← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 72

Sashe 56

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   "Ni rawa gadon mai kyau ce? Wasu tasu gadon har abada ba zasu iya sakewa da mutane ba, Ni Yanzun idan Uwata ya zo nan an santa da zafi yanayinta kenan, uwar wata kuwa sai dai kaga ana tattara kome saboda dabi'ar bera gareta."

      "Kan uban can! Ni kika zaga?"  Inji Hoor!
                "Bafa zagi nayi ba, wai ina gaya miki gadon da muka yi ne, ke baki fahimtar Yaren ne."

    Ai kuwa suka fita, can sai gasu tare da dangin Mahaifiyata, suka shigo zasu dake ta, kallon su tayi sannan ta girgiza kanta, tace musu.
"Ko kunya baku ji ba, kun dibo jiki zaku wulakantata sabida an gaya muku karya da Karerayi akan yar yar uwan ku, ko tausayin rashin uwa da bata dashi baku yi. Kun zauna akan abinda aka gaya muku sabida ranku yana sosuwa da SOYAYYA da ta samu a gurin mahaifinta.

       Da yau dukiya tana dawo da mutum tabbas Hassanah Ummina zamu bada duk abinda muka mallaka daga masarautan daura har zuwa masarautan shehun Borno, tun duniya tana kwance ahalin mu suke taka rawan gani a kasar nan.

          Dukiya mun gan shi mun kuma san shi, soyayyar da Zuri'ar mu takewa Hammah Jay, ya wuce yadda kuke tsammani..akan shi kuke tsanar Mahaifiyata? Sabida son kai da son zuciya, toh ku dake ni, sabida nice nayi magana ba mareniya ba.

Ko kunya baku ji ba, ku iyaye kuna fadan abubuwan da basu dace ba akan yan uwanku, wallahi matukar Fatima ta shiga cikin Zuri'ar mahaifiyata sai kun gane cewa shi mulki da dukiya al'amarin Ubangiji ne, yau muna kallon Hammah Jay a matsayin Mahaifiyarshi ce, sabida shi daya ta bari.

   Bamu da madadinta sai shi, mahaifiyarta ta rasu ta bar muku  ita, domin idan kun tuna da ita ga madadinta sai ku mata addu'a, amma sai gashi babu wacce kuka tsana sama da ita, da yau ana mutuwa a dawo baku ji kunyar Mameeh ta dawo ta ga abinda kukewa Yar ta ba. Burin ku sunan ta ya b'aci ace sabida rashin amana mahaifinta ya gaza bata tarbiyyar da ya dace. Ku ji tsoron Allah akan zalunci da kuka mata. Allah sai yabi mata hakkin ta, karku manta akwai rayuwa akwai mutuwa.".
Daga haka ta riko hannuna zata fita ta kalli Hoor tace mata.

"Kuskuren ki tab'a min ji kimata! Shi yasa na tab'a naki, ba kare bin damu!" Daga haka muka bar gidan. Ina kuka Allah yasa ita ke jan motar dan dukkan mu Baabi ya saka an koya mana mota.

             "Nagode kanwata Kawata." Na faɗa mata cikin kuka, girgiza kai tayi sannan ta cigaba da tuka mota tana faɗin.
"Ban san me yasa baki iya karban kanki hannun mutane ba, nifa ba zanyiwa kowa kuka ba"

       "Sabida kuka da gadon taurin zuciya ba! Kuna iya boye kaunar abinda kuke so ba! Da zaki ji yadda nake son D'an uwanki da sai kin tausaya min."

  "Mun sani mana, toh ya zamu yi da dangin Baabi? Kin san Ummi ma ba sha tayi a hannun su ba, kawai tafi su baki ne. Wallahi kaf dangin Ummi babu wanda baya mutuntaki, ana ganin darajarki fiye da yadda baki zata ba, ko jiya sai Da Kaka Bana ya tambayi Hammah Jay, akan da gaske yana sonki? Yaki bashi amsa.
.da ya bashi amsa toh ina gaya miki sisin gwal ne sadakin ki.

     .ko Ni bana tsammanin zan sami sadaki sisin gwal, amma ke naji har kowa ya gama hada kome na sadakinki.. amma mara kirkin nan ya ce baya sonki."

     Lumshe idanuna nayi sabida kalmar baya sona ba sabon kalma bace da zan ji haushinta, kalmar ta jima da zame min Alakakai. Bude idanu nayi lokacin da naji ta ja burki.

          Ikrama ne ya sha gaban mu, da sauri nace.
"Ke tadda motar mu bar nan mahaukaci ne."

Sai da ta barshi ya kusan zuwa dab damu, kawai ta finciki motar da masifar gudu, ya kuma koma cikin nashi ya rufa mana.

  Da sauri na shiga lallubar Number Saif, ban san na fada kan Number Jay ba, kawai na shiga kiran shi.....

Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....
#Mai_Dambu...
10/23/20, 10:05 AM - Ummi Tandama: *_Shiru kake ji... Malam yaci shirwa_*

A hankali ya fito cikin motar ya rike hannuna muka shiga cikin gidan. Tana zaune akan daya daga cikin kujerun falon, tun da muka yi sallama ta amsa tare da  kauda kan ta.

"Shine kika bishi! Bayan ya gama tozarta ki, a gaban jama'a ya wulakantaki, sannan yace ya sake ki,
...... Idan har yana da damar da zai wulakantaki ba kowa bane ya bada damar haka sai ke! Sabida baki san Darajar kanki ba balle shi yasan naki, ya dibo jiki yazo ke kuma kika bishi wannan wani irin hauka kike yi ne da sunan so? Ka fita ka bani guri, idan na kuma ganin ka, ranka zai b'aci sosai wallahi."

