← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 93

Sashe 78

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Balle kuma yanzun ta kula da Rayyan din ya samu lafiya. Saboda kalar kusancin da yake tsakanin su a yan kwanakin nan, ba zata kara jefa shi cikin hargitsi ba. Zata fara da dai-dai ta tsakanin ta da Ubangijin ta da farko, sauran zasu fi zuwar mata da sauki, zata roki Allah da ya saka sauran lamurran zuwa mata cikin sauki. Tana nan zaune a daki taji an kwankwasa, sai da ta share hawayenta sannan ta amsa, ta dauka ma Rukayya ce, sai taga Rayyan ne, yanda ya fara sauko rabin fuskar shi yana sakata runtsa idanuwan ta kafin ta sake bude su akan shi, dan yayi mata kamar Bilal, manya kayane a jikin shi farare kal sai hula ruwan omo mai cizawa.

"Ayya yanzun zan wuce, Bappa ya karaso"

Numfashi ta sauke tana kallon shi

"Har kana da natsuwar komawa?"

Tayi tambayar a sanyaye, kafadu Rayyan ya dan daga mata. Idan ma bashi da natsuwar komawa ba zai zauna ya jirata ba. Tunda bashi da tabbacin ranar zuwanta ko zata zo din. Komawar shi yafi mishi, ko bakomai zai samu abin yi banda zama cikin dakin su yana duba hanya kamar zai ga shigowar Bilal kowanne lokaci.

"Zai ragemun tunani, idan na koma din"

Kai ta jinjina mishi, wani irin yanayi take ji a zuciyarta da ba zai misaltu ba

"Kayi wa Abbun ka sallama?"

A hankali ya girgiza mata kai, ya shiga dakin Abbun ya samu harya fita. Yana yawan shiga yanzun, saboda yana rage mishi zafin da yake ji a zuciyar shi, ba wai suna hira bane ba. Yanzun ya san rashin son surutu halin shine, kawai yanajin dadin yanda yake iya zama waje daya da Abbu din batare da yaji iskar dakin tayi mishi kadan ba. Idan labarai Abbu yake kallo zasu kalla tare, har sai ya gaji da zaman sannan yake tashi yayiwa Abbu sallama ya koma nasu dakin. Jiyama a dakin Abbu suka ci abincin dare tare, abinda bai tabayi ba a iya yanda zai iya tunawa.

Yaji dadin abin saboda shine abu na farko da ya saka a cikin shi duk tsayin jiya. Yana daki yana kukan da ya kasa tsayawarwa sai da ya tsaya da kan shi. Ya fadama Abbu cewa yau zai tafi, amman basuyi sallama ba yau din

"Ya tafi sanda na shiga. Zan kira shi a waya..."

Ya furta a hankali yana juyawa

"Allah ya tsare ya bada sa'a. Ka kula da kanka"

Hannun kofar da yake rike da ita ya murza sosai, addu'ar Ayya na nutsar da wani abu cikin kan shi, sai da ya hadiye yawi sannan ya amsa da

"Amin thumma amin"

Harya bude kofar yana shirin fita ta kira sunan shi, dan juyawa yayi

"Idan na kiraka ka daga Rayyan"

Kai ya jinjina mata yana ficewa, duk da wani abu a tare da shi na fada mishi ya bata hakuri, da duk lokuttan da ta kira shi yana kallo bai daga ba, ba laifin shi bane ba, a lokacin yanajin magana da ita takura ne, shisa yakan zabi yaki dagawa. Amman abinda yake saka shi kuka yanzun ya kula bashi da wahala. Shisa ya zabi yin shiru, hakurin da zai bata zaiyi shi ta hanyar kiran wayarta kafin ita ta kira shi. Da wannan tunanin ya fice daga dakin, yana nufar dakin Mami da ya dade a tsaye bakin kofa yana tunanin shiga.

