Sashe 21
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
     Saukar da idanun ta tayi kan k'uguna shi, tare da d'ago kai.
     Amsar madarar yayi tare da ajiyewa a saman mirror din shi. Sannan ya juya mata baya tare da goge jikin shi. Ya jima sosai yana gyara jikin shi kuma tana d'akin.
  Yasan tana kallon shi dan yana jin haka a jikin shi.
Bai gama ida tunanin shi ba, sai jin hannun ta tayi tana me rungumo shi ta baya, rintsa idanun shi yayi tare da janye ta daga jikin shi, ya nuna mata hanyar fita.
         Ba musu ta fita tana murmushi, tun da ya zauna a bakin gadon, yake kuma jinjina qarfin hakurin Aanih! Yarinyar tasan darajar kimanta ta kuma san hujjar da zata kawo maka dan ta kare kanta, duk da tana ganiyar matantakar ta.
      Amma ba tab'a d'aga kai ta kalle shi da wata manufa ba, asalima idan ta ga yana saka kaya juya mishi baya take.
    Fatimah tana da mugun kunya da kawaici, amma soyayya ta sata bude baki ta gaya mishi sirrin zuciyarta.
   Bayan ya gama saka kayan shi ya dauki madarar ya sha, sannan ya tattara kome na d'akin ya gyara sabida Allah yayi shi mutum me mugun tsafta, baya son kazamta ko na miskala zarratin.
    Yana gama sha ya kwanta, abin shi a d'akin.
Bude kofar d'akin aka yi, ya d'ago kan shi, ya zuba mata ido.
 Juya mata baya yayi dan bai shirya tambayar su, abinda suka adana mishi ba.
     A hankali ta shigo, tare da zama a gefen gadon, tana kallon shi.
"Jaheed! Meke faruwa ne?!"
Rintsa idanun yayi kamar zai nutse cikin matashin ya furta da huci me zafi! Sannan yace.
"Babu!"
"Jay! Nasan kan! Na kuma san halin ka! Me zaka iya boye min bayan naga dimauta a kwaryar idanun ka! Bayan naga tarin tashin hankalin da suke cikin idanun ka. Ba a b'oyewa uwa ko uba tashin hankali."
    Tashi yayi zaune ya kura mata ido, idanun shi suna kyalin kwallar da suke cike fam da ruwan hawaye. A hankali ya bude bakin shi zai magana sai kuma ya fasa tare da mik'ewa ya shiga daukar yar falmarar rigar shi!(Jacket top)
  Sannan ya dauki takalmin shi na sawu ciki. Ya juya tare da barin d'akin.
"Jay!"
   Cak ya tsaya yana jin hawaye na sauka akan fuskar shi, ya d'an juyar da kan shi kad'an yana me d'an wai-waiye kad'an, dafa kafadar shi tayi ya sashi jin wani irin b'acin rai.
"Shin ban cancanci jin meke damun D'an nawa bane?!" Ta faÉ—a a sanyayye.
"Kiyi hakuri!" Daga haka ya saka kai ya fice daga gidan ma baki daya, yana zuwa inda ya ajiye motar shi ya sami Munih a cikin motar tana kallon shi.
 Shiga yayi tare da kwantar da kan shi.
   "Ina zamu je namijin Zaki!"
Kwantar da kan shi yayi tare da lumshe idanunshi, ya d'aga mata yatsun shi biyu.
    Sosai take jan motar bata tsaya ba, sai gidan Asood! Wanda yake Alberta town south.
     Wata irin kasala yake ji, tare da tsintar kan shi cikin wata irin buƙatar mace wanda bai tsammaci haka ba,. Buɗe ido yayi cikin nutsuwa yaga ta koma Mishi Aanih.
   Hannun shi ya kai kan cinyarta tare da matsawa, a cikin wata irin bugawa zuciya.
      Murmushi Munih tayi tare da bin shi da wata yaudararriyar murmushi. Fita tayi ya biyo ta, har zuwa cikin gidan.
   Tunda ya shiga, suka zube a falon, sam bai jin ya aikata abinda zuciyarshi take muradi! Amma halin da yake ciki ya wajaba akan shi ya sauke ajiyar da take jinin shi.
 .....matse cibiyar shi yayi zuwa marar shi, ya zuba mata ido.
"Jayyyyy! Ina sonka!"
   Lumshe idanunshi ya kuma yi a karo na ba adadi. Ya sauke wata irin ajiyar zuciya.
     Mika mata hannu yayi tare da b'alle rigar jikin ta, ya rungume ta.
   Jin wani irin yanayi yake kamar ba zai. Amma yana ƙoƙarin ganin ketare iyakar shi, kamar wanda aka watsawa wani abu, ya fara wani irin barci. Me dauke da mafarkai.
          Yau ma ri ke da hannu. Shi take har bakin kofar da kullum sai an bude mishi haske yake hana shi ganin mutanen cikin su. A hankali aka bude kofar yana me addu'ar Allah ya bashi sa'ar kallon meke cikin gurin, kawai yaji an rufe kofar tare da cewa.
"Babu wani magajin Izzah sai Zulum! Doly na cigaba da mulkina ko na sake aikata abinda zai zame muku mafarin bala'i."