"Allah ya huci zuciyar ki! Ayi min afwa amma wallahi ina son Mata ta," ya faÉ—a a sanyayye, d'ago kai nayi ina kallon shi. Ya gyada min kai. Sannan ya juya ya bar gidan. Ni kuma Mamah ta cigaba da min fada.

Daga nan gidan bai tsaya ba, ya wuce katsina, ta jirgin sama, yana sauka, ya kira Murad ya kai shi har gidan da Baba Galadima yake kakan Husnah yaba son suyi magana akan matsalar masarautar su. Daga nan suka juya zuwa cikin gidan sarautar Katsina, anan ya wuni yana ta wasu shirya shiryen yadda zai zauna gana yaƙe. Dan yana son fidda mutum na ƙarshe.

Yana zaune yaga wasu yan mata zasu wuce, daya tana cewa.
"Ina son zuwa kwatarkwashi, naga jikin Kakata Sahurah."

"Kai Aminatu! Itace wacce ta zauna a masarautar Daura ba?" Cikin jin dad'i yarinyar ta gyadawa yar uwarta kai,, har suka wuce. Sauka yayi ya shiga motar, ya nufi garin.

----
Dakyar ya same ta, koda ya isa gabanta, jan tsaki iska tayi sannan tace mishi.
"Sun nisanta ka daga Ziryana! Sun hanaka fahimtar inda matsalar take.

Sai dai kash sunyi kuskuren, domin yanzun haka kome zai iya faruwa daga zarar ita wacce take haÉ—e da rayuwarka ta mike da kafarta."

Daga nan ta shiga mishi bayanin abubuwan da suka fara da abin da ta aikata, sannan ta kuma jadadda Mishi irin abubuwan da suke faruwa da wanda zasu faru ma nan gaba, ta kuma gaya mishi dole ya nimo mutanen da suke niman rayuwar shi.

"Ko zamu tafi sauran dake?" Girgiza kai tayi sannan tace Mishi.
"Ni mahakauniya ce! Bani da karfin da zan iya kare kaina, itama Fulani da take hannun ka ba lallai ka koma ka sameta a raye domin sun shirya maka yadda baka yi tsammani ba."

Daga haka ya mik'e tsaye, sannan yace mata.
"Ni zan tafi!"
"Nagode ranka shi dad'e, kayi ƙoƙarin gano waye ki bibiyar ka!"
"Insha Allah!" Ya furta a hankali.

----
Washi gari.

Ya samu ganin Baba Galadima. Sun tattauna sosai, har ya mike zai bar gidan Baba Galadima yace mishi.
"Ka shirya niman wanda baka sani ba?" Juyawa Jay yayi sannan yace mishi.
"Yallabai tsaf na shirya niman shi, na shirya cin kaniyar shi, sai na gyara mishi zama, idan na kama shi sai na haramtawa Zuri'ar shi mulki baki daya, sai na fitina kome na shi muje zuwa."

Daga haka ya fice daga gidan..
Kai tsaye daura ya wuce abun shi.

----
Tun da ya isa, ya shiga yiwa manyan masarautan, lokaci guda ya shiga amsar duk wani abun da aka yi ba bisa ka'ida ba. Wasu abubuwan ma kawai jin su ake amma Jay ya Bankad'o su.

Ana cikin haka Allah yayi wa Ajiya rasu, take aka mai da mutuwar kan Jay, inda suka ce da hannun shi. Sai dai bai ce musu kome ba.

Yana sane amma yaki magana abin da ya kuma basu haushi yadda yasa aka kwashe kayan fadar aka kuma saka wasu, abin ya basu haushi domin a garin cire wasu abubuwan aka yi zaro layyu, da wasu abubuwan murmushi yayi sannan ya bada aka kaiwa Baba Magaji. Gefe gudakuwa Ba komai ke damun shi ba sai kewar Yar guzumar matar shi, ta tsaya mishi a rai.

Ban da yana matuƙar kunyar Mamah Raihanah ba, da yake ya dauko matar shi, amma cike yake da kewarta. Nutsuwar da ya samu da ita, ba na wasa bane shi yasa yake kuma jin lallai zai koma Abujan.

..... "Jay jiya na sami wannan takardun a hannun Baba Hashim, ya bani kuma abun mamaki sunan Galadima ne ya fito a cikin. Meye alaƙar shi da mutuwar Ajiya dan Abba ya gaya min cewa akwai matsala a tsakanin su. Kafin wannan abun ya fito." Karb'an takardan yayi sannan ya duba kana ya dube Najim yace mishi.
"A bisa binciken da nake, Galadima yana cikin magadan masarautan nan! Domin shi kakan shi na uku shine Zulum, Ziryana itace kakar Ammih na uku.

Abun da na kasa anan wancan lokacin da lokacin Ammina akan ta akayi rigimar! Wannan lokacin kuma akan wacece za ayi rigimar?"

"Eh amma, ina ganin babu mace a wannan karnin da za ayi rigimar akanta shine ya koma akan karagar mulkin ka." Inji Najim,

"Nima na fahimci haka,"

Shiru yayi sannan ya cigaba da dube dube, har zuwa lokacin da suka bar fadar.

.....
"Fulani! Dama ina son muyi tsayayyar magana. Waye ya.."
.
"Jalal ban san kome ba!" Ta gaya mishi haka tare da kauda kanta, dan dole ya hakura ya fita, yana shiga gidan shi, ana kiran shi a waya yazo ga shi an shigo an kashe fulani.

Wannan tashin hankali yayi matukar tasiri akan shi, yasan suna fakon mutanen da yake zargi ne, shi yasa.

Haka ya isa yaga irin kisan da aka mata, sawa yayi a kama masu kula da kofar ta, yayi ta azabtar dasu, har sai sunyi magana.
Chapter 56 · 0% Book details