← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 72

Sashe 58

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Kawo mishi abincin Husnah tayi, na zubda mata ido. Tana ajiyewa nace mishi.
"Baka kyauta mana! Kuma ka hana mu. Muyi Magana wallahi mu da kake cin mutuncin mu, mune bazamu tab'a cutar da kai ba.

        Idan nayi karya ka ce Husnah taci abincin da ta kawo, wani irin B'oyayyen firgici tayi wanda yayi masifar tasiri a idanun ta, sabida na gani sosai a idanunta.
"Me yasa kika ce haka?"
"Sabida na fahimci cewa laifin mu kake so gani a koda yaushe!"

      Kallon Husnah yayi cikin nutsuwa yana jiran me zata ce.
"Hamma! Ban tab'a jin a raina na cutar da kai ba, sai dai ban sani ba ko da nake girkin ta turo Zabba'u ta zuba min wani abu.

    Dan sau uku ina kamata tana yunkurin zuba min wani abu. Ban gaya maka bane, sabida gudun tozarci daga jinin sarauta, masu ƙarfin iko." Ya karshe maganar tana me kallon cikin idanuna.

Lumshe idanunshi yayi sannan ya zuba shi a kaina. Ban yi mamakin abin da tace ba.

     Domin fadar da suke ban ga hujjar yin shi ba, amma a haka suke yaki domin kare kansu.

"Baki ce kome ba?kin kura mana ido, ki kira Zabba'u." Sunkuyar da kai nayi sannan na juya na koma sama, na kira Zabba'u, tare muka sauko, Jay ya bukaci Husnah ta mai-maita abinda ya faÉ—a.

    Tana faɗa tana Zabba'u ta fashe da kuka, zata rantse na dakatar da ita, sannan nace mishi.
" Jalaludeen! Ana ciyar da kai guba! Kuma nayi magana ta juya laifin kan Zabba'u."

              "Hamma! Wallahi ka tambayi Munih, ita kanta Aanih tasha bata abu ta zuba min cikin abincin da nake dafa maka." Kallon mu yayi daga Ni har Zabba'u tare da Munih da take saukowa daga sama, rike da baƙinta.
         Rashin Maganar Munih shi ya sanya Jay ya amince da abin da Husnah ta fada.
"Daga yau kar na kuma ganin kafarki a kasa! Kuma kar na kuma ganin Munih taje gurinki, sannan bayin da aka kawo miki a  maida su bana son ganin su,  na kashe wannan maganar daga nan kar na kuma jin wani ya zo da batun."

            Juyawa nayi zan bar falon, yace min.
"Nace ki sallami mutanenki"
"Naji ranka shi dad'e!"

            Kwalla ne ya cika min ido, sannan na juya na bar gurin, ina jin. Kamar na shake Husnah da Munih , banzaye kawai. Na faɗa a raina, haka nayi ta sintiri daga d'akina zuwa falo..kaina ya kulle.

"Karki damu! Amma maganar bata mutu ba, domin haka gobe zata kuma kamawa da wuta."

       "Akan me? Ba yace a bar maganar ba.!"
"Tuba nake sarauniya ta."
Tsaki nayi na kwanta, har washi gari naki cewa kome, ina jin bakin cikin abin da suka min, kawai sai ga sako daga cikin gidan wai nazo.

    Dama kuma ina kallon yadda kowa yake sunkuyar da kan shi, ina shiga na sami Jay a kwance, ana mishi karin ruwa, a hankali na zauna, tare da gaishe da manyan fadan. Kallona suka yi sannan suka yi shiru, dake a falon bana sarki suke.

            "Fatimah! Meye amfanin gubar da kika saka mishi?" Inji Baba Galadima, zaro ido nayi akan shi, kafin na rike bakina, sannan na kalli bakin shi yayi fari. Girgiza kai nayi sannan nace mishi.
"Kaji tsoron Allah!"
"Ku fito min da Ita!" Fito da Zabba'u aka yi! Jikina ya dauki rawa, domin kuwa sun mata duka na fitar hankali, ta zube a gabana.
"Uwar d'akina! Kiyi hakuri sani aka yi." Lumshe idanun nayi sannan na mai da tambayar da Baban Fahad yayi min.
"Ke baki haihu ba, sannan baki bar shi ya rayu cikin salama da aminci ba,.meye ribarki."

           "Kuyi hakuri! Nayi Kuskure. Ba kuma zan kara ba," cike da mamaki Galadima ya kalle ni, sannan yayi kwafa domin yaso nayi musu, ya sami hujjar da zasu kafa a kaina.

       Kuma na san cewa hakan dole ce zata faru.
"Zamu haramta miki shiga cikin mutane, sannan bamu yarda ki yi mu'amala da kowa ba, sabida karki kara sa mana shi."

"Toh da aljanu zanyi rayuwa, kawai ku janye sharadin ku na farko, shine gaskiyar magana, amma ba makawa wallahi zan yi mu'amala da mutane, idan ta kama nayi da irinka ma zanyi ."

         "Kee mara kunya, ki iya da bakin ki,".juyawa nayi na kalli bafaden, da kan shi ya fasa ihu..sannan na nuna Galadima ina kallon Bafaden, nace mishi.
"Me kace ma?"
"Ranki shi dad'e! Kina da damar kiyi yadda kike so."
"Tashi kabar nan!"
Da sauri ya mike zai fita aka taÉ—e shi ya fadi, sai da kashin kafar yayi kara, sannan na kalli Baban Fahad, nace mishi.
"Me kace?"
"A'a! Ban ce kome ba, kawai abun ya bani mamaki yadda kika iya cutar da mutumin da kike so?"

