← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 72

Sashe 3

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    "Kinga babu kome! Jarabta ce! Kuma zan amsheta hannu bibbiyu. Sannan nafi ganin kamar canfe ne, da zaran munyi imani dashi wallahi itama zata iya tagayyara kamar Janny! Dan haka bamu yi imani da canfe ba, Allah ya bata lafiya."

        Lumshe idanuna nayi, ina kallon wasu mutane da suka saka wani yaro a cikin buhun hatsi,  mika hannuna nayi zan rike buhun, naji kamar yana kara min nisa.

        Kara mikawa nayi, Baabi yazo ya rungume ni.
"Baabi na! Sun tafi dashi ko? Ka gamsu can suna saka shi a cikin buhun hatsi! Zasu tafi dashi."

         Addu'a ya shiga tofa min kafin wani lokaci, barci ya kuma ɗaukata, ina ta surutu.

      ...."abinda ya faru! Ranar yake yawo a ƙwaƙwalwarta, sannan kuma takan manta dashi, amma yawan bata labarin Jannart shine yake taso mata da nata Ciwon dan haka babu wani abu, Allah ya bata lafiya."

              Haka suka kwana a kaina, Ummi tana gaya mishi gundarin Labarin abinda ya faru, a ranar. Sake baki yayi cikin mamaki yace.
"Akan me zaki dake shi? Kome yayi mata ina ruwanki? Wato kece ma kika yi sanadin barin shi gidan? Kai Amma wallahi banda wani dalili da na mare ki! Wallahi kin bani haushi fiye da kima.

   Gashi nan kin saulawantar da rayuwar d'an YAR UWARKI, ki barshi da Matar Uban shi, Mahaifin shi yaga min cewa.
   Yarinyar zata iya bada rayuwarta akan Yaron, shine kika mata gori akan dan ba ita ta haife shi ba? Toh ke da kike uwa daya Uba daya da Uwar Yaron, Kinga abinda kika aikata.

          Ita da bata haife shi ba, tayi abinda kowa ya gani babu me zaginta, shi yasa mana take kallon ki ranar da muka koma addu'o'in Allah ya dawo mana dashi, ashe kin san abinda kika aikata mata shi yasa take miki kallon abin.

      .toh wallahi ki shirya muje ki gayawa Jaamal abinda kika aikata ba shi ba, hatta Appa sai kin gaya mishi, domin kin zalinci zuciyar kowa! Kuma kin samu zubda kwalla sabida sakarcin ki na banza, nayi imani tayi hakuri ne sabida tana miki kallon Jannart ce a gabanta, da babu abinda zai hana bata miki rashin mutunci ba, kin bani mamaki.

      Aiko dan tarbiyyan da ta bashi, ya kamata ki d'aga mata kafa, bawai kice ta mishi tarbiyyan mugunta ba, dan haka ki shirya muje ki bata hakuri, tare da Uban Yaron, dan babu abinda zaki kuma yi nan gaba, sai dana sani mara iya ka da amfani..
#MI
#HWA
#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

{CIGABA KWARKWARAH}

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

Godiya sosai Maman Abba Allah yabar zumunci!🌹😍

UKU..
Haka Baabi Yasaka Ummi a gaba da fada har karshe ya bar mata d'akin, tana kuka da dana sanin, abinda ta aikata, a cikin daren ta haÉ—a kayanta kala daya.

Da asuba ta barni a hannun amintacciyar baiwarta, sannan suka nufi Daura.

Sun isa da wuri, dan haka sun sami ganin Sarki Jaamal. Bayan sun gaisa Sarki Jaamal yace musu.
"Amma kun fito wani guri ne? Dan naga kamar daga tafiya kuke?"

Sunkuyar da kai Baabi yayi sannan yace.
"Mun zo baka hakuri ne! Akan b'atar Jay! Shine muka zo domin mai d'akinka tasan kome!"
.gyara zama yayi sannan yace.
"Dan Rahil tayiwa Jay fada ya fita, shine zaku zo bani hakuri!

Rahil! Kanwar Jannart ce, kuma uwa ce mishi, koda me tayi bazan tsawatar mata ba, sabida tafi ni kaunar shi, kai jinka da Jannart tana raye zata yarda na dibo jiki kazo bata hakuri ne bata borance muku ba, wallahi ban tab'a jin kome akan b'atar shi ba.

Sai dai ina kyautata zaton cewa! Allah yayi hikimar haka ne dan wasu dalilai, da yana tare damu, bazai iya rayuwa babu kalubale na, dan haka babu komai."

Shiru duk suka yi sannan Aaryan yake gaya mishi, ai ga halin da nake ciki, shiru Sarki Jaamal yayi sannan yace.
"Karku canfeta, ku dauka jarabta ce! Domin yin haka dai dai yake da wasa da rayuwarta. Don Allah karki bari wani ya camfeta"

Wannan abun da ta gaya musu, yayi matukar tasiri a zuciyar su, har suka dawo gida, sun sanya dokar kar wani ya kuma cewa akwai wani abu a tare dani.

----
A hankali rayuwa take Gara mana, har na kusan gama jami'a, a lokacin na hadu da wani soja, muka makalewa juna, a waya dan a lokacin Waya ta shiga hannun kowa, idan muna wayar nan kamar zamu cinye juna, tun ina b'oyewa har na hakura kowa ya sani.

Aikuwa Adda kishiyar kakata, ta sani a gaba da Tsokana. Sai na gaya mata.
"Ke yar doguwa waye ne kuke magana dashi a wancan manta sabo."