Wani numfashi yaja mai nauyi yana fitarwa kafin ya shiga dakin da sallama yana cire takalman shi daga bakin kofa ganin Mami zaune a falon, amsawa tayi tana dorawa da

"Rayyan..."

Bata hadu da shi ba tun ranar rasuwar Bilal, bata ma fita ba saboda dalilai kala-kala, daya daga cikin babban kunya da nauyin Rayyan din kan yanda ta yanke mishi hukunci batare da ta tsaya taji bakin shi ba. Ga shi duniyar duka bata mata dadi a kwanakin, bata da lafiya amman ba zatace ga guri daya da yake mata ciwo ba. A cikin zaman makokin Bilal bata da natsuwar kirki, mutuwar bata daketa ba sai bayan an watse sadakar ukku, saboda zuciyarta bata da natsuwa kar Layla ta gifta cikin danginsu wani ya kula da cikin da take dauke da shi. Nasihar duk da Abbu yayi mata ta kasa natsuwa.

Batajin akwai wanda zai taba gane halin da take ciki. Ita kadai tasan abinda take ji. Shisa Layla din ma ta kasa samu ta zauna suyi wata magana. Tana hango yanda ba rayuwar yarinyar bace kawai ta canza harda tata. Da ace tana da mahaifa ko daya da suka rage da taji sauki, zataje wajen su ko kuka tayi su fada mata magana mai sanyi, su karfafa mata gwiwar daukar kaddarar da ta sameta. Amman babu, maraicinta bai taba tsaya mata irin na yanzun ba, saboda Ahmadi na bata dukkan kulawa. Bata da bakin da zata amsa tambayoyin mutane, kunnuwanta da zuciyarta basu da karfin jure ma maganganun su.

"Mami"

Rayyan ya kira cikin sigar gaisuwa yana karasawa cikin dakin sosai. Kallon mamaki take bin shi da shi, sai take ganin kamar akwai abinda ya canza a tare da shi da bashida alaka da mutuwar Bilal. Kujera ya samu ya zauna yana sauke numfashi a hankali, jin shirun yayi yawa yasa Mami fadin

"Abinda ya faru... Kayi hakuri, na yanke maka hukunci da sauri"

Murmushi mai ciwo Rayyan yayi

"Baya nufin bani da laifi, ina da laifi mai yawa Mami... Kiyi hakuri"

Idanuwanta taji sun cika da hawaye, shi baizo dan wani abu ba sai dan Layla. Ba Ayya bace kawai tayi tunani akan cikin da yake jikin Layla, har shi dinma, Bilal bai bar mishi wani abu da zai dinga tunawa da shi ba, ko da hotone yana bukata, suna da hotuna da yawa tare da Bilal, dan shi din baya gajiya da daga camera din wayar shi. Wani lokacin ma yana harar shi haka zai dauke su yana dariya, da zai samu duka wannan hotunan da yaji dadi, ko su zai dinga dubawa, yana bukatar wani abu banda kayan sakawa na Bilal. Cikin da yake jikin Layla ne abu mai girma na Bilal da zai dinga dubawa.

A daren jiya bayan rokarwa Bilal gafara da kuma Rahmar Allah harda cikin jikin Layla ya hada. Sosai yake jin son kan da yayi a cikin hakan, saboda yaga Layla, yaga yanda ta koma. Ba karamin kalubale yake hangoma rayuwarta a tare da cikin ba. Amman babu yanda zaiyi, bai isa ya hana zuciyar shi son ganin abinda zata haifo ba. Jinin Bilal ne, yaro ko yarinyar Bilal ce, yana son gani, shine kwai kwara daya na Bilal. Duk da zuciyar shi ta kasa hasko mishi Bilal din da Layla, cikin ya manne a wani waje cikin zuciyar shi, shisa yazo ya bama Mami hakuri, baice ita dole sai taso cikin ba, amman karta tsangwama wa Layla, tana cikin wani hali da alama.

