← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 72

Sashe 14

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    "Toh ka mai dani inda ka dauko ni mana! Tunda baka son ganin ina zuwa inda kake."

                   Take min kafana yayi, na d'ago kaina ina kallon shi, cikin kuka nace.
"Allah sai ya saka min."

    Baki na ne ya furta hakan, amma zuciyata sam bata aminta da hakan ba.

           Jay bai bar inda nake ba, sai da ya sani kuka sosai. Sannan yayi tafiyar shi.

                Innaih ce tayi ta bani hakuri, tare da gaya min bafa halin shi bane, kawai yana min haka ne dan laifin da nayi mishi.
.karfe sha biyu saura. Ina kwancen ya shigo inda nake, kunna wutar dakin yayi ya ganni zaune ina ƙoƙarin b'oye  tsimar da nake goge hancina.

       Takowa yayi cikin nutsuwa, ya saka hannu ya ciro tsimar, yaga yadda ya jike da jini.
"Aanih! Meke damunki?!"
.kallon renin hankali nayi mishi, sannan nace mishi.
"Jin dadi!"
Daga haka nayi shiru, tare da kwanciya na juya mishi baya.
"Tashi ki rakani!"

"Babu inda zani a wannan tsohon daren"
"Toh ina saka miki kayan"

Zubur na mike tare da amsar bakaken kayan na saka, ina mishi kallon tuhuma.
"Da alamu ka fara fashi da makami ko?!"
Tab'e baki yayi, sannan ya bar d'akin. Na saka riga da wandon sai yar karamar hijab.

  Sannan na fito, a hankali babu kowa a tsakar gidan.
"Shiiiiii! Naji kamar ana jan abu, juyawa nayi cike da tsoro, na hango matar ranar, sanye da doguwar rigar yana jan kasa, ya jike sosai da jini. Tafiya take ina bin bayanta,  dafa ni akayi na sake wata irin ajiyar zuciya tare da sake kara.

"Ke dalla tafi can!"
Ya gaya min,  riko hannuna yayi tare da fitar dani a gidan, har gurin motar shi muka isa, sannan ya sake hannuna ya koma mazaunin shi na shiga motar.

   Tunda ya fara tuki bamu tsaya a ko ina ba, sai a wani can gidan rawa,(club)  tunda muka shiga nake jin warin giya. Da wiwi.

        Kallon mutanen gurin nayi, sunata bad'alar su, can gefe na nima na zauna. Tunda ya shigo ake ihun zuwan shi.

     Sai gaishe shi ake, ga yan mata sai rungume shi suke.

     Da alamu ba bakon gurin bane, sannan kuma zan iya cewa duk inda yake sai ka samu ana girmama shi.

                   Ina zaune maza keta kawo min hari, ban kula su ba.
"Manyan a ina ka samu iri me kyau haka? Gaskiya ta haÉ—u."

       Bai magana ba, haka suka yi ta magana, yana jin su. Mik'ewa daya daga cikin su yayi zai zo inda nake ya rike mishi hannu.
"Karka fara!"
     Komawa yayi ya zauna,
"Toh wacece ita?!"
"Ita din kamila ce! Daga gaban iyayenta na daukota."

  Shiru yayi sannan ya mike, tare da mika musu hannu, sannan yazo inda nake ya riko hannuna muka fita, kallona yayi sannan yace.
"Me yasa kike daukar hankalin su?!"
Banza nayi dashi dan bani da amsar bashi, can yace.
"Ina magana kinyi banza dani ke wacece!"

            Dake kaina a sunkuye yake, yana tab'a ni ina dungurawa, abin ya dame shi.

   Yana kuma mamakin yadda nake wannan abin. Har dawo dani gidan, ya zagayo tare da saka hannun shi zai dauke ni, aikuwa sai ga hannun shi ya sauka a kirjina, cike da mamaki. Ya kalle yadda nake sume ga jinin nan yana d'iga daga hancina...  

.        Janye hannun shi yake son yi, amma shaidan na mishi huɗubar tsiya, kara tabawa yayi yaji yadda suke, wani irin yanayi yaji lokaci guda, d'ago fuska na. Yana kallon yadda zubda jini hanci da idanu.
.janye hannunsa yayi tare da kaini d'akina, yafita.

Tunda daga ranar, ban kuma ganin shi ba, shigar da yake yi ma, ya daina baya zuwa inda nake.

       Sosai na damu akan rashin ganin shi, ga wani irin yanayi da nake tsintar kaina, na tashin hankali.

......
Yau kwana bakwai kenan, ina kwance ya shigo min, hasken wayar shi ya dallara min, sannan ya coge a gefe..idanun shi a kaina.

    .."zaki raka ni!"

"Gaskiya indai gidan rawa ne bazani ba, sabida ba tarbiyyar gidan mu bane!"

   Takowa yayi gabana, cikin izza ya durkusa tare da haska fuskar mu yace.
"Kalli cikin idanuna! Nace zaki raka ni!"

        "Ni bazan."
Fincikoni yayi har jikin shi na rawa ya kura min ido, cikin jin haushi yace.
"Ki tashi kafin nayi.amfani da baiwar da Allah yayi min, na gyara miki zama!"

  ... Babu shiri na mike ya watsa min kayan ya ficce a d'akin, kuka ne ya kwace min.