"Ka yarda kenan?"na jefa mishi tambayar, girgiza min kai yayi sannan. Yace min
"Bani da zab'i da ya wuce na amsa!"
"Haka yayi kyau, shi yasa Galadima zai bawa Fahad Shkurah! Bayan anyi maganar shi da Jannart?"
"Wannan tsakanin mu ne! Bata shafe ki ba,"

Gyada mishi kai nayi, sannan nace mishi.
" Zaka iya tafi."
Jikin shi a sanyayye, ya fita tare da rike hannu Galadima suka fita daga gidan, zuciyar su na kara ruruwa. Kallon sauran nayi wanda dama su kansu a haÉ—e yake, jini ne ya digo min a hancina,nace musu.

"Kuyi hakuri! Ba zan tab'a cutar da karen Jay ba, balle shi.na amsa ne sabida. Bana son a cigaba da wulakanta wannan baiwar Allah, don Allah kuyi min afuwa zan kula dashi."

"Babu damuwa zaki iya kula dashi, amma sarki Kazeem ya nemi da akai shi borno suyi jinyar shi a can."

"Don Allah ku barni na bishi."
"Zaki iya shiryawa ku tafi tare!"
Dan haka na fito daga cikin falon, ina fita suka yi shiru, Abban Jay ya kalli Jay da ya bude idanun shi taree ya zauna, yace musu.
"Don Allah wai meye Galadima yake nima dani?"

"Kai zamu tambaya tunda kai ne ka shirya ka kuma bamu damar mu zama kananun mutane."
Shafa kan shi yayi sannan ya janyo laptop din shi, ya tura musu suna gani, shigowar Najim, ya kara musu bayanin abinda yake ganin ya kamata ayi.
"Munih ta zauna a gurin Mamah, ita kuma Husnah zata cigaba da amsar shirin Kakanta ba tare da tasan mun sani ba, sai dai akwai matsala"

"Wacce irin Matsala?" Suka tambaye shi.
"Dole zan raba Aanih da abin da suke damunta, ku duba na'ura zaku ga tana magana, har tana kuma nuna dagaske akwai wani a kusa da ita. Sannan kadan idan kuka isa zaku ga wani abin mamaki."

Aikuwa sunyi mamakin ganin abinda yake son gaya musu, kallon shi, Baba Magaji yayi sannan yace mishi.
"Dole idan za a raba ta dasu, zai zama tashin hankali, domin tana faffutikar ganin ka samu kome naka, ita kuma suna kokarin ganin ta koma musu, matukar aka bar ganuwar nan dole zata bisu, idan kuma aka rushe zata rayuwa sai dai zata nakasa, dan ba lallai bane tayi lafiya kamar da."

"A'a bana son ko daya, kawai ta zauna dani yafiye min Alkhairin akan ta tafi tabarni don Allah karku raba mu." Ya fada a sanyayye.

"Jalaludeen! Kuje ku dawo, amma kai da kanka zaka bukaci haka, domin tayi nisa a mu'amala dasu, tunda tana iya sawa ayi hukunci a can fadar Ziryana."

"Taya haka ya faru?" Ya faÉ—a bakin shi yana rawa.
"Ta sakacin ku da ambaton Allah! Gidanku ya zama kango, kowa yana rayuwa a inda yake, babu kome. Har gwara ita, tana mai da hankali akan ibada, shi yasa wancan mutanen basu yi tasirin juya tunanin ta ba, amma da sunyi nasarar tafiya da tunanin ta zuwa ga duniya, zai yi wuya ta iya fahimtar kome akan su.

... Kana tare da ita sai da na gaya maka, karka bari wani alamun ciki ya bayyana a tare da ita, shine kayi wannan kuskuren, har kake tuninanin dakatar dasu, ba zai yiwu ba, sabida ta rigada ta amshi kambun su, kuma abu me wuya kenan, rabata da wannan kambun, cikin ruwan sanyi. Kuje da ita Maiduguri idan kun dawo kazo mu san me zamu yi, karka manta ka dawo nan da wasu kwanaki uku, karka yarda ka wuce haka, sannan itama sayare ka dawo da ita, cikin gidan ku. Kun dai ji....kuyi hakuri don Allah har yanzun sai a hankali 🤦🏽‍♀�
10/23/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: *_Daminan bana ba irin ta Bara bace._*

"Da yafi maka!" Har ya juya zai tafi ya dawo da baya, cikin jin haushi riko hannuna zai yi nayi maza na dakatar da shi.
"Karka tab'a ni!"

"Kee wai meye nayi miki ne da zafi? Na lura haushina kike ji!" Juya mishi baya nayi na cigaba da abin da nake, haka ya karaci tsayuwar shi ya bar dakin.

A hankali kome ke tafiya, Jay kuwa, idan zai fita nakan ce mishi, ka dai dage da addu'a, kawai. Idan na fadi haka mamaki yake ji, sai ya tafi zai kuma turo min sako ga abin da yake faruwa a cikin fada Habu da kan shi ya gaya musu shi ya kashe Ajiya sannan ya kashe Fulani Hasiyah. Tun kafin ya dawo gida ya turo min sakon abin ya faru.
Tura mishi sako nayi nace mishi.

_Ka hana Najim fita daga cikin masarautan nan sannan ka kula da shi._

Sake turo min sakon yayi tare da tambaya na *Lafiya?*
_Babu_ na tura mishi sannan na share batun shi.

---
Wata na hudu da dawowa, Munih ta sauka lafiya, Yaron kyakyawa da shi, dan har yafi Yar Husnah kyau da kama da Jay, tun da aka yi haihuwar danginta na Nijar suka zo, tare da iyayen ta.
Chapter 58 · 0% Book details