← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 93

Sashe 82

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai yaji dadin yanda duk watannin daya dauka ko Ayya bata ce mishi yaushe zaije gida ba. Suna waya kullum, yana kiranta sau hudu har fiye da haka a rana, ba hira sukeyi ba, dan yakan ce

"Zan sake duba kine daman"

Kamar yanda yakan ji Bilal yace mata wasu lokuttan, so yake ya rage mata kewar Bilal da yasan tanayi a lokaci daya kuma bayason ya fama mata ciwon da baisan koya fara warke mata ba. Tun biyan farko da akayi musu Bappa yace mishi anayin wani adashi, yayi bayanin amman badan Rayyan ya gane ba, shi din bamai yawan siye-siye bane ba, badan abinda yake turawa account din Bilal ba, kusan fiye da rabin kudin haka suke zama account din shi. Ko lokacin da suke makaranta sai kudin Bilal ya kare na shi akwai dan saura

"Duk yanda kake ciro dubu dai-dai ga kudin nan ya kare"

Ya kan fada idan yaji Bilal na maganar kudin shi sun kare shi

"Koyon ajiye kudi yana da amfani, ko badan ka siya wani abu ba, tsaron lalura ne. Idan baka saba ware wasu ka ajiye ba tun kana kai kadai, zai maka wahala idan ka fara tara iyali"

Bappa ya fada mishi, ya sha dauka yana abubuwan shi a tsare sai yanzun daya hadu da Bappa, sosai yana koyon abubuwa a wajen shi, watakila mu'amala da mutane bashi da aibun da yake tunani. Tunda yanayin Bappa din yanzun yana koyar da shi abubuwa da dama

"Ace shekaru kusan talatin amman kaga mutum baya tunanin abinda zaiyi da rayuwar shi, kudin duk da zasu shigo mishi ko bashi da abin siya saiya kirkira"

Lokutta da dama zantukan Bappa kan saka shi yayi murmushi, idan kaga yanda yake magana ko tsare-tsare sai kayi tunanin yanada yara fiye da goma da suke karkashin kulawar shi. Amman Bappa ya saka shi tunanin da gaske yana bukatar adana kudade, musamman da haka kawai Bappa din yace mishi

"Idan na koma karatu inajin idan ba nawa auren ba nakane zai dawo dani kasar nan"

Yana tuna mishi da cewa zai koma, duk da yanajin kamar babu nisan da zai yanke zumuncin da yake tsakanin su. A lokaci daya yana saka shi tunani akan abubuwa da yawa, tunani akan shi da Layla, baisan me take so ba a yanzun, amman shi ya kwana biyu da sanin abinda yake so. Da tunanin yake kwana yana tashi a satin, shisa ya yanke hukunci bin Bappa yau su tafi Kano tare, duk da baice komai ba yaga jin dadin hakan, tunda ya dade yana fama da shi da ko na rana daya ya bishi suje sai su dawo yana ki.

Ko bakomai ma yana son ganin Layla, kewarta yake ji har a kasusuwan jikin shi. Yaji dadin yanda Bappa ya sai da ya shiga ya gaishe da Ayya sannan ya wuce da nufin zai dawo da dare su fita da Rayyan din. Ayya ma taji dadin ganin shi, sai da yaje dakin su ya rage kayan jikin shi ya share dakin tas sannan ya shiga yayi wanka ya sake wasu kayan yana dawowa dakin Ayya. Anan ya zauna yaci abincin da ta zubo mishi, sai da ya gama ya dauke kwanonin ya kai kitchen sannan ya dawo ya zauna. Har yanzun bai saba magana da ita har haka ba.

Tauna abinda zai fada yakeyi, dagowa yayi yana kallon fuskarta

"Ayya ina so muyi magana ne daman"

Bata san me yake so ya fada ba, ta dai bashi dukkan hakalinta tun kafin yayi maganar

"Ina sauraren ka Rayyan"

Gyara zaman shi yayi

"Zan auri Layla, idan ta haihu zan aureta. Ina tara kudi Ayya, ban san ko zasu isa ba saboda gasu kama gida da su kayan lefe"

Bata san ya taji maganar ba, tunani dayane yake mata yawo kawai

"Babu wanda ya isa ya canza kaddara"

Ta kuma gani yanzun, duka kudadenta da ya kamata ace tayi wani abu muhimmi da shi ta kwashe ta baiwa Hajiya Dije da sunan a raba Layla da Rayyan, a raba harda Bilal da take gani a kusa da ita. Ga shi yanzun kaddarar da take zagaye da su ta hada su ukkun duka a gaban idanuwanta kuma da yake bata da iko a kai ba abinda zatayi

"Ayya..."

Rayyan ya kira saboda baisan me shirunta yake nufi ba, ya fara fada mata ne saboda yasan bata son Layla a kusa da shi, bata kuma son Mami, gara taji daga wajen shi. Rayuwar shi duka yayi ta ne cikin rashin daukar duk wani abu da zatace da muhimmanci, shisa yanzun zai fara, ya rigada ya yanke hukunci auren Layla, amman baya nufin zaiyi shi bada yardarta ba.