"Addah ki fita idanuna na rufe ina ruwanki da darling dina, jeki gurin dattin ki, kuyi ta lallaba juna"
Maka min mahuhuci, Innono tayi kamata, na tura mata baki cikin jin zafi nace mata.

"Wallahi koda Baabi ya sayo miki maganin zafi ya bani, bazan kawo miki ba tunda kika buge ni!"

Ina tura mata baki.
"Yar kwaila kawai, dube ki don Allah waye zai yi asarar kudin shi ya auri mace ba kirji."

"Innono! Wallahi ki daina wannan maganar, zaki sanya ni dai na shigowa wallahi, ai haka Allah yayi ni"

"Karki kuma saka mana mijin mu" sake baki nayi tare da kallonta sannan nace.
"Yanzun don Allah sabida wancan takwarkwashen mijin ku,.kike min wannan wulakancin, na zata sabida kawai na tsokani yar uwanki! Toh wallahi sai na kuma!"

Make ni ta kuma, na tura baki na karar wayata ne ya katse ni, na dauka tare da sakawa a kunne na.
Gyara kwanciya nayi, sannan na lumshe idanuna, tare da bude shi nace.
"Barka hasken rayuwata! Muhid"

Murmushi ya sake, wanda naji sautin shi har cikin jikina, lumshe idanuna nayi tare da narkewa a cikin kujerun falon.
."farin cikina! Ya yau? Da fatan kina lafiya."

Juya idanuna nayi sannan na sauke ajiyar zuciya nace.
"Alhamdulillah! Da fatan kai ma haka;"

"Gamu nan muna fama zamu tafi gurin wani meetinga da fatan Kema haka!"

Nan muka tsinke da hira, kamar me, har Addah tana dukana, ban ce mata kome ba, sai yar kukan da na saka, muhid yayi ta min dariya.

Mun hadu da shine lokacin zamu aikin Hajji, shima zai tafi da Yan uwan shi da Maman shi, tun daga lokacin muka fara gaisawa sama sama, har muka dawo daga nan kuma soyayya ta bude Muhid Nasir Arkilla shine cikekken sunan shi, yana aiki da hukumar soja na kasar nan.

Yanzun haka yana garin Makurdi..shine yaro na uku a gidan su, yana da yayu mata biyu a gaban shi sai shi na uku sai kanen shi biyar.

Muna gama waya dashi na katse kiran na mike ina mita tare da shafa inda Addah ta zabga min duka.

Shigowar Kanin Baabi, Baba Annuwar, ya sani mik'ewa da sauri, sabida ban san me nayi mishi ba, yana dan jin zafina.

Tunda na gaishe shi, na sa kai zan fita. Ya bini da ido, da sauri na fice dan shine ÆŠan Addah na biyu, dan haka shima yana son kujeran da Baabi yake Kai.

Akwai wasu abubuwan da yake faru a cikin masarautar mu, amma bai da wani damuwa, kawai dai abin ya kasance kome sama-sama ne, kuma ana ƙoƙarin b'oyewa sabida mu yara.

Baabi yana da hakuri kuma duk abinda zaka mishi bai tab'a d'aga ido ya kalle ka.

......
Muhid ya gabatar da kanshi ga gidan mu, da ahalin gidan mu baki daya, sai kuma aka yi dace shima mahaifin shi, dan yana da sarautar a cikin masarautar mu,

Dan haka ba tare da wani tsawaitawa ba, aka saka komai cikin mutunci da girmamawa, domin anyi tunanin gwara ayi bikin nayi bautar ƙasa a dakin mijina.

Wannan tsarin yayi mana dad'i, dan haka na mai da hankalina guri guda, lokacin bikin mu na karatowa Kakanina na gurin Uwa suna ƙoƙarin gyara ni, ga matan Baabi, suma matukar ƙoƙarin na fito Matar so.

....
Haka aka yi ta shiri babu kama hannun yaro, har lokacin bikin yazo, aka fara duk wata shagalin da ake na al'ada, da sauran su a aure.

Sai dai a bangarena, tun saura kwana uku bikin na soma wasu irin mafarkai, masu mugun ban tsoro.

Ban damu sosai, ba har aka daura auren, ranar hankalin kowa ya tashi domin kuwa kin fita nayi ina kwance sai da Baabi ya saka aka b'alla kofar dakin, koda suka shigo sun same ni ina zaune, na cusa kaina a tsakanin cinyoyina, ina kuka sosai.

Zama Baabi yayi tare da cewa.
"Na zata zaki fi kowa farin ciki, dan zaki tafi gidan Muhid, Sai gashi kina zubda kwallarki masu daraja! Fatimah gaya min baƙi son auren ne? Idan baki so yau za a raba auren, dan nayi alqawarin bazan tab'a barinki, ki zubda kwalla ba."

Ciro kaina nayi cikin kuka nace.
"Baabi! Tsoro nake ji, tsoron kar wani abu ya faru."

Riko hannuna yayi sannan yace min.
"Kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru sai Ikon Allah, Insha Allah bazan tab'a barin ki, kiyi kuka ba, maza shirya an jima zasu zo su tafi dake! Khatoon ki taimake ni naji a raina na sauke nauyin da Allah ya daura min ne. Don Allah ki rike mijin ki da kima, yin amfani da hakan zai sani jin na cika Burin Fareeda."

Gyada kai nayi cikin zubda kwalla nace.
"Insha Allah Baabina!"
. Bai fita a dakin ba sai da yaga na shiga ban daki nayi alola sannan ya fita, yacewa Ummi.
"Ku lallabata."
Chapter 3 · 0% Book details