← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 72

Sashe 66

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.. tun daga ranar kome na gidan ya zama wani iri, cikin dare Idan Jay ya kwanta ko a dakin wata, toh shi zai yi barci babu wani abu, amma daga Husnah har Munih basu iya barci, gwara Munih ana d'aga mata kafa, sabida cikin jikin ta. Amma Husnah saka yarta barci. Ita kuma a sakata a gaba har kusan asuba, Munih kuma kafaffunta ke matsewa ana ja, washi gari ta farka kafaffuna suna mata ciwo,

---
Bude idanu nayi cikin nutsuwa nagan ni kwance a wani daki, kome na ciki ja da ratsin ruwan gwal, a hankali na mike zan tashi, sai ga mata hudu suka zube a gabana tare da cewa.
"Ranki shi dad'e! Umarnin ki muke jira!"
"Ina ne nan?" Na tambayeta,
"Nan daular ki ce! Al'ummar ki suna jiran ki, ana bukatar zuwan ki."
...... Ban daki suka kai ni nayi wanka sannan na fito, a hankali suka gani na suka shiga ciro min wasu kayan sawa, ana ajiye min, ana kuma dauko wasu manyan dogayen riguna, kallon wata doguwar riga nayi sannan na nuna musu shi. Da sauri suka sauko turarruka zasu shafa min nace musu.
"Karku shafa min masu ƙarfin kamshi, ina bukatar marasa karfi sosai, wanda iya hancina zan ji."

"Ran ki shi dad'e an gama!" Haka suka gama shafa min, sannan suka saka min kayan, a gaban madubin naga yadda kirjina ya fito na kalle su nace musu.
" Ina bukatar mayafi! Sannan mijina fa?"
"Ranki shi dad'e! Za ayi yadda kike so! Batun Yarima Jalal! Ba a bukatar shi a masarautan nan, domin an sha gayyatar shi nan yana kin zuwa."

Ina gama saka kayan nace mata.
"Ina son mijina anan nace! Idan ba haka ba zan saka sare min ke!"
",Tuba nake sarauniya Aanih ba zan kuma ba" daga nan ta fita da sauri. Bayan kaman minti goma sai ga su tare da wata tsohuwa. Ta shigo kallon juna suka yi sannan tace mata.
Dukawa tayi ta gaishe ni, sannan tace min..
"Bazlah!"
"Na sani! Meke tafe dake dan zan shiga fadar ne!" Na faÉ—a kai tsaye,
"Ranki shi dad'e! Akan Yarima Jalal ne! Masarautan nan tayi mishi Shamaki da shigowar shi cikin ta, sabida ke ake bukata zamu iya mai dake gurin shi ba wai dukka ba. Dan muma al'ummar mu suna bukatar ki!"

Kura mata ido nayi sannan na rufe jikina. Muka tafi a hankali duk kofar da muka wuce sai masu tsaron kofar sun zube kasa. Wata ƙatuwar Fada muka isa. Inda ake ta muhawara tsakanin manyan Fadar..
"Taya zaku ce bil Adam ne zata mulke mu! Bayan bata da alaka na jini da masarautar Dafur? Idan an bawa Sarauniya ZIRYA damar zama sarauniya sabida ruwa biyu ke yawo a jikinta, Aanih Fatimah Khatoon kuma wacece ita? Bama bukatar bil Adam a cikin daular mu, domin zata iya zab'ar son zuciyarta sama da al'ummar ta. Idan kuma kuka dage sai ita Toh Tabbas zamu bukaci a sare mana kan Yarima Jalal! Shine Yarima na goma sha biyar dake bin bayan Aanih Fatimah Khatoon! Sarauniyar zubda jini! Yayi muku ko kuma me zaku ce!"

