Sashe 35
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin ta kalli Rayyan da alamar su tafi, ledar hannunta shikuma ya karba, yana kama hannun nata suka wuce cikin yanayin da ya burge Anisa matuqa. Ita daman saboda Anisa ne ta mike, saboda bataso ma Rayyan ya kalleta, ciwo bai hana wani irin kishi rufe ta ba. Yanda ta damqi hannun Rayyan yasan ciwo take ji, ba zaice ga yanda ciwon da take ji yake ba, amman ya san shi a karance. Shisa yanzun yaji har kasan ran shi, tsayawa yayi yana kallon yanda take runtsa idanuwanta
"Sannu..."
Ya furta yanajin kamar ya dauke mata ciwon da take ji, amman babu halin hakan, ganin tana shirin tsugunnawa yasa shi kama hannunta yana hanata. Juyawa yayi ya dan tsugunna, cikin tashin hankali Layla tace
"Hamma..."
Saboda taga yawancin mutane sun fara kallon su
"Zaki hau ko saina watsa miki mari?"
Rayyan ya furta, gara ya dauketa zuwa gate, watakila su sami abin hawa, tunda yaga tafiyar wahala takeyi mata. Bata taba hango kwatankwacin abinda yake faruwa yanzun ba. Rayyan ne, tana hango abubuwa da yawa da zasuyi tare, fiye da rabin abubuwan da tasan a tunaninta kawai zasu tsaya saboda shine, amman abinda yake shirin faruwa yanzun abune da bata taba hangowa ba ko a tunanin nata. Dogon wandone a jikinta da riga, da zata fito sai ta dauki hijabin da Mami ta dinka mata, dogone kusan har kasa, sallah take yi da shi. Yanzun ma shi hannunta ya fara tabawa bayan ya kirata, shisa ta saka.
Ta fara tunanin yi mishi gardama, sai taga dama ce ta samu da bata san ranar kara samunta ba
"Sai ka kara tsugunnawa"
Ta fadi, sai da yadan juya yana harararta, murmushi take dannewa, saboda yanda yayi din kamar dole aka saka shi bashi yasa kan shi ba. Sosai ya tsugunna wannan karin tana hawa bayan shi, ta zagaya hannuwanta ta riko mishi wuya, mikewa yayi kamar bai daga komai ba
"Kasheni kike son yine halan?"
Ya fadi dakyar saboda yanda ta shake mishi wuya
"Ba zaki sakar mun wuya ba"
Ya sake maganar yana karbar ledar hannunta, sassauta rikon tayi, amman sai takejin kamar zata fado, musamman daya fara tafiya
"Allah Hamma zan fado"
Shiru Rayyan yayi yana kyaleta, ya zabi ya maida hankalin shi kan yanda zuciyar shi take bugawa akan Layla da take kwance a bayan shi
"Da gaske nakeyi zan fado... Allah Hamma"
Saboda duk tafiya idan yayi sai taji kamar ta kara sumbulowa, sosai take mamakin yanda yara suke nacewa goyo, babu wani abu mai dadi a cikin shi, ita kam har jiri-jiri take gani. Ciwon daya murda matane ma yasa ta kara saka kanta cikin wuyan shi tana makale shi sosai. Tsaye Rayyan yayi yana runtsa idanuwan shi ya sake bude su
"Na kusan yaddaki kasa idan ba zaki daina motsi ba"
Dago da kanta tayi
"Ya zan daina motsi? Ko yara idan aka goya su baka ga suna motsi ba?"
Hannuwanta Rayyan ya kama yana shirin banbaro su daga wuyan shi, ta saki kara tana dariya
"Yi hakuri... Allah ya baka hakuri, na daina"
Qwafa yayi yana rike hannuwanta saboda bayason zagaya su ta baya ya tallafeta.
"Hamma..."
