← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 93

Sashe 43

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwanakin ko sallar daya kan tashi yayi sai jikin shi yayi matuqar nauyi. Bilal dai bai fasa mishi hira ba idan ya tashi, duk da baya iya ce mishi komai. Yana dai jin dadin hirar, fiye da yanda zai iya fada. Saboda ita kadai ce yake ji ta zame mishi katanga tsakanin shi da tabin hankali. Tun sanda ta shigo cikin motar yau da zasu dawo yake jinta a wajaje fiye da zuciyar shi, sai yake jin inda maganganun Abbu suka dauketa suka jefa yana budewa. Zai rantse yana jin idanuwanta na yawan neman fuskar shi kamar zasu huda kujerar da yake a kai su leqo shi. Bayan sun sauka ma haka, yana jin yanda take kokarin yi mishi magana.

Sai take kara mishi wahalar da yake ciki, saboda tana yi kamar ita ka dai take azabtuwa da nisan da sukayi da junan su. Duk yanda yake daurewa sai da tayi mishi magana

"Hamma..."

Kawai ta furta sai da tsikar jikin shi gabaki daya ta mike, komai yana neman kwance mishi, shisa ya daga gilashin motar. Jikin shi har bari yakeyi da son fita daga motar ya riketa a jikin shi, so yake ya zagaya hannuwan shi ya riketa dam, yaji duminta ko zai nutsar da hayaniyar da take cikin kan shi. Amman babu wannan damar, zaiyi duk kokarin da zai iya na ganin damar bata samu ba. Sanda suka karasa gida har wani numfashin wahala yake saukewa. Kayan su ma Bilal ne ya shigar musu da shi.

Basu huta ba suka fara share share, har wankin su labule sai da Rayyan din yayi. Yanajin Bilal na fadin

"Kabari a bayar a wanke mana"

Bai saurare shi ba, saboda yana son yin wani abu da zai rage mishi tunani. Sanda ya gama duk wani aiki da zai iya takalowa kan shi har azahar ta kusa, yanayin wanka ya fita yayi sallah ya dawo. Bilal ya sai musu biredi a hanya saiya dafa musu shayi, shi Bilal din yana zaune kan gado ya bude laptop din shi, Rayyan kuma yana zaune akan kujera da kofin shayin da yayi mishi zafi a hanny yana hurawa a hankali da iskar bakin shi cikin son ya huce.

Wani series film ne Bilal din yake kallo tun suna gida mai suna "Suits". Shi kallo ba damun shi yayi ba, idan Bilal ya saka wata rana sunayi tare, tunda ya fara sukan kalli wasu episodes din tare. Duk dai inda ya samu Bilal din na kallo shima dorawa yakeyi. Yanzun ma idanuwan shi ya natsa kan screen din laptop din suna kallon.

"Trevor din nan ba abokin Mike bane wai?"

Rayyan ya tambaya yana kurbar shayin shi, juyawa Bilal yayi saboda yana son tabbatar da cewa Rayyan din magana yayi bayan satikan daya dauka yana azumin yin maganar.

"Abokin shi din nan da suke daki daya"

Rayyan ya sake fadi ganin kamar Bilal bai gane tambayar shi ba, idanuwa Bilal ya runtsa yana bude su akan Rayyan. Baisan yana rike da wani numfashi ba sai yanzun daya sauke shi. Sosai abinda duk yake damun Rayyan din yake ci mishi zuciya. Yayi tambayar duniya Rayyan yayi banza ya kyale shi, har fushi yayi ya gaji ya sauka da kan shi. Yakan dauki kwanaki biyu batare da yace komai ba, amman bai taba daukar wannan kwanakin shiru haka ba.

"Dan Allah Hamma karka sake tsoratani haka... Ko ba zan iya taimaka maka ba, ko banda maganin damuwar ka idan ka fadamun zan saurara. Wasu lokuttan kana bukatar wanda zai saurari matsalarka ne saika sami saukin ta..."

Idanuwan Rayyan din na kan laptop har lokacin yana kuma shan shayin shi a nutse, yaji duk wani abu da Bilal ya fadi

"Shine, abokin shin nan ne"

Ya fadi maimakon amsa Bilal din, kai Bilal ya jinjina mishi, sanin in dai ba wannan hirar da Rayyan ya fara ba, sam ba zai saurari wata daban ba.

"Shine fa..."

Ya tabbatar ma Rayyan da ya girgiza kai

"Yasa bana son mutane, har kasan raina zan yafe komai banda cin amanar mutanen dana yadda dasu"

Dariya Bilal yayi

"To a duniya waye zaici amanar ka Hamma? Da wa ka yarda?"

Dan jim Rayyan yayi, akwai tarin abubuwa da mutane suke da su da bayaso sam shisa yake zabar kadaici akan tarayya da su

"Kuma idan wani yaji kana maganar mutane saiya dauka ba daga jinsi daya kuka fito..."

Kafadu Rayyan ya dan daga

"Kai..."

Ya furta yana sa Bilal kallon shi

"Na yarda da kai da Layla..."

Rayyan yayi maganar muryar shi can kasa yana dorawa da

"Sai Abbu da Ayya"

Duk yanda bayajin kusanci da su, yana jin ya yarda dasu, basu taba cutar da shi ba, basu taba mishi karya ba. Shisa ya yarda dasu, bayason karya da dukkan zuciyar shi, ba kuma ya son cin amana kamar yanda ya fadi. Yanzun bashi Trevor yaci amana ba, amman har ran shi yake jin abin, mu'amala da mutane babu komai a cikinta sai wahala.