"Ba za a kashe Jalal ba! Amma kuma ni zan rike Aanih Fatimah Khatoon! Ziryana Burbasa Fairo..... Chaiiii 🤦🏽‍♀️�
10/23/20, 10:10 AM - Ummi Tandama: *_Banza ta kori wofi_*
"Itace zata ta rike abin da na kasa! Itace zata iya abin da banyi ba, dan haka kar naji wani yace bil Adam bazai iya ba, ina kuka kai rashin imani irin na d'an adam!? Ina kuka kai rashin tausayin irin ta d'an adam!....

Shiru Aanih tayi sannan ta cigaba da cewa.
"Zata iya! Tabbas zata iya! Nasan zata iya!." Tun tana fada da karfi har ta daina karshe na zuba a gurin ina kiran "Jay!!!" Kafin wani irin barci ya dauke ni.

"Bazlah ai sai ki maida ta, d'akinta." Sunkuyar da kai tayi cikin girmamawa tace.
"Ya shugabana ina niman Alfarmar ko za a maida ita gurin mijinta, inda yaso sai ayi ta bude mata idanu, amma ku duba Alamarin da idanun basira!"

... "Wannan maganar ki gaskiya ne, a maida da ta a dawo da bazirqa!" Gyad'a mishi kai tayi cikin girmamawa, sannan ta dafa goshina tayi wasu kalamai sai ga mu a cikin d'akina, a kan gado ta kwantar dani, sannan ta shafa cikina tana faÉ—in. Yana yin bai nuna akwai wani abu a tare da ita ba da zai tabbatar musu da ciki ne da ita..

A hankali take shafa kai na, sannan tace.
"Mun barki lafiya! Sarauniyar mu!" Daga nan suka b'ace baki abin su.

......... Farkawa Jay yayi ya ganni kwance, dan d'azun dake bazirqa ce, yayi juyin duniyar nan tazo ta kwanta, amma fir taki. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya shafi fuskana, tare da shigewa jikina yayi tare da gyara min kwanciya, a jikin shi. Bayan yayi fatali da rigar jikina.

Da asuba, muka farka kunna wutar gadon yayi tare da leka fuskana, ya duba agogon gefen gadon, huÉ—u da minti biyar. Shigewa yayi jikina sosai yana kallona, tare da kallon yadda nake yatsina fuska, a hankali yake bin ilahirin jikina, har ya kai na ture hannun shi. Tare da zuba mishi ido.

"Aanihhhhhhhh! Don Allah karki min horo da hakkina." Yadda ya kira suna ya sani jin wani irin. Shiru nayi tare da lumshe idanu na..
Ina jin shi yana kidar shi, har zuwa lokacin da ya samu nutsuwa dani, gumi nake zubawa. Sabida turmushe da yayi. Gyara min kwanciya yayi tare da shafa kaina, a sannu na mike tare da barin gadon nayi wanka da alola tsaf sannan na fito.
Kallona yayi tare da isowa gabana ya zuba min ido, kauda kaina nayi, na wuce na shiga niman kayana na saka, sannan na gabatar da sallar nafilla, shima yana fitowa ya nufi masalacin.

.........bai shigo ba sai karfe bakwai saura, yana zuwa bai ce min kome ba, yaja alluran da ya shigo dashi ya kalle ni ba tare da yace min kome ba, ya koma ta baya na zai min sai lokacin nace mishi.
"Karka fara dan bana so!"

Bai kula ni ba, ya min alluran. Sannan ya fita ya bar ni a gurin. Har dakin shi ya koma ya shirya, kafin ya dawo har barci yayi gaba dani, bai tsaya yayi feccewar shi. Sai gurin karfe biyu na rana ya dawo ya samu na farka, ina zauna akan abin sallah. Mika min kunun gyada yayi wanda ya amso min daga cikin gidan. A hankali na ke sha. Kallona yayi sannan yace min.

"Meye matsalar ki? Bana son shirun nan."
Kallon shi nayi na wasu lokuta, kafin na sunkuyar da kaina kasa.
"Jay! Kawai ina hango tarin banbancin dake tsakanin mu ne!"
"Kamar Ya?" Murmushi nayi me ciwo, sannan nace mishi.
"Kawai ina jin ba zan yi nisan kwana bane! Domin nasan dole zan rabu da kai. Akwai mutanen da suke son ganin bayan ka! Amma yanzun ba zasu iya ba.