"Dan Allah kiyi hakuri Mami, bansan ya kike ji ba. Amman naga Layla... Duka abin ya fara tabata kafin mu ya taba mu, kiyi mata fada, ki zageta idan hakan zaisa ki samu sauki, amman dan Allah kiyi hakuri, ki yafe mata. Ki yafe ma Bilal, nima ki yafe mun... Duka mu din masu laifi ne"

Hawayen da take rikewa ne suka zubo mata, tunda take bata taba jin Rayyan yayi magana mai tsayin wadda yayi ba yanzun. Ba kalaman shi bane suka sakata kuka, yanayin yanda yayi maganar ne, sai da ta goge hawayen sannan ta iya amsa shi da

"Allah ya yafe mana gabaki daya"

Mikewa Rayyan yayi, ganin yanda take ta share hawaye shisa bai iya sake cewa komai ba ya fice daga dakin. Ya so ya ga Layla, amman bai da karfin zuciyar cewa Mami tayi mata magana. Zai kirata a waye idan ya tashi. Yana fita daga dakin mikewa Mami tayi tana share wasu sababbin hawayen da suke zubo mata. Sannan ta iya nufar dakin Layla da ta tura, a zaune ta sameta a kasa, ta dora kanta saman gado, karasawa Mami tayi tana zama gefen gadon, sai da ta zauna, Layla taji gadon ya motsa sannan ta san ta shigo.

Nata hawayen da suke zuba ta goge da sauri, muryarta a dishe tace

"Mami..."

Wani irin kukane ya kwacewa Mami da yasa Layla matsawa tana dora kanta a jikin Mami din, itama kukan takeyi

"Dan Allah Mami ki yafe mun, ba zan sake ba. Dan Allah Mami, ban san ina zan saka raina ba, ina jin tsoro Mami...sosai ina jin tsoro"

Layla take fadi tana wani irin kuka

"Shikenan ko Mami? Babu wanda zai sake ganina da mutunci, kowa zai ce mun yar iska... Wallahi Mami ni ba yar iska bace, ki yarda dani, ban san me ya faru ba, kuskurena daya na dauka, nice naje gidan su Hamma, da banje ba, kuskure daya nayi Mami, amman kowa ba zai jini ba, kowa ba zai mun uzuri ba ko? Kema bakya sona yanzun, na san kin daina sona, Abbu ma haka, na muku laifi, Mami za'a zageku saboda ni..."

Hannu Mami ta dora saman kan Layla tana son ta bude baki tace mata tayi shiru, amman ta kasa magana. Tunda abin ya faru ta tattara hankalinta kan yanda mutane zasuyi mata surutu, sam bata duba Layla ba, kaddara ce ta fadama yarinyar, irin kaddarar da take zama darasi akan mutane da yawa. Batayi tunanin halin da Layla take ciki ba, kalar tunanin da takeyi, abinda take ji ita. Duk batayi tunani ba, da gaskiya sosai a zantukan Layla, kuskure daya tayi, amman babu wanda zai mata uzuri, su duka babu wanda zai musu uzuri.

Tasan mutane da yawa zasuyi mata kallon uwar da tayi sakaci akan tarbiyar yarinyar ta. Batace ana iyayi a tarbiya ba, amman ana kuskure, ba kuma kullum kuskuren yakan zama sakaci ba. Tsanani na zama mafita a cikin tarbiya, wasu lokuttan kuma tsananin kan zama silar gurbacewar tarbiya, haka sanyi akan tarbiyar ma. Abu daya zata iya cewa ta fahimta a cikin tarin kalubalen da yake zagaye da kula da kuma tarbiyar yara, shine babu abinda yake isa, kullum ka kara idan zaka iya, kayi kokarin karawa koya ne, ka fahimci yaranka, saboda duka kalar tarbiyar su bata zama daya.
Chapter 78 · 0% Book details