← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 72

Sashe 60

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........ Washi gari aka kuma hada min kome Baabi ya bani kuÉ—in wai kar na tambayi Jay, naji kewar su Sosai, kasa boye kuka na nayi SOSAI..
*Kuyi hakuri! Insha Allah mun kusan kammalawa!*
10/23/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: _Ansan da wuyar biri ake daure shi a k'ugu_

Tun da muka fito, daga gidan mu za a kai ni tashar jirgin, na fahimci ana bin mu, lumshe idanuna nayi na kwantar da kaina, haka kawai naji wani abu yana haurowa daga kafana zuwa kaina. Bude idanu nayi cikin wata irin murya nace.
"Barde! Tsaya." Kafin mu tsaya sun wuce mu da mugun gudu, "Bazlah, a kona motar da mutanen cikin su"  da sauri Barde ya juya yana kallona, ban d'ago na kalle shi ba nace mishi.

"Muje ko!"  Jiki na rawa ya tadda motar muka bar gurin, muna isa gaba kadan muka ga motar ta kama da wuta,.kauda kai nayi tare da mai da hankali na kan wayar hanuna na turawa Jay sakon abin da ya faru.
     *Wasu sun biyo ni! Amma nasaka an kona min su*
Kira na yayi na .kashe wayar baki daya domin idan bana hayacina bana son a min magana, sai dai Ni na yi maka. Muna isa tashar jirgin sama, Barde da yake tsorace dani ya kwashe min kayana zuwa cikin tashar, daga nan yayi komawan shi gida, tun a hanya ya manta da duk abin da ya faru.

                 .... Bayan jirgin mu ya tashi, naga wasu mutane suna kallona, sau daya na kalle su. Na kauda kaina, har muka iso katsina, na samu Najim yazo dauka na, mutanen nan suna biye damu, kallona daya nayi musu naga sun firgici, haka muka dauko hanyar katsina, suna kallona Najim yayi cikin damuwa yace min.
"Akwai matsala!"

"Kyale su! Zasu mutuwa zasu yi!" Kafin yayi min magana motar ta kwace musu, duk da idanuna a rufe suke sai da nace mishi.

"Ka yarda da abin da na gaya maka?"  Cikin wani irin azzaben tsoro yace min.
"Eh..eah e.h"
"Ka nutsu babu abin da za a maka! Duk wanda yake tare da sarauniyar mu yana cikin kariyar mu." Aka fada mishi haka dai dai kunnen shi. Kamar kan motar zata kwace a hannun shi nace mishi.

"Kiyashin gidan ku ba zan tab'a barin a cutar dashi ba balle kuma kai."

.... Mun iso daura lafiya, cikin nutsuwa, har kofar gidan ya kai ni na fita. Kallon gidan nayi nace mishi.
'"bari a gyara gidan domin akwai ƙura da Datti, zan karasa cikin gidan."

   Gyada kai yayi, sannan ya fito zai bude min kofar na hana shi na bude abuna. Na fita, cikin gida sun yi murnan dawowa ta, kowa yaji dad'in ganina, ni kuma ina kewar mijina, kamar yasan ina nan sai gashi nan, tashi nayi na nufi dakin Karama, sai gashi ya biyo ni yana shigowa na rufe kofar tare da rungumo shi ta baya, juyawa yayi yana kallona.
"Aanih Fatima Khatoon!"
"Na'am Jay dina." Juyo ni yayi yana kallon fuskana, yace.
"Nayi kewar ki!"
Dariya nayi sannan na rike hannun shi na saka a fuskana nace mishi.
"Nafi ka!"
"Anya kuwa? Dubi yadda kika kara kiba! Ni kuma fitinar mutane yana hanani sukuni!"

     "Sabida ka kasa tunkarar Galadima ko? Shine damuwar ka, ba kowa ba, ni bana jin kome, amma babu ruwanka akan abin da zan yi tunda kai ba zaka iya ba."
"A'a! Ke mace ce ba zaki iya dasu ba" kallon shi nayi a nutse, sannan na janye jikina. Zan bar dakin.
"Kace ni mace ce? Toh bari na nuna maka wani abu!"  Fitowa nayi dashi har shashin masu girkin su Mamah amintacciyar baiwar su, da take musu abinci ita na je na tsayawa, nace mata.
"Umma Hari! Bani ladan kisar da aka saki kika aikata?"

A razane ta juyo tana kallona zufa na karyo mata jikinta yana rawa, nace mata.
"Zan kyale ki idan kika gaya min suwaye suka saka ki, idan kuma ki ka ki. Tabbas zan sanya ayi ta zane ki har sai kin daina numfashi."

          Jikinta ne ya dauki rawa, ta mike a hankali hawaye na zuba mata, na kalle ta wani irin tausayi ta bani, saboda bana tunanin kwadayin ne yasata ta aikata haka sai dalili mai karfi.
"Me yasa kika yarda da aikin kisa?"
  Kanta a sunkuye ta zube a gabana ta kuma fashe da kuka, tana fadin.
"Bani da hanyar taimakawa yarinyar da nake rike da ita bata da lafiya, shine na sami Fulani Nanah na gaya mata, ita kuma ta bani aiki ita da Gimbiya Husnah."

                 Kallon Jay nayi wanda yake bayan mu can, naje na same shi, yana kallona nace mishi.
"Mutanen nan sun yi nisan da koda ka kama su baka da hujjar, koda bamu mata kome ba, ina tabbatar maka  gobe ba zata kai labari ba, domin ana bibiyarta, idan namu son faruwar wannan al'amarin dole mu tafi da ita cikin gidan mu."