Ban sani ba, amma ina da tabbacin, wani zai zo da tuhumar laifin, idan suka zo ka basu wannan."

Karba yayi yana kallona baki sake, sannan zai magana na d'aga mishi hannu.
"Mutanen da ake hukuntawa basu da laifi! Mai Baya cikin masarautar, sannan wanda yayi laifin yana cikin masarautan.

Ga wannan shima ka bawa Habu!"
Daga haka na ajiye kofin kunun, na zuba mishi ido.
"Jay! Duk abin da zaka yi ka tabbatar da gaskiyar, domin gaskiya bata karewa, amma karya tana karewa a duniya, don Allah karka.."

Tashi yayi tare da barin d'akin, jikin shi a sanyayye, yana son Aanih amma tsoron kar wani abu ya same ta shine burin shi, lumshe idanunshi yayi can ya kuma dawowa ya dame ni a kwance.

Karb'an kofin yayi ya kalle ni, ajiyar zuciya ya sauke, ganin yadda nake barci, ciro Alluran yayi ya min, sannan ya fita daga dakin.

Cikin barci na farka sabida ciwon ciki, a hankali na nemi tashi zaune na kasa sabida jikina yayi min nauyi, idan ban ƙaryata kaina ba, kamar abu ne ke zuba a jiki, ina cikin wannan tunanin sai gashi ya shigo ganin halin da nake ciki ya sa shi sauke ajiyar zuciya, sannan ya taimaka min bayan yayi min wani allura, ya taimaka min nayi wanka, sannan ya hadu min ruwan zafi nasha, sannan ya bani magani, sai da ya tabbatar nayi barci kafin ya fita.

Wanke kayan da ta bata yayi sannan ya dauki kayan cikin ta Yar karamar wando da dan kamfen ta ya zuba a wani baƙin leda ya haƙƙa rami ya jefa, sannan ya dawo cikin gida, ya gyara ko ina, yana aiki Zancen da suka yi da Baba Magaji na dawo mishi.
"Toh baba taya zamu kare lafiyarta da rayuwarta? Wallahi tausayi take bani!"
Girgiza mishi kai yayi sannan yace.
"Hanya daya! Kar ka bari ciki ya shiga jikinta, tunda suka fara bayyana ta sanadin zama a kujeran toh karshe idan suka fahimci zamu raba ta dasu, zasu shiga niman daukarta ko kuma su kashe mu baki daya."

"Ba dai har da ita ba?"
"Eh toh idan ta kama haka za su iya aikawa" jikin Shi ne yayi sanyi, dan haka yana barin masalacin, sai da yaje ya sayo alkura. Yayi mata nafarko, kuma bata tambaye shi ba.

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya cigaba da zama a d'akin ta, yana zaune yaji motsin mutum a saman yana lek'awa ya hango Munih yayi dan haka ya share ta, ya cigaba da zaman shi a d'akin..

---
Washi gari..

Da taimakon Husnah ya shirya, ya fita. Ina kwancen naga kamar ana shigowa da fita a saman kuma da gudu ake kome.
"Waye?!" Na daka tsawa, cak aka kuma daina, sannan nayi kwanciya na, ina kwance kawai na kuma jin wannan gudun, zanyi magana aka ce min.
"Kee ƙamar mara kunya! Yau..."

Kwala ihu aka yi, barci ne yayi gaba dani, bud'e idanuna nayi na ganni a zaune. Samar kujeran.
"Wayyo mun tuba!!"

"Ranki shi dad'e wannan shine gulab, ranki shi dad'e! Me zamu mishi?"

Kauda kai nayi nace.
"Ku Azabtar dashi mafi muni? Karku sassauta mishi, har sai ya fadi suwaye suka aiko shi."
Chapter 66 · 0% Book details