← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 72

Sashe 26

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                 Idan ka isa kabi layyin unguwar mu tukun sai na san kai na musamman ne! Har ila yau yarintar tana kwance cikin jini ku."

      Daga haka na wuce abi na, ban ma bin ta kan shi ba, sabida ba zan iya karar da wani abu bayan wanda idanuna suka gane min ba.

     .... Koda muka isa gida, Aunty Aina'uh taso fahimtar halin da nake ciki, amma naki bata fuska, dan na fahimci ita ke son b'allo min ruwa.

.......
    Ranar Laraba jirgin su Najim ya sauka a garin Lagos, cikin nutsuwa suke saukowa tare da jin dadi. Shaƙar iska yayi cikin nutsuwa sannan ya fesar yana me ɗauki ganin mahaifar shi.

         Kallon shi Najim yayi kafin yace mishi.
"Abba ya gaya min cewa, garin Lagos yana daga cikin garuruwa masu dinbun tarihin rayuwar ka, domin anan aka kafa soyayyar da ta samar da kai.

                Dan haka idan zamu dawo nayi kokarin ganin mun sauka ta nan, domin ka fara jin ƙarfin shigar masarautar daura"

           Tab'e baki yayi cikin ko in kula, kamar bai damu da yadda yake so garin ba, yanzun burin shi su isa garin daura yaga yadda mahaifar shi take. Wannan itace muradin zuciyar shi. Zaman minti goma suka yi sannan suka nufi wata jirgi da zata kwashi fasinjojin Abuja sannan ta ajiye su daga can su sami jirgin da zata dauke su zuwa daura.

                     Tunda suka taso kirjin shi yake bugawa, tun yana zaune har ya tashi zuwa ban dakin cikin jirgin. Bai yi kome ba ya kuma fitowa.

          Ya zauna, har suka iso abuja, anan suka sake samun wani jirgin zuwa katsina, kafin nan jikin shi ya jike jagwa da gumi.

      Karfe biyar da minti goma jirgin su ya sauka a garin Katsina, suna isa suka sami. Fahad.

   Cikin wani irin farin ciki idanun shi cike da kwalla ya rungume Jay, duk da ya manta fuskar shi, amma ya rike shi sosai.

          A hankali ya juya ga Najim yana cewa.
"Aminin Arziki Barka da hanya. Babban lauyan mu!"
.  Ya sake Jay ya rungume Najim, murmushi yayi sannan Najim yace mishi.
"Ni ba surukinka bane da bazaka gaishe ni da da'a ba?"

        "Banza Bakwai, ba zan gaida ka ba, mara mutunci. Jannart ce ko zaka mutum ka dawo sai an bani ita ko Saraki?"

      Murmushin yake Jay yayi tare da juya idanu,  motar Fahad suka shiga.

       Suka fara tafiya, suna hira sama sama,  tunda suka fara tafiya Najim ya fahimci ana bin bayan su, dan haka yacewa.
"Kai Uban Maganannu tsayar da motar nan"

Tsayawa Fahad yayi motar tazo ta wuce su da gudun tsiya, murmushi Najim yayi sannan yace.
"Kasan me zai faru? Mu koma gidan sarkin Katsina"

       "Malam Lauya!"
"Nace muyi abinda na gaya maka," ya faÉ—a da matukar muhimmanci.
"Toh"

Da sauri ya sake hannun da suke, sannan ya koma daya bangaren, tun kafin su bar layin gurin Najim ya kira wayar wani kafin su isa wata mota kirar toyota, tazo tare da wani saurayi.

  Canza motar suka yi sannan Najim ya mika mishi kudin da zai hau wata yana cewa..
"Mansoor karka shiga motar ka bar shi anan, sabida wani dalili.

      Wannan kuma zamu tafi da ita, dan haka ka kiyayye yan sanda zasu zo nan!"

   Daga haka suka koma cikin motar, Jay na kallon su, har suka fara tafiya Fahad yace.
"Najim! Kaina ya daure da sauya motar nan, sannan kuma kace a nima mana me bakin gilashi. Me yasa?"

            Banza yayi da shi yana wani aiki da yar na'urar computer din shi.
"Saboda banzan surutun ka, baka san ana bibiyar motar ka ba, banza kawai baka san kome ba sai yadda kudi yake shiga da yadda kudi yake fita."

     Shiru yayi can ya kira wani a waya, suka sake magana..sannan ya kashe wayar. Tare da cewa Fahad.
"Kashe wayar ka, wasu babin didigin layinka."

Da sauri ya kashe wayar dan Allah ya daura mishi masifar tsoro.

  ......
   Sunyi dogon tafiya kafin suka kuma haduwa da mutanen suna jiran motar su, koda suka wuce su.

    Najim ya kuma kiran abokin shi ta intanet, daga nan suka ci-gaba da tafiya, har suka haɗu da wata motar kirar sieena, anan suka tsaya tare da sauya motar baki daya, sanan suka bar wannan toyotan a gurin.

                 Suna shiga wannan motar Jay ya zuba mishi ido.
"Saraki wannan kallon naka damuna yake, don Allah tambaye ni kome zan gaya maka banda wannan irin kallon."

                 "Me ke faruwa?" Inji Jay,
Shiru yayi sannan yace.
"Wato abinda yake faru, duk shiri ne na dakatar da kai, karka shiga masarautan."

