← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 93

Sashe 8

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta alaqanta hakan da yara uku duk maza da Maryama take gani ras a gabanta, Haris, Jabir, sai kuma Naadir. Shisa take daddaga mata kai har haka, ko da gadone ta fita a cikin gidan yanzun, tunda ita mazan ta biyu, sai mace guda daya. Duk yanda take jin cewar Bilal nata ne, duk kuma rashin banbancin da Ahmadi yake nunawa tsakanin Bilal da yaran shi ba zata hada shi a cikin magadan Ahmadi ba. Tasan wannan har kasan ranta. Akwai shakuwa mai karfi tsakanin su Khalifa da yan uwan su, zata jinjinawa Ahmadi ta wannan fannin.

Tun tana nesa-nesa da ganin yaranta bangaren Maryama har ta fara saduda, na rana daya bata taba ganin Maryama tayi kokarin cutar dasu ba, a fuska ma bata nuna wannan alamar ba, duk da Gwaggo kance mata

"Mugu bashida kammani, wanda yake kusa da kai yafi samun damar cutar ka Maimuna, kiyi kaffa-kaffa da yaranki"

Tana kuma iya kokarinta, tunda har yanzun da wahalar gaske Maryama ta basu abu su karba, ko menene kuwa. Itama Maryama tun abin na damunta harya daina, bata kuma fasa gwada basu duk abinda suka samu tana baiwa nata yaran ko tana ci ba. A ganinta dai ta fita hakkin su tunda ta basu, zabinsu ne karba ko kin karba. Gara ma Bilal da ta rasa kalar yaron, tunda take sau hudu hannunta ya taba kaiwa jikin shi da sunan duka, shima akan Maryama ne, indai yana son abu ta bashi saiya karba yaci, duka dukan da tayi mishi har wani zazzabi tayi, zata rantse tafi shi jin zafin dukan.

Tana son yaranta, tana son yaranta fiye da tunanin mai tunani, amman daban take jin Bilal, har a ranta daban take jin shi, bayan kauna akwai tausayin maraicin yaron da yake manne a zuciyarta. Gashi da manyance na ban namaki, kuma duk yafi shakuwa da ita a cikin yaran, zaka gansu suna tsakar gida suna wasa, amman yafi zabar zama a kusa da ita akan ya shiga cikin yan uwan shi suyi wasa. Ko kwance take shiru tana tunanin duniya sai Bilal ya shigo ya hana mata wannan tunanin, da shirmen shi da hirar shi takan ji sauki a ranta.

Tana jinjina yanda Malam Mainasara yace Maryama zata iya cutar da su Khalifa, a karo na farko da take kyautata zaton ta akan Maryama

"Idan baki tashi tsaye ba, sai ta sabauta miki yara, so take babban danta ya gaje komai na gidan, yafi kowa a zuciyar mijin ku"

A kasan shakkun da takeyi akan maganar akwai tunani barkatai da ya jefa kwakwalwar ta, lokuttan da takan ga kowanne yaro zaune a kasa, amman Haris nakan cinyar Ahmadi, ko wasu lokuttan da zai baiwa kowa abu, sai taga ya diba cikin nashi ya karawa Haris, sosai zuciyarta ta cika da tsoron tabbacin maganar Malam Mainasara. Amman zata gwada shi taga idan aikin shi yana ci kafin ta yarda da bugun kasar da yayi mata. Dan harta gaji da wannan tarkacen Malaman na Khadi da Gwaggo, kowanne a cikin su fadar yanda ayyukan Malaman yake, sai a kanta ne hakan yake zama daban, sai a kanta ne aikin bayaci tunda ga Maryama nan daram a gidan Ahmadi, har dinki takeyi da a cewar Ahmadi ai daman tun a gida tanayin abinta.