"Kiyi mun magana Ayya, ni din ban saba jin maganar ki ba, ina so in aureta, idan hakan na nufin in jira sai kin amince zan jira in dai bata da matsala da hakan itama, amman kice wani abu dan Allah"

Haka kawai taji zantukan shi sun karya mata zuciya. Kai ta jinjina kawai, muryarta na rawa tace

"Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kaimu lokacin"

Numfashin da baisan yana rike da shi ba ya saki. Ya dan kara jimawa batare da sun cewa juna komai ba sannan ya mike ya fice, sai da yayo sallar azahar ya dawo sannan ya shiga bangaren Mami, itama suna gaisawa kan shi a kasa yace

"Layla fa? Ina so inyi magana da ita Mami"

Dan jim Mami tayi kafin ta mike, dakin Layla ta nufa tana Kwankwasawa kafin ta tura, tana zaune a kasa da alamar sallah tayi itama, dan ko hijabi bata cire ba

"Ga Rayyan a falo yana so yayi magana dake"

Mami ta fadi tana juyawa batare da ta jira amsar Layla din ba, dakinta ta koma. Zuciyar Layla har cikin tafukan hannayenta take jin su. Ta ga kiran shi amman bata daga ba, saboda yace mata zaizo bata bashi amsa ba, tunda safe da taga sakon shi take kuka. Yanzun ma idanuwan ta taji cike taf da hawaye, watakila idan yaga bata fita ba ya hakura ya kyaleta, batajin zata iya bari ya ganta a yanda take din nan. Cikinta ya fito sosai tunda ya shiga cikin wata na biyar, har awo na farko tayi, yanzun takan ji motsin abinda yake ciki, har bacci yakan tasheta idan yayi wannan kwakkwaran motsin.

Text taji a wayarta, ta mika hannu tana daukowa ta duba, Rayyan ne

"Ba zakici gaba da shareni ba, ba zan barki kici gaba da shareni ba. Idan baki fito ba zan shigo"

Hawayen da suka zubo mata ta share tana dafa gadon ta mike da dakyar. Cikin yasa tana kallon Mami da wata daraja ta daban yanzun. Ko juyi zatayi a bacci saita tashi zaune idanuwanta tar sannan take juya, ga wani irin ciwon jiki da take fama da shi naban mamaki. A kasan zuciyarta haka kawai take jin kamar kafarta daya a duniya take daya kuma a wani waje da bata da sunan da zata bashi har yanzun. Tana tallafe da cikinta ta fito daga dakinta, bata ga fuskar Rayyan ba, bayan kan shi kawai tagani, amman ya isa ya karyata mata duk wani tunani da tayi na binne mafarkin samun shi.

Saboda wata irin soyayyar shi ce ta taso mata tana saka har abinda yake cikinta yayi wani irin motsi daya sakata kiran sunan Allah cikin yanayin da ya saka Rayyan juyawa ya sauke idanuwan shi cikin na Layla da ta bude. Sai taji ta daburce, juyawa take shirin yi ta ruga, wani waje take son kasancewa da baya nan

"Layla... Dan Allah... Karki boye mun"

Rayyan din ya fadi cike da wani irin tsoro a muryar shi da yayi mata tasiri. Ganin ta tsaya tana juyowa yasa shi mikewa ya zagaya zuwa inda take yana fuskantarta. Jikin shi bari yakeyi daga ciki, hatta da zuciyar shi rawa takeyi mishi. Baice yanayinta bai taba shi ba, bai kuma yi kokarin boye hakan dan karta gani ba. A duk rana tun bayan daya sani da cikin jikinta yake kwana yana tashi. Amman hakan baisa yaji saukin ganinta dauke da shi ba, ganin shi ya fito sosai haka.

"Hamma"

Layla ta kira da wani yanayi a muryarta, tana saka har dayan hannunta ta kare cikinta kamar tana son boye shi saboda irin kallon da Rayyan din yake mata

"Kaima ka daina ganina ko? Ka daina ganina sai cikin da yake jikina"

Ta karasa maganar tana jin wani daci a zuciyarta da hawayen da suka zubo mata. Kai Rayyan yake girgiza mata, amman ya kasa hada idanuwa da ita har lokacin, cikin kuka tace

"Na sani, kowa baya gani sai cikin nan, kamar ba a jikina yake ba haka nakeji, ina jin kamar tare da cikin ni na bace, shisa kowa baya gani na"

Sai lokacin ya iya kallon idanuwanta da suke cike taf da hawaye yana furzar da numfashi ta bakin shi, bayajin akwai wasu kalamai na lallashi da zai fada mata

"Ina ganin ki, ina ganin ku duka ba zan miki karya ba. Amman ina ganin ki"

Cewar Rayyan yana dorawa da

"Na san na fadi abubuwa da yawa. Zan sake fadin wani yanzun. Zan aure ki, ba dan abinda ya faru ba, dan ina son ki, zan aure ki in har yanzun kina jin zaki iya rayuwa da ni"

Sai da ta dafa kujerar da take gefenta sannan ta iya tsugunnawa saboda yanda kalaman shi suka daketa. Numfashi take fitarwa wani irin kuka na kwace mata. Tsugunnawa yayi shima, idan zai fada mata sau dari ba zai gaji ba, saboda bayason wannan kadaicin da yake gani a cikin idanuwanta, bayason yanda take jin kamar ita kadai ta rage a duniyarta, kamar babu wanda zai taba fahimtar halin da take ciki, wannan yanayin shi yake kaika fadawa depression, abinda zaiyi komai da yake karkashin ikon shi na ganin bai bari Layla ta dandana wannan duhun ba.

"Na fadama Ayya, ta mana fatan alkhairi. Bake kadai bace ba, ba zan fahimta ba nasani. Amman ina tare dake, koma menene ni da ke muna tare"
Chapter 82 · 0% Book details