Sashe 37
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
  Bayan kamar minti biyar, sai ga kiran shi.
Sai ga kiran shi, ya shigo min tare da cewa.
"Kamar ya baki san shi ba? Zai biki, ki gayawa yan sandan da suke gurin zasu taimaka miki da wani abu."
          Ban ce mishi kome ba, dan koda na juya ban ga mutumin ba, haka muka taso ina duba shi ban gan shi ba, har muka iso sokoto, kafin tashi na hango shi tsaye yana kallona, tsoro ne ya kuma kamani, garin na turawa Saif sako, ashe wai Jay na turawa.
     _Don Allah kayi wani abu kaji sace ni zasu yi gashi nan yana shirin tawowa inda nake don Allah kayi wani abu_
     Fita mutumin. Yayi nima na fita, koda na iso inda za a zo dauka na, kawai naji an watsa min abu a jikina, ina dubawa naga madara, dan haka na juya da sauri na nufi ban daki domin na goge jikina, ina shiga kaina a sunkuye, kamar ance na d'ago kawai naji an toshe min bakina da hancina, shaƙar hodar bilis nayi ban kuma sanin abin da ya faru ba.
    Sauke numfashi Asood yayi tare da sanya min nikkaf ya fito dani a hankali har inda suka ajiye motar su.
       ----
Yana aiki da laptop din shi ne ya ga sakona,kamar bazai bude ba kawai ya buÉ—e.
Sharewa yayi ya cigaba da abin da yake can yaji zuciyar shi tana girgiza, gwada kiran layin yayi. Ta katse, ya kuma kira ta katse.
    Saka smart watch din da yake hade da wayar hannnta yayi ya shiga ƙoƙarin gano ainiyin inda take, bai samu nasarar gano kome ba, amma wayar tana airport.
  Mik'ewa yayi a hankali ya shirya cikin kananun kaya, bakakke, sannan ya dauki duk wani abin da yake bukata, yana fitowa ya kira Najim.
"Duk abin da kake mu hadu yanzun nan zaka kai ni tashar jirgin sama"
  Fitowan yayi har falo ya sami Mamah bayan sun gaisa da Mamah yace mata.
"Bari na dan fita bazan jima ba Insha Allah."
       "Ubangiji ya tsare, ya kare ka da kariyar shi. Allah ya dawo da kai lafiya!"
"Amin Ya Allah! Nagode sosai Mamah na!" Daga haka ya fita. Ya sami Najim yana jiran shin. Koda ya shiga yayi ƙoƙarin tambayar shi inda za shi amma yayi banza da shi.
    Tun da suka fita yake tsaki yana ce Mishi ya tsaya yayi musaya shi ya dawo gurin zaman shi Najim yaki tare da cewa.
"Wa? Ni zaka kashe wallahi ban isa ba"
  Dan haka ya kara gudu sosai, kamar zasu tashi sama, Allah ne ya kai su airport yana zuwa dakyar aka sami jirgin da zai isa sokoto, sabida sun gama diban fasinja.
    Ji yaƙe kamar ya riga jirgin isa Sokoto, koda suka isa abin da ya fara shine kiran layinta da yake cikin airport din, haka ya isa ya samu suna, ana niman ta sabida kayanta da aka gani. Nan ya gaya musu abin ta tura mishi.
 Nan aka nimo yan sandan, tare da danginta, Baabi ne ya zo, bayan an mishi tambayoyi ya tabbatar da sunyi magana da ita.
   Kallon Jay yayi cikin nutsuwa yace mishi.
"Kai kace ta tura maka sako?!"Â Nuna mishi wayar yayi sannan ya ce.
"Ban san a akayi ba amma Tabbas ta turo min sakon, kuma wayar har yanzun a bude take."
     Nan aka kuma gwada kiran wayar tana karar, dan haka aka shiga tambayar mutane, wani ne yace yaga wucewar ta ban daki daga nan bai ga fitar ta ba, sai wani mutum rungume da wata mata me sanye da nikkaf.
       Shiru Jay yayi da a rikice ya shige ban dakin, wayarta ya shiga kira. Can yaji "ziiiimmm"
Yana dubawa yaga wayar ce a kasa, da sauri ya É—auka, tare da duba wayar akwai ki.
Goge fuskar wayar yayi bayan ya fito, ya tsaya yana gwada budewa.
     Duk taki buɗewa, dole ya haɗa da agogon hannun shi ya shiga niman yadda take cire key din wayar.
       Yana sakawa kuwa, wayar ta buɗe. A hankali ya shiga bin sakon wayar har idanun shi ya sauka akan sakon da Ikrama ya tura mata. Da cewa.
_Yadda Mahaifinki ya hanani aurenki haka nima sai na lalata miki roman ki_
Sai sakon Asood da ya tura mata,
_Kamar yadda kika ki amincewa da ni! Haka kina ji kina gani zan,,,, karasa abinda wancan jahilin yayi miki wato Jay_
    Kallon sakon yayi lokacin kusan daya suka turo mata, fitowa yayi ya sami Baabi ya ja shi gefe suka yi magana, sannan Jay na zuwa ya sallami yan sandan, da wani abu aka kashe maganar.