Gidan nasu kullum cikin mutane yake da sukan kawo dinkuna ko kuma suzo karba, dan dinkinne yasa Maryama harta datsa mata magana kwanaki

"Ina da ayyuka da yawa a gabana, ina da hidindimu Maimuna, ki daina tunanin ina da lokacin yi miki wani abu. Wallahi banda wannan lokacin, gidane dai yanzun na fara zama a cikin, saiki bari idan Allah ya tsara zan rigaki kwanta dama sai kiga an fitar miki da gawata daga gidan nan"

Maganganun sun mata zafi kuwa, sun kuma sakata tunanin fara sana'a itama, amman ta rasa, ta dai yiwa Ahmadi magana, yace zai tayata tunani, watakila ko takalma ne sai ya dinga kawo mata, ko ta tara kudade ta bayar sai ya saka mata a shagon shi ana juyawa, duk ribar saiya kawo mata abinta. Ko babu komai a ganin Maimuna zata samu wadatattun kudin da zataci gaba da naimarwa kanta da yaranta taimako wajen kariya daga sharrin masu sharri. Yanda Malam Mainasara yace tayi da rubutun haka tayi kuwa, sai dai tayi sa'a Ahmadi ya hanata fita da ranar komawar ta zagayo.

Sai da akayi wajen kwanaki takwas tsakani sannan ta sami dalilin da tayi amfani dashi wajen fitar. Mamaki ta dingayi tana karawa, saboda karyayyun tsinkayen da Malam Mainasara ya batane ya juye cikin wani farin kyalle ya nannade, ya jujjuya a gaban idanuwansu ita da Khadi, ana bude kyallen saiga tsinke mike kyam kamar ba'a karya shi ba

"Ma shaa Allah, aiki yayi yanda ake so. An samu damar karya sihirin"

Farin ciki fal ranta, farin cikin da batayi wasu dakika tanayi ba, tsoro ya maye gurbin shi, jin Khadi tace

"Saura raba soyayyar Haris da Ahmadi Malam, ya za'ayi da yaron?"

Zungurinta Maimuna tayi cikin tashin hankali, Khadin na zabga mata harara, taga alamar ko kadan Maimuna ba zatayi hankali ba har yanzun. Har wani abin tausayine a batun daya shafi kishiya

"Ni dai kar ayi mishi wani abu, idan sihirine a warware abin ya kaunace shi dai-dai da sauran yaran"

Maimuna ta fadi cikin rawar murya, ba jan yaran take a jikinta ba sam, bata dai tsangwamar su, idan sun zo bangarenta su zauna, idan abincine suka samu su Khalifa naci sukan ci dasu, suyi wasan su. Amman Haris har rawar jiki yaron yakeyi idan ta saka shi ya miko mata abu, ko kuma Ahmadi ya aiko shi bangarenta, da gudun shi yakan shigo. Harda murmushin nan da duk idan yayi sai taga kamar Ahmadi. Batasan kome takeji akan su Haris kauna bace, tafi alakanta shi da shakuwa da kuma shiga rai irin wanda yara suke dashi, wani garin magani ya dauka ya bata

"A ruwa zaki dan barbada yasha, shikenan"

Karba dai tayi kawai badan zuciyarta ta aminta ba, haka ta dawo gida tana jinta kamar marar lafiya. Duk shigowar dasu Haris din sukayi ranar ta kasa ko da mikewa balle ta barbada maganin ta san yanda zatayi ta bashi. A haka Ahmadi ya shigo ya sameta, yaran suka tarye shi da gudun su suna fadin

"Abbu sannu da dawowa"

Kamar yanda suke kiran Ahmadi da shi, Maryama kuma Mami. Amman duk a cikin yaran Haris ya zabi ya dauka, sai ta bishi da kallo, bataso yanda ya tabbatar mata da zancen Malam Mainasara ba, sam bata zaci Maryama na da zuciyar wannan muguntar ba. Ita kam ba zata saka ido Ahmadi ya dinga nuna bambanci a tsakanin yaran ba.

"Duk yaran baka ga kowa ba sai Haris kenan?"

