← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 93

Sashe 51

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayafi kawai Layla ta cire, ko towel bata dauka ba ta fice daga dakin. Da yake sukan dibo ruwa da bokatan wankan nasu, da sun fito bandaki sukan saka omo su wanke shi har bayan. Shisa tasan ruwan ciki mai tsarkine, karkatawa tayi ta fara wanke hannayenta, a karo na farko da takejin sauqi irin na addinin musulunci, niyyarka a zuciya idan ka daurata tayi, ba saika fadeta a fili ba, bata da kwarin gwiwar motsa labbanta da daura niyyar wannan wankan da take tunanin ya zame mata dole. Tashin hankalinta bai fara ba sai da ta wanke fuskarta tana sake bude idanuwanta a cikin bandakin.

A daddafe ta karasa wankan, kayanta ta mayar tana fitowa, can ta baro bokitin, sai Anisa ce ta koma ta dauko, doguwar riga ta dauka ta sake kayan jikinta da take da tabbacin ta gama saka su har abada. Wayarta ta bude jaka tana dauka, tana kallon yanda hannunta yake bari, a kasa ta zauna. Tambayoyin Bilal ne suke dawo mata, amman yanda ta kula ya kasa gane yanda akayi abinda ya faru ya faru, haka itama take cikin wannan rudanin. Ta san sanda ta shiga dakin su, ta tuna sanda ta zauna harta sha ruwa, amman daga nan babu abinda zata iya tunawa banda tashin hankali da wani irin firgici marar misaltuwa.

Dakyar ta iya lalubo lambar Bilal tana kiran shi, bugu biyu ya daga

"Hamma ba mafarki bane ba, ba mafarki bane Hamma..."

Ta furta da wata irin nisantacciyar murya, girman kalaman na zauna mata da wani yanayi daya birkita mata komai, wayar ta sauke daga kunnenta tana ajiyewa a gefe, kafin ta janyo kafafuwanta ta hade su da jikinta. Har lokacin jinta takeyi kamar bata da kaya

"Martabar ki darajar ki Layla, martabar ki sutturar ki..."

Kalaman Mami suka dawo mata. Kalaman na tuna mata da Mami

"Mami... Mami"

Ta ke kira cikin wani irin tashin hankali, duk wata nasiha da ta tabayi mata tana dawo mata. Da gaske martabarta suttura ce a wajenta, sutturar da bata gane muhimmanci ta ba sai yanzun da take jin bata tare da ita. Kuka take nema amman sam yaki zuwa, banda wani irin numfashi da take ja tana fitarwa kamar mai ciwon asma babu abinda take iyayi, batsan shigowar Anisa dakin ba sai da taji ta kamota

"Dan Allah kiyi mun magana Layla"

Cewar Anisa da hawaye cike taf a idanuwanta, dan ita bata son tashin hankali sam, sai lokacin wani irin kuka ya fito tun daga kasan zuciyarta tana sakin shi cikin shesheka, ko ina na jikinta bari yakeyi

"Kiyi hakuri, banma san me ya sameki ba, ko me ya faru, dan Allah kiyi hakuri..."

Anisa tace tana kara rike Layla a jikinta, yanayin yanda take kuka ne yake ba Anisa tsoro, saboda bata taba ganinta cikin yanayi irin wannan ba, wayarta da ta fara ringing Anisa ta dauka tana dubawa, an rubuta

"Mami ❤"

A jiki, gyarama Layla kwanciya tayi a jikinta

"Dan Allah kiyi shiru, kinga ga Mami tana kiran ki"

Wata irin mikewa Layla tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi, fisge wayar tayi daga hannun Anisa, tana kifeta akan cinyarta, kamar hakan zai hanata rurin da takeyi, jikinta kara bari yakeyi cike da sabon tashin hankali, ji takeyi kamar Mami ta gane, kamar tasan me ya faru shisa take kiranta, tana yankewa wani kiran na sake shigowa, amman ta kasa dubawa, sau biyar ana kira tana yankewa, kukanta ke kara tsananta saboda tashin hankalin da take ciki, saboda tasan duniyarta ce gabaki daya tazo karshe shisa Mami ta gane, shisa take kiranta. Bata da abinda zata fada mata

"Fyade"

Shine kalmar farko da ta dace a yanayi irin wannan, ita kuma ce kalma guda daya da zata iya labewa bayanta dan samun sauki. Amman zuwan kalmar tunanin ta, alakanta Bilal da wannan kalmar kawai barazana take karawa shige da ficen iskarta. Ko kwaya Bilal yasha ba zai taba mata fyade ba ita tasani, ita zata bada shaidar waye Bilal. Shisa bata da kalmar da zata fassara abinda ya faru din, bata da shi, da duk dakika da yanda rudani da tashin hankalinta suke karuwa. Wanne irin mugun abune wannan yake faruwa dasu? Kamar wanda akayiwa asiri, asiri ne kawai abu daya da take da shi da zai fassara mata abin nan ta yarda, sai kuma iskokai, amman a iya saninta bata da iska, haka ma Bilal.

Sai dai akwai iskar da bata bayyana sai daga baya, watakila abinda ya faru da su kenan. Amman wa zatayiwa wannan bayanin ya gane?

"Ke yanzun kina tunanin shi Rayyan din da kike biyewa idan tsautsayi ya gifta a tsakanin ku zai aure ki?"