     Kamar giftawa sai tsintar kanshi yayi a wata masarautar na daban wanda shi kan shi ba zai iya cewa ga abinda yake gani ba, zuɓewa suka yi a gaban shi tare da bashi hanya matar tana rike da hannun shi har bisa wata kataga da akayi ta da d'anyen azurfa, sai kambu da aka sanya mishi. Akan shi wanda ya haifar mishi da wata irin yanayi na musamman, bude idanun shi yayi ya kafe shi akan ta, sanye cikin kaya me launin ruwan ja, kanta sanye da wata irin kambu duk inda ta wuce sai ka ga mutanen sun zube akasa rigar jikinta ja ne.
  ....kuma yana haifar da jini sabida jikewar shi, tana nisa gaban shi ta kalle shi tare da zare siririn jar igiyar da take gaban rigar ta. Taja rigar ta zube daga jikinta kyakyawan surar jikinta me cike da kyau da kuma haiba.
    Suka bayyana mishi.
"Jalaludeen! Karka kuskura ka amince da shi ba Ziryana bane Zulum ne!"
       Juyawa yayi tare da lek'awa yana kallon su, a daidai lokacin da ta dauki hannun shi ta sanya a k'ugunta, kallon fuskar ta yayi, tana murmushi tace mishi..
"Jayyyyy! Baka yarda Aanihn ka bace?!"
       A hankali ya shafa k'ugun shi, jin wani abu yayi tare da fidda shi, kafin ta fahimci kudirin shi, tuni ya soka mata sai da ya biyo ta bayan ta, daidai shigowar wasu wanda ba zai iya cewa gasu waye ba, kawai sai ganin yayi Fatimah ta yanki jiki zata zub'e ya riketa a kirjin shi, gefen shi kuwa matar nan ce ta fashe da Dariya bayan ta rikid'e zuwa wani baƙin bamaguje tare da girgiza jiki ya b'ace yana faɗin.
   "Indai zaka iya kashe Macen da kake so tabbas Ni d'aya zan cigaba da mulki tare da...."
       "Jayyyyy! Dole kai.... Har olau baka kaunata?!" Tayi mishi tambayar hancinta yana zubda jini, haka ma gefen bakinta yana zubda jini.
     "Rayuwata! Farin cikina! Sadaukarwa ce a gare ki, Aanih kar ki manta i...."
A firgice ya farka daga mafarki da yake, tsintar Munih ba yayi a kirjin shi tana wani irin barci me cike da nutsuwa tare da jin dadi, d'agota yayi tare da ganin babu kome a jikin shi, daga shi har ita.
  Mamaki ce ta kama shi ya daki kanshi tare da tir da abinda ya faru.
    Hankad'e ta yayi cikin tashin hankali ya dira daga gadon, yana tangaɗi har ya shiga ban daki, ruwa ya sakarwa kan shi tare da sake kuka.. sabida ganin yadda tsinci kan shi cikin mummunan yanayin.
     A gurguje yayi wanka tare da tsame jikin shi ya fito,ko inda take bai kalla ba, ya shirya tsaf sannan ya nufi waje ɗaukar wayar shi tare da mukulin motar shi yayi ya fito a sanɗa kamar wanda yayi wani mugun abu, yaba gudun kar asirin shi ya tonu.
"Jay!!! Ina zaka tafi ka barni cikin wannan yanayin! Bayan ka lalata min rayuwa ta! Shine zaka gudu kabar ni!"
Ta karshe maganar cikin Kuka, me mugun tasiri a zuciyar wanda ya saurara, cak ya tsaya tare da juyawa yana kallon yadda jikinta yake rawa, hatta halittar jikinta girgiza yake.
Cikin matuƙar bakin ciki da nadamar rayuwa, zuwa yayi gabanta ya tsaya tare da taimaka mata ta saka kayanta, ganin yadda jikinta ya b'aci da jini ya sanya shi zaro manyan dara-daran idanun shi akanta, yana kallon fuskarta! Jikin shi kamar wanda aka jona mishi lantar ki haka yake rawa.
"Munubiya! Gaya min me ya faru? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji wani laifi nayi haka. Ka jarabce ni da zina! Ya Allah na tuba ka yafe min!"
Rungume ta yayi hawaye na zuba daga idanun shi, yana d'aga a bayan ta, ya kuma k'amk'ame ta, sabida bai zaci haka ba.
"Shi kenan! Ya Jay, ka raba ni da abinda ko wacce mace take takama da shi! Wani namijin ne zai yarda banin aikata ba, ka rabani da wanda zai zame min abokin rayuwata! Ya Jay nasan ba aurena zaka yi ba! Me yasa kayi min haka? Me yasa na cancanci haka daga gare ka! Meye laifin kaunar da nayi maka.
Nagode zaka iya tafiya, nima zan iya tafiya. Tunda ka iya tafiya Nigeria da baka da kowa kabi wata mace ai ba damuwa me zaka yi da ni!"
Ta faÉ—a cikin wani irin kuka, tare da kifa kanta a kirjin shi, shafa bayan ta yayi, sannan ya fara da cewa!
"Inji waye yace bazan iya aurenki ba? Kiyi hakuri! Insha Allah zan duba Alamarin amma muje asibiti!"
"A'ah ba zan iya zuwa ba, in kara tozarta kaina! Bazan kuma na wulakanta kima ta ba, kawai ka kai ni gida, ka mai dani gida." A birkice tayi maganar ga baƙi ɗaya ya gigita mishi hankali, ga kukan da take, kasa motsawa yayi yana kallon abin da yafi karfin tunanin shi. Shi ba abin yayi ta kuka ba, sai na bakin ciki.