Sashe 7
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tambaya, so yake ya bude bakin shi ya gaya mata rasuwar dan uwan da yasan duk a cikin gidan su tafi shakuwa da shi, tsiran su ba wani mai yawa bane ba, duka shekaru biyu ya bata, kuma shi kadai ne take ji har kasan ranta duk a cikin yaran matar Baban nata da taki jinin ta bude idanuwanta tagani. Amman kowa yasan Maimuna yasan Audu, ko kasuwa yaje tsarabarta daban take da ta sauran mutanen gidan. Badume daya koma da zama bayan auren shi bai yanke zumuncin da yake tsakanin su ba, duk juma'ar duniya yana shigowa, kuma kowa yasan dan ita kadai yakanyi hakan, har gida yake zuwa ya dubata ya kai mata yan tsarabun da ya siyo.
Kusancin su mai girmane, shisa aka rasa mai zuwa ya fada mata gobarar da ta afka musu tun a daren jiya, gobarar da tai sanadin rayuwar Audu, matar shi da yaran shi biyu, cikin ikon Allah tana barin Bilal, jaririn da satin shi uku da haihuwa. Lamarin da ya girgiza kauyen Badume da kewayenta, domin Audu mutum ne mai karamci da sanin ya kamata, tun zaman shi babu wanda zaice ga ranar da yaga fuskar shi ba dauke da murmushi ba. Mutum ne da yake samun shaidar arziki ko da baya waje. Ahmadi aka samu har wajen aiki, suna ganin kamar zai fi mata sauki idan taji daga bakin shi, shikuma yana juyayin yanda ba zata taba manta a bakin shi taji wannan lamarin ba.
Da bakin shi ya fada mata zancen auren shi da Maryama, zancen da ya birkita mishi Maimunar shi ta yanda har yanzun bata dawo dai-dai ba, shi din mutum ne mai rauni, sam ba zai iya fada mata wannan zancen ba. Asalima yana ganinta yaji idanuwan shi sun ciko da kwalla, kwallar rashin Audu da ba ita kadai zataji shi ba, kwallar tausayin matar tashi da halin da yasan zata shiga. Bai iya komai ba sai hade dan sauran tazarar dake tsakanin su yana rikota jikin shi, zuwa lokacin harta fara kuka tun kafin ma tasan meya faru, jikinta ya gama bata koma menene ya faru ba abu bane me kyau.
Ko ina jikinta bari yakeyi
"Me ya faru? Ahmadi waya rasu? Ko Baba ne?"
Take tambaya tana dagowa daga jikin shi, kai ya girgiza mata yana kokarin danne kwallar dake son zubo mishi. Dakyar ya iya cewa
"Ki dauko mayafin ki..."
Batayi musu ba, dan ko ina jikinta bari yake, mayafin ta dauko tana rike dashi a hannunta ta fice daga dakin, tama manta da Rayyan da yake kwance a cikin dakin, takalman ma, daya nata, dayan na Ahmadi daya cire a bakin kofar ta saka. Saida ya fito daga dakin ya kalleta cike da tausayawa, nata takalmin ya tsugunna ya dauka yana tura mata, kula tayi ta zare nashi, ta saka nata. Sannan ya dago yana saka takalman a kafar shi. Maryama da ta fito goye da Haris ya kalla, da idanuwan shi yai mata nuni da bangaren Maimunar, ganin har tayi hanyar waje
"Rayyan yana bacci..."
Ya furta a hankali, itama da alama hankalinta a tashe yake
"Me yake faruwa?"
Dan lekawa yayi bai hango alamar Maimuna ba, hakan yasa shi fadin
"Audune Allah yayi mishi rasuwa, sunyi gobara jiya da dare, kamar da iyalin duka..."
Yanda Maryama ta dafe kirji tana sakin wani salati daya fito da kuka yasa Ahmadi wucewa yabi bayan Maimuna, ta yanki hanya kuwa sai sauri takeyi. Kunya ya cire ya ajiye gefe yana karasawa da sauri ya kama hannunta ya rike. Ko da suka isa gidan ma bai saketa ba saida ya karasa da ita har cikin gidan. Inda ta samu tashin hankalin da bata taba tsammani ba, tayi suma ranar yakai hudu tana farfadowa ana gaya mata labari kala daya. Tun da dare data samu natsuwar da zata iya mikewa taje ta karbi Bilal da sai kuka yake a hannun Yayar Audu din wato Talatu.
"Da kin barshi kin ji da kanki kawai Maimuna, ko tsayuwar kirki bakya iyawa..."
Talatu ta karasa cikin kuka. Wata mata da Maimuna ba zatace kowacce ba a lokacin ta karbe zancen da fadin
"Shima yaron zafin maraici ne yake taba shi, duk wanda suke shayarwa an gwada bashi mama fur yaki karba..."
Hannu kawai Maimuna ta saka tana daukar Bilal batare da tace musu komai ba ta fice daga dakin. Waje ta samu a tsakar gidan tana zama da yaron a hannunta, tanajin kamar duk duniya shi kadai ne alakar data rage mata a tsakaninta da Audu, kamar babu jinin shi a jikinta, kallon Bilal take, kaunar yaron na ratsa duk wani sassa na jikinta, tana tuna yanda ko ranar suna shi satika uku da suka wuce harda ita ake tsokanar Audu da yaran sak shiya biyo, duk ya kwace ma Jummai matar shi kamanni da yaran nasu, kunya irin ta Audu murmushi kawai yayi ya fice daga gidan.
