← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 72

Sashe 18

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Zai sha bakar azaba da nacin Bala'i, domin bata iya dogon magana bata ambaci Baabi ba, abin dariya da tace min shekarunta  amma kullum tana nan kamar jinjira, tsabar kaunar da ka gina mata a zuciyarta.

               Yallabai nasan nayi maka laifi da na sace Yarka, sai da babu sauki Gaye irina a samu mace ta kwantsama mishi mari, ai kuwa kasan haka bazai ma sabu ba, shi yasa na dauketa ranar aurenta.  Domin nima na rama tijarar da tayi min.
          Kayi hakuri! Sunana Dr Mujaheed Harisou Agla! Don haka ga Yarka nan zaka iya kaita asibiti a kara bincika maka ita!"
. Yana gama fadar haka ya mike abinshi.
                     "Jay! Don Allah karka tafi"
"Ke manta dani! Zan tafi can nayi rayuwa ta, ki zauna kiyi aurenki amma ina son don Allah idan kin haifi mace! Ki ajiye min ita zan dawo na dauketa kuma ta faÉ—a soyayya ta."
."Jayyyyy!" Na kira sunan shi.
"Don Allah ka tafi dani! Wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimake ni, ban san lokacin da haka ya faru dani ba!"

        Juyawa yayi gaban jama'a yana kuma kallona, ya tako gabana.
"Ke zaki iya rayuwa mana, Insha Allah mijin ki zai zama mutum mai kamala."
.rufe mishi baki nayi cikin wani irin kuka, jini na zuba ta hancina ..
"Jay Ina sonka!"
Cike da mamaki yake kallona, sabida shi duk abinda nake bai fahimci cewa soyayya bace....
#Mai_Dambu....
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA HUDU
"Da gaske! Ina sonka ne? Don Allah karka ka min shiru."

   Dariyar da ban tab'a ganin yayi ba, ita ce yaƙe yi tare da nuna ni da yatsar shi.

"Meye amfanin cin fuska?! Idan baka sonta a bayyane yake tayi hakuri! Amma mu a halin babban gida mun san dajarar kanmu Yace da Mahaifinta ya zab'e ta sama da mutanen shi, zaka iya sadaukarwa haka, don Allah ka tafi Allah zai bata wanda take so." Inji Ummi Rahil,

     Daga haka ta riko hannuna tayi zata ja ni.
"Jay!"

      Na faɗa cikin kuka, bata dube shi ba, ta ja hannuna.

  Cire hannunta nayi, da sauri na sha gaban shi.
"Kace wani abu! Don Allah kayi wani abu! Karka tafi ka barni. Kai kace bazaka tafi ka barni ba. Me yasa zaka karya alqawarin da kayi min!

           Don Allah kayi hakuri kaso ne!"

      "Kinga ni bana jin kome akanki! Asalima Ni bana kaunarki! Wallahi bana sonki! Kinga ne kiyi hakuri ki...."

Kifa mishi mari nayi, kuma sai tsoro ya kamani, naja da baya.
"Kayi hakuri! Bazan kuma ba kawai ina ganin abinda idanun ka suke faÉ—a ne! Jay karka manta ina sonka! Ka fahimci sakon da zuciyata tazo maka dashi."

       "Yayi kyau! Amma bari na gaya miki! Ni bazan tab'a auren yar ashirin da biyar ba, balle ke da kika kusan haihuwa na,  talatin da hudu fa, ji min cutar kai! Ke bani hanya. Tsabar rashin tsoron Allah ina zan kai ki bazawara."

   . girgiza mishi kai nayi tare da riko hannun shi.
"Wallahi ba yadda kake tsammani bane, Jay"

    "Ke bani hanya na wuce, na kawo ki gidan ku ga iyayenki da danginki, kiyi zaman ki."

          "Babu inda ka! Ka dawo! Idan kuma kana ganin karya ne kafi daga gidan nan Mu gani! Jalaludeen D'an Jannart! Baka isa ka fita daga cikin zanen kaddarar mu. Ina sonka kuma ba zaka tab'a."

     Jini ne ya shiga zuba min, daga kowani kafa ba.  Juyawa naga cikin gidan yana min, a hankali na tafi zan zube yayi maza ya tare ni.

                          "Ku taimaka min! A kai ta asibiti."

           "Babu inda zamu kaita! Kai kuma mun gode! Amma ba zaka bar gidan nan ba, sai Har Mahaifinka yazo."

Inji Rahil!
"Ban gane ba? Wallahi tafiya zan yi! Tunda na dawo muku da Yarku!"..

        "Idan kasan darajar iyayenka zaka iya tafiya."

Shiru yayi kamar ya fasa ihu, tare da zama yana hararar kowa a falon, karban ta suka yi tare da kwantar da ita. Maganinta suka dauko aka fara shafa min..

      A hankali jinin ya fara tsayawa matse bakina suka yi zasu bani maganin, na watsar da su.
           Duk yadda suka so su bani maganin na sha, naki asalima guduwa nake son yi, sai da ya taso ya matse ni sosai, tare da amsar maganin ya bani da karfin tsiya.

