayi rubutun da yake ganin yana rabe mishi biyu, saida ya runtsa idanuwan shi ya bude su tukunna ya iya karantawa da muryar Bilal a zuciyar shi

"Nayi kuskure na sani, ba zan kara shiga tsakanin ka da Layla fiye da yanda nayi ba Hamma, ba saika yafe mun ba, dan Allah ita ka duba zuciyarka, nasan akwai wajen da zai iya yafe mata, ka yafe mata. Ka dora duka laifin a kaina. Nagode da tarin kaunar ka, ka kula da kan ka, ka kula da Ayya"

Ya karanta wasikar yafi sau ashirin kafin asalin ma'anar ta ya zauna mishi, cikin wani irin tashin hankali ya fito daga dakin, tun daga bakin kofar yake fadin

"Ayya!"

Yana kara kwala mata kira harya karasa bakin kofar dakinta inda suka hade saboda daman ba bacci takeyi ba, kiran shi ne ya sata mikewa tana tahowa da sauri, ko da yana yaro kome yake bukata bai taba mata irin wannan kiran ba, yana ganinta kafafuwan shi na kasa daukar shi

"Ayya ya tafi... Ayya tafiya yayi... Bilal tafiya yayi ya bar ni... Dan ba zan yafe mishi ba sai nace ya tafi? Me yasa zai tafi? Ina ya tafi Ayya?"

Duka zancen shi a baibai take jin shi, jijjigata Rayyan ya fara yi, saboda yasan babu inda Bilal zaice bai fada mata ba, gara ta gaya mishi ya bishi ya dawo da shi.

"Ki fadamun inda ya tafi Ayya... Kinga ni me yace mun..."

Wasikar Ayya ta karanta, fahimtarta ne yake mata wahala saboda babu yanda Bilal zai tafi wani waje bata sani ba, balle ace irin wannan tafiyar, ture Rayyan tayi tana nufar dakin su ya rufa mata baya, kayan Bilal ne tagani a zube, batayi magana ba ta sake fitowa tana jin Rayyan na biye da ita har cikin dakinta inda ta dauki wayarta, tana mamakin yanda komai yayi mata shiru, lambar Bilal ta kira a kashe, duka lambobin shi a kashe, Rayyan ta kalla da shima yaji a kashe ne, kai dai kawai yake girgiza mata, duniyar na kara hargitse mishi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su da wani irin matsananincin tsoro daya ziyarce shi

"Ayya dan Allah..."

Cewar Rayyan yana dafa bango ya sulale kasa, a cikin daki yake, amman duniyar duka yake ji tayi mishi fili, babu kowa a cikinta sai shi kadai, bai san inda zai nufa batare da Bilal ba

"Ayya ki ce mun bai tafi ba, dan Allah kice ya dawo"

Rayyan yake fadi yana jin iska ta daina kaiwa cikin kan shi, kafin wani irin duhu ya rufe mishi idanuwa ruf, yana saka Ayya tsugunnawa ta riko shi kafin ya karasa kaiwa kasa, kan shi a jikinta yake da wani nauyi da batayi zato ba, nata kan ta dora a na shi, tunda take bata san akwai tashin hankali makamancin wannan ba, a wahalce ta dago, muryar da zatayi amfani da ita wajen neman taimako take nema ta rasa yau.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 1, 2021.

27

Ko sallamar Abbu daya dawo daga masallaci kan shi tsaye ya nufo bangaren ta bataji ba. Zuciyar shi na wata irin dokawa ganin ta rike da Rayyan din

"Rayyan..."

Ya kira muryar shi na fitowa yar karama saboda tsoron da yake ciki.

"Me ya same shi? Me ya faru?"
Chapter 71 · 0% Book details