Kalaman Mami suka dawo mata, suna kuma tuna mata da Rayyan daya fice daga kanta na wucin gadi

"Na shiga uku, Anisa na shiga uku na"

Ta ce cikin firgici

"Ki daina Layla, babu kyau fadar haka, ki daina dan Allah. Kiyi addu'a koma menene zai zo da sauki"

Kai Layla take girgiza mata wasu irin hawaye masu dumi na zubo mata, jiya ta ga yanayin da bata taba gani ba a cikin idanuwan Rayyan, a karo na farko jiya yayi mata kalar murmushin da bata taba gani ba, zata rantse daga zuciyar shi yayi mata murmushin bayan ta fada mishi tana son shi, kamar yana son gaya mata ita da shi din zasu iya faru, a cikin murmushin shi ta ga possibility din zaman su a karkashin inuwa daya a matsayin masoya da zai iya kaisu da aure wata rana, ta hangi cikar burinta a kwayar idanuwan shi. Da yace ta tafi sai taga kamar akwai rokon da yake mata, kamar yana bata amanar kanta ne kafin ya dawo.

"Bana son kowa a kusa da ke Layla"

Ya sha fada mata, a wasu lokuttan takan gane zai fadi kalaman tun kafin ya furta su. Da wanne ido zata kalle shi? Ya zatayi mishi bayani ya gane? Zai fahimceta? Zai fahimce su ita da Bilal idan sukayi mishi rantsuwa da su kan su har yanzun basu san ya akayi abinda ya faru din ya faru ba. Wayarta da ta sake daukar ruri ta katse mata tunanin da takeyi, wannan karin da wani irin bugun zuciya tasa hannu ta birkita wayar tana ganin

"Hamma Na"

A rubuce, bakinta da matuqar nauyi ta iya furta

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Wani irin yanayi take ji da batasan ya zata fassara shi ba, ashe haka tashin hankali yake bata sani ba? Ashe haka asalin firgici yake, ko ranar da ta fita bandaki cikin dare taga gicci tayi tunanin aljani ne bata firgita irin wannan da take ciki yanzun ba. Tashin hankaline da babu wanda zai taba fahimtarta sai wanda ya taba shiga cikin irin yanayin da take yanzun. Wayarta da ke ruri ta ga Anisa ta mika hannu ta dauka, da sauri ta rike hannunta

"Ba dagawa zanyi ba, zan saka a silent ne"

Tayi maganar cikin wani irin yanayi, a silent din ta saka mata wayar tana mikewa ta ajiyeta gefe. Fita tayi daga dakin, ruwan sanyi ta siyo ta dawo. Guda daya ta dauka ta tsiyaye a kofi ta zo tana ba Layla din da ta girgiza mata kai

"Ki sha dan Allah, watakila kidan ji dama-dama"

Hannu biyu ta saka ta karbi kofin saboda yanda jikinta yake bari, shan ruwan tayi sosai, Anisa ta karbi kofin tana ajiyewa a gefe. Mikewa tayi ta fita ta daura alwalar la'asar tana tunawa Layla yanda itama batayi sallar ba. Dakyar ta iya mikewa tana dauro alwala, a karo na farko ta tsinci kanta da kunyar tsayawa a gaban Ubangiji, sai take jin kamar ita din bata cancanci tsayawar ba, kamar tana da tarin laifukan da batasan yanda zata fassarasu ba, har Anisa ta idar ita tana ta rakubewa a gefen gado

"Kinsan la'asar da saurin wucewa, ki samu kiyi sallah sai ki sha panadol ki dan kwanta. Sannu"

Kai ta jinjina, ko da ta gabatar da azahar ta sake mikewa ta gabatar da la'asar ta idar Anisa batace mata komai ba. Hannuwanta ta daga tana rasa abinda ya kamata ta roka, gabaki daya addu'o'inta basayin tsayi ko da can, idan tayiwa iyayenta da suka rasu, sai Mami da Abbu, sauran ta fatan samun Rayyan ce, sai kuma Bilal, shima bata taba mantawa da shi a cikin addu'o'inta, in tayi tama sauran yan uwanta shikenan. Lokutta da dama sai tayi niyyar mikewa sai taji kamar bata kyauta ba, kamar saboda Rayyan da Bilal ya kamata tayiwa Ayya itama, a ranakun da abin yake ci mata rai, takan koma tace

"Allah ya raya miki duka yaranki cikin aminci Ayya, Allah ya yafe miki, nima na yafe miki duk ce mun mayya da kikayi"

Wasu ranakun kuma turo labba takeyi ta mike abinta, yanda Ayya bata sonta, itama hakan take ji. Amman yau ta rasa abinda zata roka, a karo na farko ta rasa. Tana tsakanin rokon sauki, ko kasancewar abin da yake faruwa mafarkin da tasan ba haka bane ba.

"Mami.. Mamina... Allah ka dauke duka saukin a kaina ka bata....Allah Mami...Mamina"

Shi take fada hawaye masu zafin gaske na zubar mata. Nan take zaune kan dardumar, tun tana iya fadar kalamai har suka bace mata, banda Mami da take kira tana wani irin kuka babu abinda take iyawa. Anan Magriba ta sameta ta tashi tayi, isha'i ma haka. Duk yanda Anisa taso ko ruwan shayine ta kurba kiyawa tayi. Zuwa goman dare sanda ta kwanta zazzabi ya rufeta kuwa. Tun Anisa na mata sannu, har ta daina amsawa, tana jinta ta tabata, tayi luf dan Anisa ta samu bacci, sannan kuwa ta hau sama tana kwanciya. Bude idanuwanta takeyi, dan duk idan ta rufe bata ganin komai sai ita da Bila a abinda take tunanin mafarki ne, tambayoyin da take da su idan ta fito dasu fili zai iya barazana da imaninta, shisa ta zabi taci gaba da fadin

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ko zata samin saukin da kalmomin sukan samar a yayin tashin hankali.

*
Chapter 51 · 0% Book details