Sashe 8
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kuma san cewa, tunda Hikmi yayi fushi dasu, dakyar ya dawo gare su, dan haka ya fara tanadin yadda zai dawo gare shi, amma dole sai ya tsaya yaga yadda zasu kaya da yarinyar.
      ......
Tafiya yake a cikin duhu, yaji an rike mishi hannu, a hankali tace mishi.
"Muje na isar da sakon da na kasa, bana son yadda kake rayuwarka! Kaji."
  Bude wata kofa akayi yi haske ya cika mishi ido, firgi ya mike tare da ganin Na'am tana d'aga labulen d'akin shi.
"Bakwai saura kwata, shi yasa nace ka bar zuwa wayon dare amma dake kunnen kashi gare ka gashi ka rasa sallar asuba, tashi kayi sallah."
     Ban daki ya shiga yayi wanka da alola, sannan ya fito daga ban dakin jallabiyar ya saka ruwan madara da hularta, ya shimfid'a abin sallah ya fara gabatar da sallar.
   Yana idarwa ya mike, kamar ba zai shiga makarantar ba, ya kuma shirya cikin kananun kaya ya dauki jakar shi ya tsaya gaban madubi ya gyara gashin kan shi, sosai sannan ya sauko.
  Kallon Muniba yayi sannan ya kauda kanshi, ya ja kujera ya zauna.
"Amma ya dace zaman gida?"
" Ai gwara kayi mata magana na rasa gane kanta, tace ita bazata bai sai ka daina kula yan mata."
Kura mata ido yayi sannan ya sauke wata irin murmushi me tattare da miskilancin, sannan ya É—an dibi abincin shi ya fara ci a hankali yana yi yana kallon agogon hannun shi.
  Yana gamawa ya mike, sannan yace.
"Indai akan yan mata ne!"
Fita yayi har ya kai bakin kofar fita ya saka madubin shi yace.
" Sai hakuri."
Daga haka ya gyara zaman jakar shi yayi ficcewar shi daga gidan.
    ---
Fadar da Abban Ablah da kuma Umma Fouzan suka min kamar nice na karya kaina da gangan, dan haka nayi kuka kamar idanuna zai fita, daukar takardun asibitin yayi yana dubawa yaga ashe tsagewan kashi ce, ba karaya ba.
  Ajiyar zuciya yayi sannan ya kuma ajiye ya fita, washi gari ina zaune Umma Fouzan ta kawo min wani kwando cike da fulawa tare da wasu takardun gaisuwa tare da ban hakuri akan abinda ya faru. Sai wasu kayan zaki.
  Yadda ta kafe ni da ido ya sani kauda kai nace mata.
"Ban san shi ba, ki ajiye a inda ya kawo!"
Na cigaba da abinda nake.
    ----
Hmm! Yaron ya takura min sosai, har takai ya shigo cikin gidan, sabida kawai ya bani Hakuri abinda abokin shi yayi min, sai da Umma Fouzan tayi min fada, sannan nake kula shi.
   Tun daga ranar, yana tasowa zai tafi makaranta zai biyo ya duba ni, idan kuma ya taso ma haka zai biyo duba ni.
  Har na cika kwana sha biyar, da dauri, shi yazo ya kawo ni aka warware min suka duba ya had'e kashin. Daga nan na tako har ajin mu, Barka yan ajin suka min, nayi godiya dake duk zaman da nayi, a gidan nan shi a banza ba.
Muna karatu musamman Ni da bana makarantar, ta online Class.
       ...... Hango d'an iskan yaron nan nayi, yana ajiye motar shi, addu'a nake Allah yasa nazo da wani abu me tsini, duba jakar nayi naga babu wani abu me tsine, har zan rufe sai naga ashe akwai yar roban kayan karafunan lissafi, budewa nayi na dauki Abinda zan dauka ina murna, ina maida jakar agogona yana faduwa kasa, dauka nayi dai-dai fitar malamin na fita da sauri ina gyara zaman agogona, ashe bai zauna ba, da sauri nake sauka, na shiga ts tsakanin motocin da suke gurin, ina zuwa gurin motar shi, na kace tayar gaba.
   Take yayi wani fitar da iska, na kuma komawa gefe na cake tayar gefen, ina gamawa na juya zan tafi, muka yi tawo mu gama dashi, karfen da agogona suka zube na juya da sauri na bar gurin, zuciyata na wata irin bugawa, na tsoro. Bai fahimci abinda nayi mishi ba, sai dai ya dauke karfen da agogona yana juyawa, cike da mamaki.
            Ganin motar ya sauka kasa ce yasa shi fahimtar, abinda na aikata mishi daukar agogon yayi ya saka a cikin aljuhun shi, tare da dukar motar da hannun shi, ran shi na kara b'aci.
Idan dalibai suka san abinda ya faru da shi, tabbas zasu mishi dariya, dan haka. A fusace ya nufi ajin mu.
   Tunda ya shigo naga yadda idanun shi, suka kad'a jajjur har jini na kwantawa akai ya sani kauda kaina cikin tsoro. Ina shiga ajin naga babu agogona, kafin nayi wani yunkuri na hango shi yana tawowa.
 A hankali yake takowa har zuwa inda nake, ya dafa hannun shi akan tabirin da nake yace.
"Kin shirya?!"
Banza nayi da shi, kawai yasa kai zai fita, kawai yace.
