← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 72

Sashe 55

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Fatimah!" Ya kira suna na da karfi, sabida jinin da ya gani yana bin kafana, yaso ya taimaka min, naki. Amma haka ya nace min, har muka gama wankar, ina fitowa shima ya fito, shiryawa yayi sannan ya fita. Can sai gashi da leda, har nasaka kayana na zauna ya sani na cire mishi wandon, kamar zanyi kuka.

Haka na cire, ya gama duba ni sosai, sannan yayi min alluran kashe zafi. Kafin ya dawo ya rungume ni muka kwanta. Duk da na gaji, amma ina son komawa gida. Haka yayi ta lallabani har muka yi barci ina kwance a jikin shi.

Karfe biyu na rana muna farka wanka muka yi tare da sallah, duk abin da yake min na kasa sake jiki dashi, haka ya fita ya sayo mana kaya, wasa wasa, ya shiga min wani irin salo, wanda ya sani jin wani irin tsuma sosai a raina.

Bai nemi kome ba, amma Tabbas salon shi mai tsayawa ne a rai. Na kasa magana biye mishi nake, da zaran naga zai sab'a Number, sai nayi maza na dakatar dashi. A hankali muke ta shagalin mu, har dare. Kasa hakuri nayi na mishi magana akan ya mai dani gida, cewa yayi.
"Ni ban gama amarci ba, idan na gama da kaina zan kai ki."

Haka muka kwana, washi gari ne na fadi gaskiya na, domin Jay ya biyar dani, hanyar da ya dace sai da nayi kuka wiwi, sannan ya kyale ni, muna yi wanka. A hankali nake tafiya sabida yadda nake jin jikina. Kasa wani dogon motsi nake ina zubda kwalla. Har na shirya ce min yayi.
"Idan baki daina kuka ba wallahi bazan mai dake ba." Haka naja baki na shiru. Har yanzun lokacin ya gama mulkin shi sannan ya sani a gaba muka dawo Abuja, tun a bakin kofar nake tsoron shiga sabida Mamah da fadar da zata yi...🙄😸😹 Honeymoon honeywahala
10/23/20, 10:04 AM - Ummi Tandama: *Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi*

Ban kuma tsinkewa da Jay baya yina ba, sai da na fito matar shi ta tsare ni zata min rashin mutunci, Rumah ta dakatar da ita.
"Kina wani abu kamar Jahila! Kina hauka akan mutumin da ya kusan kare minti arba'in a cikin d'akin ta.

       Haka bai ishe ki ba? Haka bai nuna miki ita ce abin da yake bukata ba."

"Rumah! Bana son damuwa, mata ta zo muje." Ya mika mata hannu! Cikin dauki da murnan ta mika mishi hannu. Yadda ya rike ta sai da ta kalle shi.

       Suna barin shashin, ya makureta a jikin bango, tare da zare mata idanu.
"Wallahi Munih kina kure hakurina, idan na kuma ganin kin zagi Aanih sai na karya miki hannun ki. Wacce bata san ciwon kanta ba."

                  Sake ta yayi ta fadi kasa, sannan yayi wucewar shi, sashin sa. Yana shiga dakin shi ya d'aga labulen da yake kallon inda su Aanih take, a sanyayye yake kallon yadda take niman shi. Tana duba ta inda zai ɓullo amma har ta shiga cikin motar babu shi babu alamar shi.

  .... Har ta zauna ta kuma fitowa, domin gyara zama. Kamar ance ta d'aga kai ta hango shi yana kallonta, sake labulen yayi tare da juya bayan shi, ga tagar.

     ---
Tunda na gan shi yana leke na abin ya bani mamaki da al'ajabi, kawai na shiga motar tunda ba zai min amfani ba.

          Tunda muka dauko hanyar gida, na shiga damuwa sosai. Domin naga sakon Saif da ya turo min akan gashi a gaban Dangina, ya kawo ƙara na akan abinda muka mishi ni da Jay.

        Tunda naga sakon jikina yayi sanyi, na rasa yadda zan gaya mishi abin da min bai kyau min ba. Haka nayi shiru, can naji Ummi tana magana a hankali. Tare da bawa Baabi hakuri.

       Can ta kashe wayar sannan ta juyo gare Ni tace min.
"Meye amfanin abinda kika yiwa mutumin da zaki aura? Kin ja min Bankad'a  a cikin danginki. Sunce nice nake sanya ki abubuwa saboda d'an yar uwata meye yayi zafi da Mahaifinki yake min barazana akan aurena?"

  Shiru nayi tare da sunkuyar da kai na ƙasa, har muka isa sokoto.. Ummi waya take cikin harshen kanuri, ban san meke faruwa ba, amma naji Hanisah tana ce min.

        Baabi ya haɗa Ummi da Babanta ne shi yasa take ta magana tana faɗin gaskiya.. har muka shiga cikin gidan. Inda na samu yan uwan Baabi da Saif ana jiran mu, Ummi bata tsaya ba tace zata yi sallah idan zasu iya jiran mu toh.
   Tsoto ya kamani musamman da naga dangin mu baki d'aya, har da kakata Ummi.

        Bayan mun idar muka nufi inda ake tattaunawar,.ina bayan Ummi. Dake ranta ya b'aci sosai zama tayi tana kallon kowa a wajen tarr.