Ta bukata, tsareta Ahmadi yai da idanuwa, duk rashin kunyarta tana bala'in shakkar shi, yanzun ma tsintar kanta tayi da sauke nata idanuwan. Saida ya sallami yaran ya basu alawa da biskit din daya siyo musu tsaraba, suka fice daga dakin, sannan ya kara kallon ta

"Me yake shiga kanki ne wani lokaci?"

Kallon shi tayi itama

"Ni babu abinda ya shiga kaina, amman kana nuna bambanci tsakanin yaran. Inma Haris kafi so bai kamata kana nunawa karara ba, ko ni zuciyata bata sosu ba, yara ai suna gani, kuma yaro baya mantuwa"

Numfashi Ahmadi ya sauke, Allah ne shaida yana kaunar yaran shi, idan ma akwai wanda yakeji daban a cikin su Zubaida ce. Kaunar da yake ma yarinyar daban take, sai yake jin kamar tafi kowa bukatar kaunar shi, dan kasancewarta mace, ko kallon su yake yana hasaso yanda rayuwa zata kasance musu, sai ya dinga ganin su Khalifa sunyi aure da iyalinsu suna zuwa duba shi badan suna bukatar shi ba, dan kyautatawa kawai, amman yakan hango Zubaida har karshen rayuwar su tana bukatar kulawar shi, kuma ba zataji kamar ta girmi taimako daga wajen shi ba.

Haris na da kwalafaci, a iya zaman da yake da yaran shi yana kula da dabi'un su, Haris na cikin yaran da suke yunwar kulawa, ko yanayin shi ka gani yanda yake so yayi komai dan ya faranta maka ko zaka kula shi ya isa ka fahimta, ba bambanci yake nunawa ba, kaunar su yake nuna musu dai-dai bukatar su, amman idan yai kokarin fahimtar da Maimuna zata sauya zancen shi zuwa wani abin. Shisa ya sake zancen gabaki daya

"Yaya Ayuba kemun maganar kara bude wani shago, ina jin zan mishi zancen zaki kawo wani abu ko yaduka ne a siyo a juya miki...."

Kai kawai ta iya jinjinawa, ta kula da maganar Haris ne bayaso ayi. Shisa ta kyale shi, washegari kuwa da safe saiga yaran sun shigo dakinta, tana hada shayi. Zuciyarta na rawa ta sami kofi ta shiga kitchen, anan ta kwanto maganin da yake nade cikin karbun zaninta, sai take ganin kamar Ahmadi zai fito ya ganta, barbadawa tayi a kofi tana saurin zuba ruwan shayi a ciki, dan shekawa tayi, ko bai shanye ba inta samu ya kurba hakan ma ya isa. Tana shiga daki ta ajiye kofin a kasa ta nufi inda Bilal yake rike da cokali mai yatsu da batasan inda ya dauko shi ba karya cake ido ko wani waje. Kama shi tayi ta karbe cokalin, kallonta yakeyi da ido kawai tunda da wahalar gaske kaji kukan shi.

Tana juyowa taga kofin shayin da ta ajiye a hannun Rayyan, ya kuma daga ya kafa bakin shi

"Rayyan...."

Ta kira cikin tashin hankali, kafin ta karasa ta karbe kofin harya shanye. Dago shi tayi gabaki daya ta rikice

"Na shiga uku ni Maimuna.... Na shiga uku, Rayyan...."

Take furtawa tana tale bakin shi kamar hakan zai dawo da abinda yasha, kafin ta saka hannu tana taba fuskar shi, goshin shi da wuyan shi, har hannu tasa cikin rigar shi taji ko ya fara alamun zazzabi, bata taba tsorata irin haka ba, sauke shi tayi kasa dan sai buntsurewa yake yi tana tsugunnawa itama

"Dan ubanka ka tsaya kafin in kwada maka mari"

Ta fadi jikinta ko ina na bari da tashin hankali, dai-dai shigowar Ahmadi

"Lafiya? Me ya faru? Me ya same shi?"

Ya jero mata tambayoyin ganin yanda take a rikice

"Kamar wani abu naga yakai bakin shi, kafin inzo harya hadiye"
Chapter 8 · 0% Book details