"Toh bismillah!"
     Daga haka ya fita, ban damu ba, kawai dai naji a raina bai da mutunci kuma zai iya kuma min abinda yayi ranar, shi yasa da aka tashi nazo fita na kiyayye fita da sauri.
   Duk yadda nasaka rai zai min abu bayi ba, sai ma shirin da muke da Hikmi, take rashin ya kuma b'aci, dan haka ya shiga hada mana abinda zai rabamu.
   ..... Bayan sati biyu.
Na fito da sauri zan, isa inda muke haduwa da Hikmi domin yaron yana da ilimi sosai, sai naga baya gurin, dan haka na juya zan koma aji. Kawai naji yan mata suna ta min dariya ban damu ba, sai da wata tace min.
"Amma gaskiya kina da jiki me kyau."
Kallonta nayi, dariya suka saka sannan ta mika min wayar hannunta, tare da sanya min magudanar kallon, a hankali ya fara tafiya, Hotona ne gani a gaban wani Bature yana shafa jikina, a tsorace na sake wayar ya fadi kasa.
    Ji nayi kamar bazan iya daukar kaina ba, na zube kamar danyen nama a kan ciyawar da take gurin, kuka yaki zuwa min, kawai na mike ban tsaya ba, sai a filin da suke buga kwallon kwando, basa gurin suna cikin makaranta dake guda biyu ne, ina shiga gurin na same su da Hikmi, sai fada suke shida Abeel babban shaidanun yana zaune. Asood da Bilal suna raba su, ina zuwa na same shi yana fadin.
"Idan yar uwanka aka tozarta zaku ji dadi? Insha Allah sai kunyi dana sanin abinda kuka aikata, haba don Allah."
   "Muje Hikmi! Na Barsu da Allah."
     Juyawar da zanyi naga abu ya fado daga aljuhun wandon shi, kallon abin nayi da ido, naga an rubuta,(Golder ring condom) wani irin kuka ne ya kwace min, lokacin da na fahimci, sun rufe kofar da na biyo, shi kuma sun saka shi a tsakiyar su suna mishi dariya.
"Ai mun gode maka, gashi nan ta yarda da kai, kai kuma kayi sanadin kawo mana ita. Jay gaya mana ya zamu yi da ita?;"
    "Ku barsu su tafi!"
Saukowa yayi sannan ya tako zuwa gabana, yana kallon yadda nake kuka me mugun ciwo, ya amshi jakata ya ciro wayata, ya mika min yana murmushi yace.
"Ya kika ga wasan? Hmm" daga haka ya juya ya fita, raina ya b'aci dan haka na fita da sauri, ina isa inda ya ajiye motar shi na dauki wata sandar da naga ni na buga a jikin gilashin motar sai da ta fashe.
     Bai kalle ni ba, na tsaya a gaban shi, ina mishi kallon kaskanci.
"Idan ka fasa daukata tsirara ka rena Iyayen ka, banza wanda bai san darajar mutane ba, wawan Yaro kawai kai har ka isa ka tozartani? Wallahi baka isa ba, kuma ni da kai shege ka fasa."
   Daga nan na wuce abuna, tun daga ranar bamu kuma, yin wata rigima ba, dan hoton ya zaga makarantar mu.
  Har takai malamai sun min caaa, aka kirani zuwa ofishin shugaban makarantar, koda na shiga na same su. Kallona suka yi na sanan suka shiga tambayana, abinda ya faru.
Ban boye musu ba, Jay da abokan shi suka min haka, sannan Ni ba jikina bane fuskata aka dauka, dan haka suka kira Jay, ai kuwa yana zuwa, ya tsaya suna tambayar shi, yace shi yayi kuma bashi bane Abeel ne, kallon shi Mahaifin shi yayi cikin damuwa dan yasan zasu dakatar dashi na kwanaki ne.
. Aikuwa haka ce ta faru aka bani hakuri na fita, bayan na tafiya suka mishi fada sosai.
   ...... Wata guda suka dakatar dashi, amma yana karatun shi, a (online) haka da ya faru ya dawo min da kimata, dan haka na fita hanyar kowa, shima kuma Hikmi na rabu dashi dama shige min yayi muke karatu tare.
      ......
Na mai da hankalina sosai kai karatu, dan haka koda ya dawo, bana shiga harkan kowa, sai dai wannan karon ya dawo da zafi ne.
  Abinda ya fara min, shine sanyawa malamai suna hanani shiga ajin su, karshe na kuma zuwa gaban mahaifin shi, aka shiga tsakanin mu, amma bai hakura ba.
..... Haka zasu saka hotona, suyi b'atanci akaina, ban kuma magana ba, sai ma kauda kan da nayi, abin yana damuwa.
     Watanni uku muka fara jarabawar zango na farko, aikuwa zance Alhamdulillah. Sai dai ranar da zamu gama jarabawa aka wurgo min, da takardan satan amsa, kawai akan idanun me kula da jarabawar.
  Duk yadda naso dakatar da kar a soke min jarabWata, sai da aka yi, nayi kuka kamar idanuna zai fita. Shi kan sa da yaga yadda na rikice ina basu hakuri sai da jikin shi yayi mugun sanyi, zuwa gaban shi nayi nace mishi.
"Hankalinka ya kwanta? Ka rama abinda nayi maka, toh nagode sosai, amma ka sani wallahi sai na rama."