          "Assalamu alaikum jama'a Barkan ku, ba wani abu ya hada mu anan ba, sai magana akan abin kunyar da Fatimah take shirin aikatawa a cikin masarautan nan! Jiya da dare Saif ya kirani yana gaya min Ya kama Fatimah da D'an Sarkin daura da ita suna masha'ar su."

Ba iya Saif ba hatta ni sai da muka kalli Bana Annuwar, jikina ya dauki rawa sosai, kamar wacce aka jona min lantarki.

          Kallon Baabi nake kam shi a sunkuye, tare da kallon Saif shima na shi a sunkuye, wani irin kuka ne ya kwace min.  Na shiga rantse rantse.

        "Wallahi babu abinda ya haɗa Ni da Jay, asalima fada suka yi Saif ka fada musu gaskiya mana"

  ..shiru yayi, sannan Baba Annuwar ya shiga fadar wasu abubuwan masu daure kai da muni, wanda sam ban aikata ba, kallon Baabi nayi tare da son ganin shin ya yarda da abin da suka ce, amma yaki kallona.

       Nan kowa ya shiga fadar albarkacin bakin shi. Daga nan suka min cin mutuncin akan Jay. Juyawa da suka yi zasu zagi Jay Ummi tace musu.
"Baku isa ba! Baku haifu ba, yar ku dai ku mata fada amma duk wanda ya Kuskura ya zaga min d'a ko ya sake kazamar bakin shi akan Jalaludeen. Toh na rantse da Allah sai masarautan nan ta tashi tsaye da kafaffunta.

     Sannan kai Annuwar da kake maganar cewa Jay da Aanih suna masha'ar su, kai meye ribar tozarta d'an uwanka a gaban jama'a?

  Meye amfanin cin fuska haka, sabida yana da hakuri ko? Sabida baya fada baya kome duk abinda zaku mishi akan ta bazai tab'a cewa kome ba.

       Toh wallahi ku kiyayye abinda zai sanya shi yayi magana, kai kuma Saifullah zaka aureta ko ba zaka aureta ba?"

    Bakin shi na rawa yace.
"Zan aureta!"

      "Tashi kar na kuma ganin me kama da kai sai ranar auren ku" da sauri ya mike, yana fita ta shiga gayawa yan uwan mu magana, tare da cin mutuncin su. Kamar yadda suka yiwa Baabi, cikin izza tace musu.

"Ban da nima a cikin nima, haramun ne da sai an nimawa Jalaludeen auren yarku muga ta karshen tsiyar ku, kuma a biya sadakin da ba'a tab'a biyan wata mace da shi ba a cikin masarautan nan ba."

Korata tayi sannan ta zauna tayi musu wankin babbar riga, sannan ta bar falon abin ta, tana zuwa ta amshi wayar hannu na, tare da kashewa.

   Bayan tafiyar ta, nan suka shiga fadan abin da yayi musu, har da cewa.
"Matukar  Aanih ta auri yaron nan babu mu babu ita. Taje can su kara ta, dan bazata  ja mana faduwar daraja ba, daga masarautan Zazzau ba."

                      "Hmm! Ban san me yasa Rahil take takama ba, ban san me yasa take jin ita wata ce ba, ko ce mata aka yi muma sakarkaru ne da zata zauna yana gaya mana magana, son ranta wato d'an Yar uwanta shine abin burgewa ta kare laifin shi.

        Toh Wallahi duk abinda take ji zata samu, dan.."

Shiru tayi sakamakon haÉ—a ido da suka yi da Ummi tazo gurin Baabi.
"Hajiya kenan! Da fatan na barki da ɓaɓatu! Duk ba laifi bane, amma kin san kome lalacewar gawar Giwa tafi kwando tara,"
Gaban Baabih taje suka yi magana sannan ta d'ago kanta. Mik'ewa yayi sannan ya basu hakuri da abinda ya faru.

......
.  Haka da yayi musu ya masifar d'aga musu hankali, nan suka fita daga gidan. Aka shiga yawo damu a cikin Zuri'ar mu.

   Su lallai Baabih ya min fada tare da Ummi, shi kuma bai ce komi ba, sai ma zuba ido da yayi.

    Abun ya zama rikici da ya janyo aka hanamu shiga cikin gidan kakanmu, hatta wasu abubuwan an hanamu shigar cikin shi, balle kuma irin su Suna da wasu abun.

..... Matar kanin Mamana ta haihu dan haka nayi ta rokon Baabih ya bar ni naje, ni da Hanisah. Muka tafi mun je an karb'e mu hannu bibbiyu. Muna zaune a dakin Ayyah kakanta ta gurin Mahaifiyata.

Sabirah da Hoor, suka shigo y'ay'an maza muke dasu, Baban su ke bin Mamana, suna gani na suka fara dariya tare da faÉ—in.
"Makara! Kece a gidan sunan bayan an hanaku fita sabida ana gaya muku gaskiyar da baku so?"

      "Shi yasa naga ganku cikin sanin ya kamata, zancen manyan na manyan ne, mu yara ina ruwan mu."inji Hanisah, wata irin B'oyayyen ajiyar zuciya na sauke tunawa da nayi ita din gwana ce a masifa, gyara zama nayi tare da zuba musu ido.

         "Ke karki min rashin mutunci!" Inji Sabirah.

Budar bakin Hoor tace mata.
"Ai gado ba karambani bane, abinda aka sha a non..."
Chapter 55 · 0% Book details