Ta fara ya katseta da
"Har surutu idan baki daina ba yaddoki zanyi"
Shiru Layla tayi tana jin idanuwan mutane a kan su, amman ko a jikin Rayyan, tafiya kawai yakeyi kamar gabaki daya filin makarantar su kadaine a cikin shi har suka fara hango gate.
"Bansan me kike ci da kike da nauyi haka ba"
Dakuna fuska tayi
"Ni ce nake da nauyin?"
Ta tambaya
"In kika kara magana saina jefar dake"
Shirun ta sakeyi, daman shine yayi mata magana, tunda ai tayi shiru. A gate ma ta tsammaci ko a cikin security din wani zai musu magana. Amman meye basu saba ji ba, idan ma sun tare su ko da ba kanwar shi bace da yace musu kanwar shice zance ya kare. Sai da suka fita kofar makarantar sannan ya sauketa yana mayar da numfashi. Da gaske yayi mamakin nauyin da take da shi, wuyan shi duk ya gaji, haka bayan shi ma. Napep ya tare musu suka shiga, kusan rabin jikin Layla akan shi yake
"Layla jikina zaiyi ciwo"
Rayyan ya furta yana kamata ya kara gyara mata zama yanda zata kwanta a jikin shi kamar bai gama mitar zaiyi ciwo ba. A haka har suka karasa kofar gidan su. Shiya kamata ta fito ya sallami mai napep din tukunna suka shiga cikin gidan. Kana jin hayaniyar mutane, amman kowa na daki, kan shi tsaye dakin su ya wuce yana daga labulen hadi dayin sallama. Bilal da yake kwance daga shi sai singlet ya mike babu shiri ganin Layla. Riga ya dauka da sauri yana kokarin sakawa, itama Layla sadda kanta kasa tayi. Yana karasa saka rigar ya tsayar da idanuwan shi cikin na Rayyan.
"Zazzabine a jikin ta, ba zan iya barin ta ba"
Rayyan ya fadi, saboda ya ga tarin tambayoyin da suke cikin idanuwan Bilal din tun kafin yayi su. Har lokacin kuma kallon shi Bilal yakeyi, saboda na farko, abinda yake damun Layla din bawai na asibiti bane ba, na biyu, a hostel din tana cikin yan uwanta mata da zasu fi fahimtar matsalarta, na uku, baiga dalili kwara daya da zaisa Rayyan ya dauko ta ya taho da ita ba. Na biyu ina yake so ta kwana, gidan maza ne, idan kaga mace to wani cikin kabilun da suke hayane ya kawota, tunda ko yanzun ma akwai budurwar wani Joseph da yake gidan, kusan sati daya kenan da tazo. Amman babu wani hankali a cikin abinda Rayyan yayi tunda basu da inda zasu ajiye Layla, kuma hauka yakeyi idan yayi tunanin zasu kwana a daki daya su duka ukkun.
Ko da ace ciki daya suka fito gabaki daya abune da zai zama zabin su na karshe a matsayin su na baligan musulmi, kuma hausawa. Shisa ya zabi yace
"Allah ya kara sauqi"
Ya juya ya dauki wayar shi, takardun da yake nazari yana karasawa ya zira takalman shi da suke gefe ya daga labule ya fice daga dakin. Irin halayyar nan na daya daga cikin halayen Bilal da bayaso. Layla takalma ta cire tana karasawa kan gado ta kwanta, dan bata da lokacin ganin jin dadi ko akasin haka a fuskar Bilal. Rayyan ledar hannun shi ya ajiye, yana bin bayan Bilal din
"Bilal..."
Ya kira ganin harya kusan karasawa dakin su Shehu. Juyowa Bilal yayi amman ya tsaya a wajen, sai Rayyan dinne ya taka ya same shi
"Idan kana da abinda zaka fada mun ka fadamun, bana son ka dinga bani attitude..."
Ya karasa da gajiya a muryar shi, cikin idanuwa yake kallon Bilal din
"Me yasa zaka dauko ta? Meye zakayi mata anan da ba za ayi mata a hostel ba?"