        "Lallai!  Baka san wacece ni ba? Kuma dole itama ta mutu!"
           Ga baki daya ji yayi tsigar jikin shi ya mike me haka yake nufi.
         Addu'a ya fara tofa mata, wani irin ihu take tare da kai mishi duka, ina yakushin sa.

     Can na koma nayi likus, ban kuma fahimtar kome ba, sai da asuba.da ba tashi sallah.

       Ganin bakona ya sani komawa na kwanta, ina me jin haushin abinda na aikata na kasa b'oye son da nake mishi, yaro karami ya chaza min lissafi.

      ---
"Ni da na gama abinda zan tafi tunda mun fito sallah, ina son gobe na wuce Canada!"

      "Kayi hakuri! Mahaifinka yana zuwa! Dan tunda na ganka a Canada na shiga bibiyarka, sai gashi kai Khatoon kake bibiya.

                     Ban san me yasa na kasa daukar mataki akan abinda kayi min ba, sai dai nasanin soyayyar da nayiwa Janny gaskiya ce! Shi yasa ban ga laifinka ba.

  ..bazan maka dole akanta ba, tunda baka sonta, amma ka sani abinda kayi kusan kuskuren da Mahaifinka ya kwantanta kenan!"

      "Nifa ban fahimci abinda kuke nufi ba. Na bar iyayena a Canada! Akan me zan damu da wasu iyayen."

             "Ta yaro kyau take bata karki! Mu shiga ka karya sai kayi Sallama da Kanwar  mahaifiyarka zaka iya tafiyarka."

   Bazai iyawa Aaryaan musu ba, amma gaskiya yana jin Fad'uwar gaba, akan halin da yake ciki.

            ---
Karfe goma na safe, Jaamal da Sarah suka sauka tare da Aswad. A hankali suka karasa inda Motar da Aaryan ya turo musu, suka shiga.

     Basu san dalilin kiran su da Aaryan yayi ba, amma tsabar faduwar gaban da Jaamal ya shiga kamar zuciyar shi zata diro daga kirjin shi.

          Koda suka isa cikin gidan, wani shashi na daban aka kai su, har cikin falon Aaryaan suka isa, wanda yake zaune tare da Rahil. Tayi kuka har ta godewa Allah.

        Magana take a hankali, tana fada halin da suke ciki.

     Cikin sanyin jiki, Sarah ta nime guri ta zauna, tana kallon su. Abinci aka shiga jera musu.

      Daga bisani yace.
"Fulani Maryam ko zaki shiga daga ciki, sai su karya suma anan."

           Mik'ewa Sarah tayi ita da Rahil, suka shiga.
Tunda aka ajiye mata abin karyawa ta kasa ci.
"Hussainah zuciyata a tsora ce take! Don Allah gaya min meke faruwa! Ina Fatimah take."

          Riko hannunta yayi suka nufi d'akina, dai dai ba fito wanka kenan,ina zaune Hanisah tana busar min da gashina.

            "Alhamdulillah! Yaushe aka dawo da ita!?!"
"Jiya ta dawo da d'an uwan ta.

     Abin da mugun daure kai,.taya aka yi suka haɗu.?" Inji Rahil,

  Cikin kasaita wanda yabi jikinta da jininta, ta tako har cikin dakin. Tana kallona,
"Fatimah! Ince babu abinda ya faru.da aka dauke ki?!"

   Cikin jin nauyin abin na sunkuyar da kaina, kasa nace.
"Hum-uhum!"

"Ummin su waye d'an uwanta da ya dawo da ita haƙa?!"

    Jan hannun ta Ummi tayi, suka shiga d'akin ta, ta nuna mata abin karyawa, sai da suka gama karyawa sannan ta amsa kiran Baabi.

     Sun sami Jay a zaune tare da su Baabi, yaki magana. Duk yadda suka so yayi magana, yaki cewa kome.

.... Karshe Mamah Sarah ta zuba Mishi ido, cikin kaduwa tace.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangiji talikai! Jalaludeen!"

Ta faɗa a raunane, tare da tasowa zuwa gaban shi, ta zauna.  Hawaye na zuba mata, yau gani take kamar gata ga Janny.  Kuma rike hannun shi tayi cikin nata, kwalla ya d'aga cikin hannun su.

   Ta kuma d'ago kan ta, shima kuma ya d'ago nashi kan. Abubuwan da suka gabata suka shiga dawo mata, wani irin kuka na taso mata.
"Jay! Rabon ka shine ya salwanta da farin cikina, samun ka shine ya maye gurbin farin cikina, Jay don Allah kayi magana. Dani da Jannart guri guda muka zauna.

Abu daya muka so! Gashi nan a gabanka. Da nayi hakuri na bar mata Kawunta da yau tana raye cike da farin ciki, da nake fatan samu da itama ta same shi nima na same shi.

         Don Allah kayi min magana, kaji Yarona, kayi min magana. Idan ta kama na baka labarin amintar mu, tare da soyayyar mu. Duk zan gaya maka amma kayi hakuri kace wani abu mana."

    ...... Kamar ba zai magana ba yace.
" Toh me zance? Iyayena suna Canada! Yarinyar da na dauka na dawo da ita! Don Allah ku bar ni nayi tafiya."
Chapter 18 · 0% Book details