← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 72

Sashe 12

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Cikin tashin hankali da tararradi ya fara magana.
" Don Allah na roke ku karku mata kome, naji nayi laifi"
"Wayyo Allah na! Jayyyyy! Kazo zasu tafi dani."
Na fada ina ihu, yana son ya tawo, nan kuma wasu sun rike shi, kamar mahaukaci haka yake musu ihu.
"Karku tab'a min mata ta, ku barta nace baku ji ne!"

                     Suna kai ni, Gurin shugaban su suka watsar dani, rigar jikina na sanyi suka cire min da karfin tsiya, sannan uku suka danne ni, shugaban ya shiga ƙoƙarin yaga min wandon jikina.

   Kuka nake tare da rokon su, amma ina har sun zare wandon.
"Jayyy! Don Allah zo karka basu su min haka."
  
   Ina kallon mutumin ya cire wandon shi, tare da min rumfa da kirjin shi, ban san lokacin da kuka me ciwo ya kwace min ba, dan hankalin shi baki daya, suna kan kirjina ne.

                  Hannun shi ya kai, da niyyar tab'awa, sai ganin shi muka yi yana aman jini, cikin tsoro sauran suka sake ni, tare da niman arcewa da gudu.sai ganin su muka yi suna faduwa a mace.

Da sauri Ya karaso tare da cire rigar shi ya mika min, yana kauda kan shi, ina sakawa.

Ya mika min hannu na tashi, sai kallon yadda mutanen suke faduwa muke, a tsora ce na koma bayan shi na boya tare da boye fuskana, a bayan shi.

                      Hannuna daya a samar kafad'arshi, cikin tsoro.

   Sai a  lokacin muka fahimci guguwar da ta cire guri guda take, tare a guri ɗaya tana tashi sama.
"Jay!"
    Ashe addu'o'in yake, kallon bakin shi nake, tsabar yadda addu'ar take fita. Da wani irin gudu guguwar tayo kan shi, na rike rigar shi tare da kwala ihu,  watsewa guguwar tayi,  a bayana naji an tab'a ni. Cikin wani irin tsoro na juya.

  Wata mace na gani cikin jajjayen kaya, tana fidda hayaki a kanta da idanunta.

"Dole kema ki d'andani abinda taji! Dole ki biyo ni, dole ki buÉ—e idanunki dole ki sadaukar da Rayuwar ki domin na shi, dole ki taya mu yaki! Tun daga farko kuka shiga zanen kaddarar juna! Babu yadda zaki yi ki fice a nashi haka zalika shima bazai fice a naki ki, dole a karasa bashin da ba kune kuka ci ba."

   Kasa motsi nayi, naga ta juya tare da zama hayaki ta baje.
             Ba zance na kuma fahimtar wani abu ba, amma tabbas na bude idanuna na ganni kwance a wani daki,. hannuna daya dauke da karin jini.

Mik'ewa nayi zan zauna, aka ce min.
"Koma ki kwanta."

  Wata mata ce, cikin shigar wata irin Wutar rissa, bakin shi. Kallon na jikina naga nima an sauya min kayana, daga riga da wandon jikina, zuwa wata duguwar riga, wacce suke kiranta da Bougaje.

        Fita matar tayi, can sai ga tare da wasu maza biyu.

"Innaih sannu da ƙoƙari, har ta falka? Sannu ya kumarin jikin naki?"

        Lumshe idanuna nayi sannan nace musu "da sauki."

   Ina rufe baki jini na saukowa daga hancina.

      "Ina Mujaheed din yake?! Halo dai Jinin yana zuba, kuma bamu san meke haifar da zubar jinin ba, dole a san abin yi." Suna cikin maganar ya shigo.

   Fita suka yi, can ya kuma dawowa da wasu malaman jinya aka zo, suka fita dani.

   Lokacin jini ke fita daga hancina, haka idan nayi tari jinin xan fitar abinda ya d'aga musu hankali kenan, baki daya. Suka rasa yadda zasu yi dani.

     Haka yayi ta bincike ko zai samu matsalar da nake fama dashi, amma bai yi dace ba.

           Karshe bayan an dawo dani dakin da nake. Suka mikar dani. Zasu mai dani gadon kawai na yanki jiki na fadi.

    Sai da aka kira shi, yazo lokacin ga baki daya na suma.

    Rayuwata ta zame mishi tashin  hankali, domin zubda jinin da nake ba na wasa bane. Shi kan sa ya fara dana sanin dauko ni da yayi.

       Sai da suka hada da rokon Allah da addu'a, na farka ban kuma jin wani ciwo ba, sai na masifar jin Jay! Wani irin abu nake ji shi  kamar zuciya ta, zata fito daga kirjina.

       Ban san lokacin da na shiga wannan halin ba, sai dai na wayi gari.ina ji a raina zan iya rasa rayuwata akan Jay.

.......
Na ji sauki sosai, har an sallame ni. Dan wulakancin amadadin ya kaini inda zan zauna cikin gidan su. Sai ya kai ni can bayan gidan su.gurin masu aikin gidan.