"Mu din kenan ba za'a yafe mana ba?"

Bilal ya tambaya yana murmushi, kai Rayyan ya girgiza mishi, yana saka idanuwan shi a cikin na Bilal din

"Ba zai yafu bane..."

Yanayin da yayi maganar na saka wani abu tsirgawa Bilal din. Shirune ya ziyarci dakin suna maida hankalin su kan film din da suke kallo, wannan karin kowa da abinda yake tunani a cikin kan shi.

*

"Hamma..."

Layla ta fadi cike da farin ciki tana zagaya hannuwanta a bayan shi ta rike shi. Idanuwan shi Rayyan ya lumshe yana jin wani irin yanayi da ba zai misaltu ba, sosai a watanni shiddan sa suka wuce mishi a hankali yaso nisanta da Layla, amman ya kasa. Yana bukatar ta a kusa da shi in har zai sami natsuwar kammala jarabawar zangon. Satin farko da suka dawo makaranta ta zo wajen shi, inda ya saba zama. A gefe ta zauna batare da tace mishi komai ba. Sun kai mintina arba'in a zaune kawai. Shirune da yake cike da ma'anonin da basa bukatar kalamai. Shirune daya samar mishi da natsuwar da baiyi zato ba.

Da zata tafi, jakar shi ya bude ya zaro jacket yana mika mata, babu musu ta amsa ta saka a jikinta. Ita kanta ta samu natsuwa, da gangan a ranar ta saka doguwar rigar. Tana son ko yaya ne ta ga wani kusanci da yake a tsakanin su tunda baya mata magana. Haka taci gaba da zuwa su zauna shiru kawai, a ranakun da tasan yana azumi takan kai mishi abinci har gida. Sau biyu yana hanata zama, tana ajiye kwandon da ta jera kuloli Rayyan yake mikewa alamar su tafi. Shisa ta daina sallamar mai napep ko mashin din daya kawota, tana ajiyewa itama take tafiya ba saiya koreta ba.

Ranar da taji kamar zata mutu idan batayi magana da shi bane ta dauki waya ta kira shi, yana dagawa wani irin kukane ya kwace mata da yasa Rayyan din lumshe idanuwan shi, yanajin wani abu na budewa a zuciyar shi

"Layla..."

Ya kira da wani irin yanayi daya kara tunzura kukan da takeyi

"Ban san ya zanyi ba... Ban sani ba wallahi"

Ya fadi yana sauraren sautin kukanta da yake kara mishi hayaniya a cikin kan shi. Kamar katinta ne ya kare wayar ta yanke, kira ya kai biyar yayi bata dauka ba, yaso ya share, har kwanciya yayi, sai ya kasa. Idan kuka yake so tayi zai bata dalili, bayason wannan kukan nata. Mikewa ya tsinci kan shi dayi yana saka takalma, gani yake idan ya taka ba zai isa inda take da wuri ba shisa ya hau mashin. Sanda ya karasa bakin hostel din, ya mata kira yafi goma kafin ta daga tana fadin

"Hello..."

Muryarta na fitowa daga can kasan makoshi

"Layla..."

Rayyan ya furta yana lumshe idanuwan shi, abinda yake ji yaso yayi kokawa da shi ya kasa

"Ki fito... Ki fito in ganki"

Ya karasa hadi da sauke wayar daga kunnen shi. Sanda ta fito hula ce kawai a kanta, bai san ya zai kira abayar jikinta ba, ta dai mishi kyau saboda farar hular da ta saka. Baya son hada ido da ita bai gama karewa fuskarta kallo ba, ji yake kamar ya dade bai ganta ba, wata irin kewarta ke danne shi

"Hamma..."

Layla ta kira sunan shi daga kasan zuciyar ta, hannu Rayyan din ya mika mata, da sauri take takawa ta karasa tana kama hannun na shi, ta sa kafa ya hankade kashedin Mami da rokonta da yake shirin yi mata katanga da Rayyan din. Shi kam babu abinda yake ganewa, babu abinda yake gani a duk fadin wajen banda ita, babu abinda yake ji banda son hada jikin shi da nata, a hankali yake jan hannun nata da yake rike da shi harya hadata da kirjin shi inda yake jin kamar ya jima a cikin dokar daji, yanzun daya riketa ne ya iso gida.

Bai taba furtawa kan shi yanda ko ina bako bane a rayuwar shi banda wannan yanayin, har Bilal wani lokacin yakan ji kamar bakone a wajen shi, amman banda Layla, tun ranar farko daya fara hada idanuwa da ita suka firgita shi yasan ita din ba bakuwa bace a yar karamar duniyar shi da take cike da tarin hargitsi, ta jima a tare da shi, tun kafin ya santa kaddara ta hada hanyar su, tun kafin ya ganta yaga halitta mai kalar idanuwanta.

"Hamma"

Layla tayi maganar da alamar kuka da wani shauki a muryarta tana kara shigewa jikin shi. Ita kanta abinda take ji ba zai misaltu ba, kalar duk soyayyar da take gani daban take da wadda takewa Rayyan. A jikin shi kawai taji ta yanzun, amman launin duniyar gabaki daya ya sauya mata. Idanuwanta a lumshe take, bata taba ganin kyawun duhun da yakan baibaye kwayar idanuwanta bayan ta rufe shi ba sai yanzun, saboda a cikin duhu take yawo harta isa wani waje da ya haska mata Rayyan a tsaye, tana kallon shi da zuciyarta da take cike taf da soyayyar shi

"Shhh..."
Chapter 43 · 0% Book details