  Kura mishi ido yayi, sannan ya kuma mai da kan shi yana fad'in.
"Suwaye suke son ganin bayana?"

          "Akwai mutane da yawa, matsalar wasu ba a san fuskar su ba."

        "Toh taya aka yi na bar gida?" Ya kuma wurgawa Najim tambaya.
"Bamu sani ba"
Najim ya bashi amsa a takaice.
    A hankali suka shiga garin daura, tare da sauke ajiyar zuciya. Dukkan su uku suna fadin Alhamdulillahi!

          Tun kafin su isa fada Jay yake kallon garin, cikin wani irin yanayin farin ciki, ya kasa fahimtar halin da yake ciki har suka isa cikin Masarautar, wanda aka shagali.

      Tsigar jikin shi ne, ya mike sakamakon busar alkaki da kakaki da ake, tare da buga tambura.

                   A hankali yake sauka daga motar bakin shi dauke da addu'ar da Manzon Allah ya bada da zaran zaka shiga cikin jama'a.

           Kallon shi ake ana faɗin.
"Lafiya d'an sarki jikan sarki! Lafiya Sarakin Asali, taka lafiya me Shehun Borno me Sarkin Musulmi, Lalle maraba da namijin duniya! Murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya! Zauna lafiya d'an karamin su kuma Baban su! Lafiya Kanin Ummu Rumana Jikar Ummu Rumanah!  Takawar ka dodon su.

                    Barka da zuwa Magajin Izzah! Barka da zuwa Magajin masarauta! Barka da Zuwa Yayan Gimbiya Jannart Yayan Gimbiya Jannart, An gaida D'a ga Gimbiya Sarah! Takawar ka lafiya Barde namijin zaki.

                   Wuwuwu ina gwani ganawa ina maji kira ga nawa, Chau namijin Giwa."

        Duk sai yaji shi kamar bai cika mutum ba, a hankali yake takawa, yayinda Najim da Fahad suke taka mishi baya, dogarai suna rike da jakkuna shi, da gudu  tawo tana fadin.
"Yaya Jayyyyy!"

    Ba tare da ya ganeta ba, ya tsaya cak yana jin kiran yarinyar har cikin kwakwalwar shi, da gudu ta faɗa kan shi ya rungume ta. Fashewa tayi da kuka, tana son magana kuka yaci karfinta, sai nuna mishi hanya take tana son tayi magana takarda saboda kukan da take dakyar tace.
"Ni...ce ....Ja...nan... Kanwar ka da ka tafi ka bari, Ga Raihanah can ga Kuma Ummu can muna kewar ka"

     Rungume ta ya kuma yi yana fadin.
"Ba zan yafe masu ba! Ba zan tab'a barin hakkin hawayen ki ba..gani nan na dawo Noorie!"

      Cikin wani irin murna tare da ihu tace.
"Ya ce min Noorie."

     Aikuwa take masu shela suka fara kara bisa suna fadin cewa.
"Saraki ya kuma kiran Gimbiya Jannart da Noorie haka ya sata farin ciki."

Aikuwa dake ana son karawa magauta haushi aka shiga sake ganguna, jan shi tayi har babban falon tsohon sarki Jalaludeen.

Tare yake da yaran shi tare da jikokin shi, ga kuma Aminan shi, a hankali ya shiga dakin tare da sallama, ya tsaya zai cire takalmin shi.
        "Barka da Zuwa Amale!"

         D'ago kan shi yayi cikin nutsuwa ya kalle ta, murmushi yayi tare da zubar hawayen, sannan ya cire takalmin ya isa gaban Jaamal ya zuba gwiwar shi a kasa, tare da sake wata irin kuka.

Wanda ya kuma saka kowa a falon kuka, sunkuyar da kai Jaamal yayi tare da tuno Jannart din shi, shekaru Ashirin da bakwai.

                  Rungume shi yayi tare da ce mishi.
"Ban san yaushe mutumin nan ya koyi kuka ba, dan a sanina baya kuka sai dai ajiyar zuciya."

                    Murmushi tsohon sarki yayi sannan yace.
" Idan gora tana rawa ba a cika  bane, dan haka ban ga jarumi a gabana ba Ragon mata na gani, wanda mace ta sanya shi biyota."

        Janye jikin shi yayi daga na Kawu, sannan ya share kwalla da take fuskar shi, ya sake murmushi. Yana shafa kan shi. Tare da kallon kakan shi ya matsa kusa da shi, ya zauna ya kasa magana sai shafa yalwatattacen gashin kanshi yaƙe cikin wani irin farin ciki mara iyaka.

         "Yanzun ina Iyayenka na can?" Kakan shi ya tambaye shi.
Kallon Jama'ar dake falon yayi sannan ya sunkuyar da kan shi kasa.

     "Nayi rashin adalci, har na dawo basu tsaya nayi sallama dasu ba." Ya faɗa a sanyayye,

                 Share batun kakan shi yayi sannan ya kuma mai da hankali gurin tambayar shi.
"Me ka karanta?"

   Murmushi yayi sannan ya shafa kan shi yace.
"Likitan mata da yara ne Ni!"

             "Matakin digiri ko ka kara gaba?"
Gyara zama yayi sannan yace.
"Zuwa mataki na biyu na digiri."
Chapter 26 · 0% Book details