    Kuma ya saka aka bani dakin da bai da maraba da matattarar dabbobi, kullum da safe ni ke kwashe kazamtar su,bayan na basu abinci. Tun ban saba ba, har ta kai na saba dasu.

    ...raƙumai ne suke kiwon su abakin Innaih naji labarin ai kusan rabin su na Baban shi ne! Murmushi nayi kawai, ina jin dadin idan yazo kwashe su zai tafi kiwo. Burge ni yake, domin yana saka wata shudin mayafi tare da rufe fuskar shi.

   Yau ma ina cikin basu abinci,  na zubawa wata Rakuma mace ido, tana ta nishi.

      Wai ashe haihuwa zata yi, kawai naji Innaih tace min.
"Fadima! Kira min Mujaheed, yazo Rakumar nan haihuwa zata yi, maza yazo ya san abinyi."

          Da sauri na fita sanye da kayan bougaje, bayan na rufe fuskana da wani baƙin mayafi, haka kawai yasani na dinga rufe fuskana dan cin mutumci,
      Wai yake gaya min.
"Ke fa bawani fasali ne da ke ba, domin tsayinki yayi yawa sai kace sallar dare, gashi kin cika yanayi da aljanu.

         Idan na takura kaina da kallon ki, sai naji kamar na boye kaina dan sak kike da aljanu, don haka daga yau kar na kuma ganinki babu mayafi in ba haka ba zan iya yin komai. Musamman abinda zai samar min da nutsuwa ta. Shi zan aikata."

Tun daga wannan ranar na daina, wannan gangancin. Daga nesa na hango shi....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:51 AM - Ummi Tandama: https://my.w.tt/W07hVCuVdab
MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

GOMA
Last free page
Ki gaya min meye nayi miki haka da zafi?" Ya faÉ—a tare da dukar motar, kamar zai fasa hannun shi.
      A tsora ce k'ame jikina ina sake wata irin kuka me mugun cin rai.
"Cire min kayan jikinki nan?!"
A razane na kafe shi da ido, jikina yana wani irin rawa, ban san lokacin dana zube akan gwiwata ba, tare da matse jikina a guri guda, ina keerrma.
"Don Allah ka rufa min asiri! Mu ahalin gidan sarauta an samu da kamewa, sabida kimarmu itace shaidar tarbiyyan mu. Ba iya ahalin masarautar ba, duk macen da tasan kimarta! Dole ta kare shi don Allah ka rufa min asiri." Na fada cikin kuka,

"Cire kayan nace ko na cire nayi abinda na gadama dake!"

"Wallahi bazan cire ba, kawai ka bi takai na da motar ka, zai fi min kwanciyar hankali da ace na cire."

   Lallai Jay mahaukaci ne! Ko nace d'an mahaukaciya, ba tare da jin ko Dar ba, ya tawo ya shiga yaga sauran kayan jikina.

   Wani irin bakin ciki ne, ya sani kasa kuka. Ina girmama rashin mutunci irin na Jay, sai da babu wata kaya a jikina, sannan ya nuna min motar ya shige yana kallon agogon hannun shi.

  Kamar na had'iye zuciyata dan bakin ciki.
"Ina da abin yi!"

..kauda kan shi yayi, sabida yaga na kasa tashi, a hankali na isa jikin kofar baya na bude tare da shiga cikin motar.
"Nice zan zama driven ki?!"

     A hankali na fito tare da kare kirjina, na shiga gaban motar, ina kuka. Da wani mugun gudu ya finciki motar daga ni sai yar buje tare da shimin da na saka, babu yar rigar mama a cikin jikina

  Sai kare jikina nake ina, kuka munyi doguwar tafiya kafin, ya taka birki sai da na tafi kamar zan hantsila.
"Na rantse kika dame ni da kuka zan zane ki!"

   Cike da mamaki na ciro kai na, ina mishi kallon.
"Ka zane ni fa? Ai ni ba Yarka bace."

   "Ficce min a mota!"ya daka min tsawa, wani irin rawa jikina ya ɗauka, na fara bashi hakuri.
"Don Allah kayi hakuri bazan kuma maka magana ba."

      Sake sake motar yayi a guje, kamar  zai tashi sama, gashi tsabar mugunta ya.kure karfin sanyin motar, sai rawan sanyi nake.

    "Don Allah ko zaka rage karfin sanyin nan ne?!" Banza yayi dani, sai ma kure karfin da yayi. Atishawa nayi ta sakewa tare da jin wani irin sanyi yana shugaba kamar zanyi hauka, da wutsiyar ido yake kallona, tare da tauna bakin shi, sai da muka yi tafiyar awa biyu, sannan ya tsaya. Ya fita zuwa bayan motar. Ya ciro min wata ƙatuwar rigar sanyi tare da wandon shi gajere zuwa kwanji. Sai wata yar karamar riga.
Ajiye min yayi tare da tadda motar dan wulakancin yace min.
"Ina sauri ki fita ko saka kayan suna bayan.. idan kika b'ata min lokaci sai na tafi na barki."

     Kallon wajen nayi na kuma duba a gogon motar shi, ban san lokacin da kwalla ya cika min ido ba, karfe biyu na dare.

"Don Allah ko zaka, fita na saka a cikin motar."
Chapter 12 · 0% Book details