Da tasan duk bankwana sukeyi da ta bishi sun dan zanta, da ta bishi ko yan mintina ta kara samu a tare da shi. Amman ina, ko ganin karshe da tayi mishi juma'ar data gabata basu wani dade ba, ruwa kawai yasha
"Nayi yamma Maimuna, idan Allah ya bamu aron rayuwa a gidanki zanci abincin rana juma'a mai zuwa"
Ta tuna kalaman shi, da suka saka hawaye masu zafi zubo mata. Tana kara rike Bilal a jikinta, wani irin zazzabine ya rufeta da tasan kaduwa da firgicine suka saukar mata da shi. Ance an gwada bashi mama yaki karba, ita kam gwadawa tayi yanzun, kamar Bilal yasan kalar kusancin da yake tsakanin ta da Audu ya kuwa karba, kafin wani lokaci yayi luf a jikinta. Aikam hakan ba karamin kara rikita kowa yayi a gidan ba, haka akaita koke-koke ana zantukan zumuncin da yake tsakanin Maimuna da Margayin. Ba ayi bakwai ba kuwa sai da ya zamana babu mai gwada karbar Bilal daga hannun Maimuna, masu tunanin cewa ma zasu rike shi basu furta zancen ba, dan ta nuna abune da ba zai yiwu ba.
Rayyan ma da Maryama ta biyota dashi, kamar yasan wani abu mai girma ya faru, baiko gwada zai sha Mama ba, larabar tazo musu da sauyi mai girma gabaki dayan su. Tayi rashi babba, ta kuma karbi amanar da take tunanin babu wanda ya cancanci a yarda da yai rikonta sai ita, ta karbi Bilal da Ahmadi ya nuna goyon bayan shi dari bisa dari a kai. Ko bai auri Maimuna ba, shi din mai rike jinin Audu ne, akwai wannan kusancin a tsakanin su. Shisa har yanzun da take rike da Bilal, rashin Audu yake kara tabata
"In shaa Allah in dai ina numfashi ba za kai maraici ba....babu wanda zai kalleka ya kiraka maraya"
Ta furta a fili tana share kwalla, sosai take kallon yaron, yanda duk akance tana kama da Audu, yanda har ranar sunan Bilal da ake ma Audu tsiya aka dawo kanta bayan fitar shi cewa ai itama Bilal din kamanninta ne, yau sak Audu take gani a fuskar yaron, dogon hancin nan nashi, idanuwan shi da kowa kan tanka har akayi zaton baki zai kama su, komai na Audu take gani a tattare da Bilal. Rayyan da yake baccine ya farka ya rarrafo yana karasowa inda take zaune. Hakan yasa ta share kwallar da ta zubo mata.
Hannun shi Rayyan ya mika ya kama na Bilal din
"Kaga kanin da ka samu ko Rayyan?"
Maimuna ta fadi, tana kallon yanda kamar Bilal ne yaji maganar da tayi ba Rayyan ba, dan shi ya sa dan karamin hannun shi yana rike yatsan Rayyan din, haka kawai yanayin yasa zuciyar Maimuna wani irin dokawa da karfi, a lokaci daya kaddara na budewa yaran shafin da a dogon tunanin Maimuna bata hango musu ba.
1991 Kano.
"Rayyan..."
Maimuna da duka yaran suke kira Ayya ta kira tana sakawa Shamsu riga a jikin shi.
"Rayyan..."
Ta sake kira, saboda taga giccin shi, shirin makaranta takeyi musu. Suzo su dauki safa kafin Ahmadi ya shigo ya samu basu shirya ba ya dora laifin a kanta. Dan akan makarantar yaran daga boko har islamiyya bayason wasa sam. Wani lokacin idan tayi mitar fadan daya koya sai yace zama da itane, ita ta koya mishi fada.
"Wallahi Rayyan na fito sai na dake ka"
Ayya tai maganar ranta a bace, tana balle maballin rigar da take jikin Shamsu
"Ayya kina kiran Rayyan ne? Yana wajen Abbu"
Bilal ya fadi, dago kai Ayya tayi
"Kai ne ka wuce daman?"
Kai ya jinjina mata yana saka murmushi kwace mata. Shekaru biyar kenan, a cikin shekarun tana da abubuwa da yawa da zatayi godiya domin su, ciki harda karin yara biyu da Allah ya bata, Rukayya sai Shamsu da take goyo yanzun. Duk yanda a fakaice bayan shekaru biyu da shigowar Bilal rayuwarta ta samu cikin Rukayya, Ahmadi nata kokarin tunatar da ita kan yanda yake fada mata komai na Allah ne, duk ta daga hankalinta akan rashin haihuwa, yanzun gashi nan komai da lokaci yayi Allah ya bata.
"Hmm..."
Kawai ta iya furtawa, ita kadai tasan wahalar da tasha kafin ta samu cikin Rukayya, duk kalar tsoronta saida Khadi ta rakata wajen Malam Mainasara, kuma zata gode Allah da ya bata wannan damar
"Bakin aljani ne aka saka ya shafar miki mahaifa. Aikine akayi babba gaskiya"
Rubutu ya bata na kwana uku, daya a barbada gishiri, daya a barbada sikari, dayan a saka lemon tsami. Sai wani tsinke kwakwa daya karya wajen gida takwas yana samun leda ya daure a ciki, yace idan ta dawo da tsinken za'a gwada aga idan rubutun yayi aiki ko akasin hakan. Zatayi karya idan tace bata dawo da shakku a zuciyarta ba, saboda maganar shi na cewa har yaranta Maryama take son cutarwa. Amman a tsayin shekarun nan ta yarda Maryama zatayi komai dan ta cutar da ita, dan yanzun takan biye mata idan ta takaleta, da wahala ta fadama Maryaman magana daya bata rama ba.