Da sauri Rayyan ya amsa da
"Kulawa, zan kula da ita anan"
Numfashi Bilal yake fitarwa, ran shine bayaso ya baci sam
"Ka manta gidan maza ne nan Hamma? Ina dacewa ta kwana a cikin gidan nan? Me yasa baka tauna abinda zuciyarka ta raya maka kafin ka aikata? A hostel zata kwana da wasu a daki, idan tana bukatar taimako zasu fi saurin bata, anan fa? Ita kadai zata kwana..."
Kai Rayyan ya girgizawa Bilal, duka a cikin abinda yayi baiga na fada ba, yaje ya dubata yaga tana zazzabi, idan ya dawo hankalin shi ba zai kwanta ba shisa ya daukota ya taho da ita. Baisan yanda zaiwa Bilal bayani ya fahimce shi ba
"Zan kwana da ita"
Yanda Rayyan din yai maganar yasa Bilal jinjina kan shi da ya fara alamar ciwo
"Kai da ita? A daki daya?"
Kai Rayyan ya daga mishi
"Ni ba bacci zanyi ba, ina zane. Kuma zan duba abu haka. In tana bukatar wani abu zan sani"
Idan ya tsaya zai iya fadar abinda zaizo ya dame shi, ko kadan Rayyan ba rashin dacewar su kwana daki daya da Layla yake gani ba. Tunanin shi ya tsaya a iya kula da ita ne, baisan ta yanda zai nuna mishi illar hakan ba, musamman wani abu daya tokare mishi kirji ya hana mishi tunanin komai
"Sai da safe"
Ya iya furtawa muryar shi na fitowa a shaqe, kai Rayyan ya jinjina, yana bin Bilal da kallo harya shiga dakin su Shehu, sannan ya koma. Layla ya samu in ta juya nan ta juya can
"Kin ci abinci?"
Ya bukata, kai ta girgiza mishi
"In hada miki tea?"
Da kai ta sake amsa shi, Bilal ya dauko musu wani flask daga gida, yakan dafa tea saiya saka musu a ciki. Yanzun ma cike yake, hada ma Layla kawai yayi yana mika mata kofin ta tashi zaune. Ya hada mata shi da kauri sanin bata ci komai ba, a hankali take kurba tana kallon shi ya natsu kan zanen da yakeyi, zaka iya rantsewa kamar baisan tana dakin ba, sanda ta gama shanye ta danji sauki-sauki. Kawai saita tsinci kanta da son ganin me yake zanawa. Dan haka ta mike tana zuwa ta gefen shi ta leqa, dago kai yayi
"Bana son gulma, ki tashi daga saman kaina"
Turo baki tayi
"Ba aljanu ne da kai ba balle kace na tsaya a kanka zasu ta shi"
Ganin ya motsa yasa ta yin tsalle daya tana matsawa, dariya takeyi ganin yanda yake kallon ta, ta san da lafiyarta kalau saiya masgeta. Shisa ta rufa ma kanta asiri ta koma ta kwanta
"Meye kake zanawa Hamma?"
Ta tambaya, banza yayi ya kyaleta. Kawai dan ta dame shi ne yasa ta dinga mishi tambayoyi, towel din da yake kan kofa na Bilal ya janyo ya ajiye a gefen shi, surutunta har tsakiyar kwakwalwar shi yake ji
"Kaji Hamma..."
Layla ta fadi, ko kadan bata ga dago towel din ba sai da ya shauda mata shi
"Mayya ce ke?"
Towel din ta janye tana ajiyewa gefe, juya kwanciya tayi. Ya furta kalmar daya san zata bakanta mata rai hankalin shi ya kwanta. Zanen shi yaci gaba dayi har sai da yaji shirunta yayi mishi yawa, dubawa yayi yaga tana bacci. Net din da tunda Bilal ya daura musu shi suke fada a kai ya saki yana gyara mata sosai. Kuma kawai dan ya cakar da Bilal din ne yasa shi fadin