  Sai da nayi ya ishe ni, sannan na saka kayan, doguwar riga ce har kasa, a hankali na fito daga dakin. Wannan karar da naji na ranar can.
"Shiiii!"
   Tsintar kaina nayi da bin inda kar'ar yake fitowa, kawai naji ya fincikoni. Tare da ja na,.muka fita.
    

                 Sai da ya jefa ni cikin motar, sannan ya dawo yaja mu, tun a hanyar nake aman jini. Kaina kamar zata yi bindiga, buga motar yayi bayan ya tsaya, cikin jin haushi yace.
"Duk abinda zaki yi, sai kin rakani party nan!"

         Babu yadda na iya haka muka nufi, inda suka shirya, shirmen su. Bana jin dadin shigar da nayi.

... Tunda muka shiga, abokan shi suka ja shi can gefe. Wani cikin su yazo ya takura min da surutu. Karshe da na gaji, na silale zan gudu. Ashe sun ga fita na daga dakin party wani daga cikin abokan shi yace mishi.
"Yarinyar da kuka zo ta fita fa! Kuma naga su Ghali sun bita."

   Mik'ewa yayi, yaji gabaki daya, bazai iya dogon tafiya ba, komawa yayi ya kwanta a kujeran. Tare da buga kanshi, yana faɗin.
"Yarinyar kamila ce! Ni ne na daukota domin daukar fansan abinda tayi min, taya zan su min haka."

Dakyar ya mike,  yana buga kanshi sannan ya fito. Can nesa yaji ihuna, da sauri ya shiga niman inda nake, nan kuwa kokuwa suke dani, daya na kokarin yaga min rigar jikina, daya kuma yana me rufe min bakina.

  .... Wani irin kuka ne ya kwace min, cikin tashin hankali na kwala mishi kira.
"Mujaheed!" Sake toshe min bakina suka yi, tare da kai ni kasa.
Allah ya bani Sa'a wanda ya rufe min bakina, na gantsara mishi cizo, sai da yayi ihu, a lokacin Jay ya iso, tare da zama a gaban su.
"Karku mata kome! Domin mata ta ce!"

.   Da mamaki suka zuba mishi ido, Ghali ya dauki wata sanda a gurin ya make mishi kai, tare da cigaba da dukar shi, sannan ya tura wanda na ciza, ya dauko musu ruwa.

      Zuba mishi ruwan suka yi, sannan suka mike tare da cewa.
"Karka kuma gigin kawota gidan casu, domin wallahi gobe zamu kuma farmata."

... Gyada musu kai yayi, suna tafiya na iso gurin shi da sauri, tare da kallon shi, dake abuge yake mika min hannu yayi da sauri na rarrafa jikin shi ina kuka sosai.
"Jay! Ka kai Ni gurin Baabina, bani da lafiya! Idan baka kai Ni ba wani abu zai same ni!"

       D'ago kaina yayi, giya tana gaya mishi wani abu na daban, kafin nayi wata yunkuri sai jin bakin shi nayi cikin nawa, duk yadda naso kwace kaina, na kasa.

           Hancina da kunne ne, suka fara zubda jini, kafin wani lokaci, idanuna sun rufe da jinin, saukar da bakin shi yayi wuyana, tare da Binta da wata zazzafar sumbata.
Sai ganin kaina yayi yana reto.

    Dakyar ya mike tare da lallubar makulin motar shi, ya kunna, sannan ya nufi motar tare da daukata, shi kanshi bai san inda zai kai ni ba.

    Tunda ya ajiye ni a cikin motar, ya nufi gida dani, dakyar ya isa konace Allah ya nufa muna da nisan kwana.

                Daukata yayi zuwa dakin da ya bada na zauna, ya kwantar dani, sannan ya fita. Dakin shi da yake da taga ta wajen d'akina, ya shiga. Ko cire kayan jikin shi bai yi ba, ya kwanta.

            ---
Washi gari! Koda ya farka, a hankali abinda ya faru daren jiya ya shiga dawo mishi.

   Ganin har yayi Sallah tare da wanka bai ji muryana ina wasa da Yar Jinjirin Rakumar nan ba, ya sanya shi fitowa. Har tsakar gidan.

        Gama kewaye tsakar gidan yayi kafin ya koma inda Innaih take aiki, yace.
"Innaih ina wancan Yarinyar?!"
   
Cike da mamaki take kallon shi, kafin ta maida kanta, izuwa aikin da take sannan tace.

"FaÉ—imah ba yarinya bace! Magajin Izzah, kawai jikinta ne da bai nuna alamar girma."

Tanke fuskar shi yayi cikin jin haushin abinda Innaih tace.
"Innaih! Tambayarki nayi ina take?!"
"Allah ya huci zuciyar ka! Barden Damagaram."

              Nuna mishi dakin tayi, cikin wani irin Izzah da jin kai, ya nufi dakin, daga shi sai 3 qrt. Ya iso bakin kofar.

      Yana turo kanshi sai da ya razana, sabida yadda gashin kaina yayi buzu-buzu, ga Idanuna da suke fidda jini.

            Mai da kaina nayi kasa ina gogewa.
"Dama baki da lafiya ne?!"
Banza dashi nayi, na cigaba da goge jinin.
"Ina miki magana kinyi banza dani.!"

   ...
"Don Allah ka kyale ni! Ka mai dani gurin Dangina, idan ba haka ba. Mutuwa zanyi."

Fita yayi daga dakin, ya nufi dakin shi. Ya shirya ya bar gidan,
Chapter 14 · 0% Book details