  ..."ban fahimci abin da kike nufi ba?"
"Hamma Jay!" Karama ta kwala mishi. Da sauri ya juya gurinta kasa magana tayi tana nuna mishi hanya, juyawa nayi gurin Umma Hari, ta kuma sake wani irin kuka, tana me rokona tana faÉ—in.
"Ki cewa mijinki ya hakura da fada da Galadima, sabida taurin kan shi matar Uban shi matar da ta rene shi itace aka sani na zuba mata gub..." D'aga hannu nayi zan mare ta aka rike hannun.

"Ki godewa Allah da bata mutu ba, sannan gubar ba me tasiri bane, tana shan danyen madara zata amayar dashi, ban da haka."
A fusace na juya ga Mamah Nana, kallon ta nayi. Zan yi magana ta saka min hannu a baki.
"Ki bar ni na d"aga muryana, domin Tass nake na aikata kome. Da alamu kina son dan yaron mijinki, dan haka kiyi kaf kafa dashi kafin fushin mu ya ta'azara akan shi, ke kuma hari. Kamar yadda kika sake bakin ki, haka zaki karasa rayuwarki babu harshen magana."

"Karki kuskura ki mata wani abu dan zan iya sakawa a.."

"Ayi me? Toh bari naga idan kin ji labarin na tura mijinki da uwar goyan shi duniyar mutuwa ya zaki ji, kiyi maza ki dakatar dasu tafiya asibiti domin sunan shi gaw." Rike mata wuya nayi tare da jingina ta da bango.
"Duk wanda ya Kuskura ya taba min miji, sunan shi gawa kuma ki jira dawowa na."

Da sauri na bi hanya da zata kai ni, gurin Mama Sarah na samu ya bar gidan da sauri. Komawa cikin gidan nayi. Na kuma kowa waje da sauri. Kamar Mahaukaciya. Tsayawa nayi na takarkare na fashe da wani irin kuka, tare da zuɓewa a kan gwiwa ta, Bazlah ce ta bayyana da wasu da ban san su ba.
"Sarauniyar ki gaya mana me kike bukata."
D'ago jajjayen Idanuna nayi, wanda jini ya kwanta a cikin su.
"Husnah! Nanah, Galadima! " Ku kai min su baitul azab, karku rangwata musu, ku shayar dasu madarar azaba, ku horasu babu dare babu rana. Kuyi musu mafi munin azaba, wanda zasu Fahimci girman laifin su.

Idan ta kama ayi ta yanka namar jikin su, ana bawa dabbobi suna ce a aikata."

"Mun bi umarninki mun kuma tabbatar zamu aikata."

Daga nan wasu suka suka tashi zuwa cikin gidan, suka dauki Nanah da Husnah, can wasu suka dawo, tare da Galadima.

"Baki son su rayu ne? Ko baki son mahafinki da yan uwanki su rayu? Tunda kin zabi haka bari na tabbatar miki da abin da zan iya aikatawa. Ziryana ki hada hannu dani. Na amshi masarautan. Ni na cigaba daga inda na tsaya."

"Bakin Azzalumin ba zan tab'a baka wannan damar ba, zan saka a sake ka sabida Aanih amma ba zan kyale ka ba."

Daga nan na mike zan tafi, rike hannuna yayi ina juyawa na wanka mishi wani marin da sai da bakin shi ya fashe nace mishi.
"Kul!"
Daga nan na juya abuna.
"Ranki shi dad'e! Zaki iya rufe idanunki, yanzun haka Yariman da Mamar shi sun isa Asibitin kema idan kika rufe idanunki zamu kai ki can."

Gyada musu kai nayi tare da rufe idanuna.
"Mun iso!" A kofar shiga asibitin na ganni, sannan suka tsaya a gurin ba iya su ba, wasu ma dayawa suna. Nan a bakin kofar asibitin, har dakin da aka kwantar da Mama Sarah, a bakin kofar naga Jay a tsaya, a hankali na isa gare shi na kwantar da kaina abayan shi, na sake Mishi kuka a hankali nace mishi.
"Jay naji tsoron kar wani abu ya same ka." Janyo ni yayi sannan ya riko hannuna, yana faÉ—in..
"Babu abin da zai same ni facce Allah ya rubuta min a zanen kaddarata dan haka ki daina damun kanki Insha Allah kome zai zo da sauki."

Har likitan ya fito, yana kallon mu yace mana Jay yaje, ni kuma na shiga d'akin, na sameta hawaye na zuba daga gefen idanunta, rike hannunta nayi, ta bude ido a hankali ta zuba min su..sannan na tace min.
"Aanih kin zo kema? Aanih masarautan Akwai fitinannu dayawa, basu son gaskiya. Gashi nan suka son nasara mu.

Ina da yakinin zaki taya shi kafa gaskiya, don Allah."

..... "Mama irin wannan maganar kamar kina rokona ne, Ni kuma kunyar haka nake ji. Zan bawa Jay goyan baya har ya kafa adalci Insha Allah "

A hankali take gaya min, sakon Maman Jay, kallonta nayi da jajjayen Idanuna nace mata.
"Kiyi hakuri! Ba zamu rusa Ganuwar ba! Yin haka dai dai yake da zunubi domin akwai shugaban mu a gurin,.kuma kar mu kuma jin maganar rushe ganuwar nan,?"

Wani irin tsoro e ya kamata, daga haka na juya mata baya, kuka ya tawo min, ina gaya mata cewa.
"Zan iya miki kome amma bazan rushe ganuwar ba, domin akwai masu ibadar su a gurin, yin haka zunubi ce Babba."
.haka na fita na barta, har Jay ya shigo..
Chapter 60 · 0% Book details