  Sannan ya dauki kayanta, suka nufi gida da Baabi, ya kalli Baabi kadan sannan yace mishi.
"Baabih, kasan me yasa nace kar yan sanda su shiga Maganar?!"
  Girgiza kai yayi yana jiran ta cewar Jay.
"Sabida darajarta! Sabida wnada zata aura, bai dace ace sunan ta yana b'aci ba, sabida faduwar kimarta. Idan aka bar abun a rufe babu wanda zai tab'a sani, sannan Insha Allah nan da awa goma zan dawo maka da ita, kaga maganar aure ba abin wasa bane.
        Dan haka Insha Allah zan dawo da ita!"
 ..... Har cikin gidan ya ajiye baabi, sannan ya cewa driven yazo ya raka shi, suna fita. Duk wani inda ake harkan banza sai da Jay yayi, kan shi ya kulle.
.a karon farko da yaji yana son Hikmi ya taya shi aiki. Ya kira shi ya gaya mishi.
    Sannan ya tura mishi sakon Number Asood da Ikrama, bayan wani lokaci ya turo mishi inda a suke tare da Asood a guri guda, har da tasiwerar gurin.
      Kamar mahaukaci haka ya finciki motar.
    ---
Lokacin da aka kaini inda suke, wurgani suka yi, sannan fita.
     Ruwa suka, watsa min me shegen sanyi, sannan Ikrama yazo ya tsaya a kaina, tsare da zuba min ido.
  Nan ya saka hannun shi, ya gaya min rigar jikina, dake har zuwa lokacin ban farka dai dai ba.
  Haka suka yi ta, tozartani ba tare da na san abin da ke faruwa ba.
        Har kusan karfe bakwai na dare, ina yashe a kasa, kafin Asood ya taso ya fara kokarin tsinka bra din jikina, lokacin na bude idanuna da suka min nauyi dakyar na had'iye yawun baki na nace mishi.
"Don Allah karka min abin da, zai wulakanta ni!"
        Haka nayi ta rokon su, ba iya shi ba hatta sauran abokan shi, dariya suke min.
    ---
Jay ya sami shigowa unguwar sai dai babu yadda zai yi ya shiga dan kofar gidan yan sanda ke tsaron shi, dan haka ya kira Baabi suka yi magana tare da niman ya bashi Number Habib, can kuwa aka turo mishi ya kira shi suka yi magana.
  Can ya kashe wayar, bayan kaman minti sha biyar, suka iso tare da Habib, suka samu shiga gidan, kai tsaye ya shiga bin inda Asood yake, sai da suka yi tafiya me nisa sannan suka shiga gidan, kallon Habib yayi sannan yace.
"Bana son a kama su! Kawai ka koma gefe kaga yadda aka fara dole na gyara musu zama."
  Gyada kai Habib yayi dan ya sha kirb'a a habbar shi.
   Wani katako ya cire, a jikin wata teburi, ya bi bayan Ikrama ya zabga mishi a gefen fuskar shi, haka ya fadi tim, ganin shi a kasa, yasa sauran suka fara niman hanyar gudu sabida hannun Jay rike yake da katako, ba ga kuma yan sanda a bakin kofar fita, ai kuwa dole suka koma, lokacin yana dukar Asood.
Matsalar su shine duk sun bugu ne da giya, haka yayi musu likis, idanun shi jajjur, sannan ya cire rigar jikin shi, ya mika min.
"Saka bamu da lokacin da zaki yi kuka, shi yasa ake cewa kuna saka Hijab gashi nan babu wani abin da zaki kare jikin ki. Da shi aikin banza kawai.
  Taya maza ba zasu dinga kawo miki Hari ba, dube ki fa. Sabida Allah? Ko kishin kan ki baki yi, balle kiyi kishin mutumin da yake shirin aurenki,
  Ban tab'a haduwa da mara amana irinki ba, dube ki fa."
   Yadda yake sauke min Bala'i sake baki nayi ina kallon shi..
"Jay Kana sona? Jay kishina kake fa?"
Wani irin kallo ya watsa min kafin ya juya zuwa dakunan da suke cikin gidan, ya samu wata daki ya ciro wata sabuwar rigar shadda yazo ya mika min na saka.
  Sannan ya dauki gyale na ya mika min na yafa, a sannu ya riko hannuna muka fara tafiya, ina kallon fuskar shi. Da take tamke.
    "Jayyy!" Na faɗa da karfi sakamakon, sukar wukar da Asood ya kai mishi, juyawa yayi ya kalle ni a sanyayye, kafin yace min.
"Rufe idanunki!"
 Jikina na rawa, idanuna yana tsiyayyar da hawaye, ya juya tare da sake ni, ya rike hannun Asood. Juya hannun yayi idanun shi jajjur.
     Sai da ya karya hannun sannan yace mishi.
"Kai Abokina ne? Ita kuma Fatimah mata tace! Ko ya wani yazo keta mata haddi sai inda karfina ya kare. Don Allah mu dakatar da wannan abin daga nan, bana son ya tab'a mutuncin gidajen mu."
  Daga haka ya sake hannun Asood, sannan ya shafa cikin shi yaji ba wani ciwo bane dan yanka ce a samar fatar shi.