← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 72

Sashe 4

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina sallah ina kuka, har na idar, sannan na zauna naci gaba da kuka, ina tausayin kaina da Baabina, Shigowar Mama Sarah da Umma Raihanah, da wasu mata dai da suke da daraja, duka shiga shirya ni cikin liffaya, tare da min wanka da turaren zamani da na hadin Maiduguri, aka kaini shashin kaka na, inda Baabina yake, tunda na shiga na matsa jikin Baabih na daura kaina a bisa cinyar shi, ina sauke ajiyar zuciya.

Haka suka min nasiha sosai, sannan aka zo za a fita dani na rike shi, nace.
"Wallahi bazan biku ba, shi zai kai ni!"
.dayawa yan uwan shi, sun ji haushina amma ban damu ba, sabida bani da kowa sama dashi, Haka ya riko hannuna ina kuka ya amshi keyn mota ya saka Ni gefen shi, bai dauki kowa ba, muka nufi gidan su Muhid, tun kafin mu isa aka kira Muhid aka gaya mishi ga Amaryan shi babanta yake kawo ta.

Yan rakiya na, sun biyo bayan mu, koda muka isa. Har cikin gidan ya kaini ya zauna a babban falon gidan yayi ce a kira mishi Maman Muhid! Cikin shigar kamala ta iso.

Bayan sun gaisa, sannan yace mata.
"Toh ga Fatimah Khatoon nan na kawo miki ita, Bata san mahaifiyarta ba, amma tasan Baabinta, Amma daga ganin Muhid nasan cewa! Yayi sa'an Uwa, ko babu kome zaki riketa a matsayin yar da ta taso babu uwa, nagode sosai."
.ya faÉ—a a raunane, cikin damuwa da kewata. A hankali ya mike na kuma rike hannun shi. Cikin kuka ina cewa.
"Baabi! Don Allah!"

Rikon da Muhid yayi min itace ta hanani karasa abinda zan fada, haka baabi ya tafi ya barni a cikin su, Ummi da Sauran mutanen suka kai ni dakin Naman Muhid, kowa sai magana yake akan irin shakuwar da take tsakanina da baabi.

Dakyar nayi barci me cike da ban tsoro da firgitarwa, cikin dare, naji ana ta hayaniya, buÉ—e idanu nayi naga Maman Muhid tana share kwalla, hannunta rike da calbi, tashi nayi zaune tace min.
"Koma ki kwanta kinji!"

Shigowar Tayar shi tana kuka wiwi, ya sani tashi zaune ina raba idanuna.

"Allah ya jikan Muhid!"

Wasu irin taurari naga suna yawo a kaina, daga nan yadda na bude baki zanyi magana, kawai sai bushewa nayi a gurin. Hankalin su yayi mugun tashi.

Akan lokaci aka wuce dani asibitin kwararru na nan Sokoto, aka shiga duba lafiya, kafin asuba Baabi ya iso, cikin farar jallabiya.

Ina kwance, zama yayi a gabana yana me tausaya min, har na farka rike wuyana nayi ina son nayi magana amma ya makale.

Dakyar nace mishi.
"Baabih ruwa!"
Babu ruwa a dakin dole ya fita, aka nimo ruwan ya dawo ya bani nasha, wani irin kuka ne ya kwace min, ban san ya akayi ba nayi aman jini. Abin ya d'aga hankalin Baabih akwai Kanwar shi da take aure a Canada, tazo itama , dan haka zama tayi a jikina.

Haka na zama kamar mahaukaciya, bana hum bana hmm! Har tsawon kwanaki bakwai aka sallame ni, daga nan gidan Mu aka wuce dani, a lokacin Ummih da Ammih suka ke kula dani, na sha matukar wahala, sabida bana iya magana da kowa, mutuwar mijina. Ya dake ni.

Ashe rungume Ni da yayi shine kawai abinda zai hada mu dashi, haka nayi ta jinyar zuciyata. Na tsawon watanni sannan na koma makaranta dan saura kiris na tasa jarabawar karshe.

Muna gamawa na samu damar tafiya, bautar ƙasa, har zuwa lokacin naki sake jiki da wani namijin dan gani nake kamar abinda ya faru da Muhid zai kuma faru dashi.

Koda na gama bautar ƙasa, na samu koyarwa a cikin wata makarantar kwana da take nan Sokoto.....
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

      Fatan Alkhairi gare ki Mame na group ɗin Bagudu 😍🌹

HUÆŠU

Cikin lokaci ƙalilan na fara koyarwa, bawai dan albashin ba a'a, sai dai haka yana matukar rage min kewar Muhid, sosai na maida hankali na sosai akan abinda nake.

              Shi yasa sam ban kuma damuwa da kowa ba, sai dai haka kawai muna cikin wannan yanayin Sai ga Baraq ya shigo rayuwata.

           Tun daga ranar da na ganshi, a daren na kwana ina mafarkin shi, inda nake ganin shi kwance cikin jini.

Washi gari haka na tashi babu walwala, tunda na nufi makarantar na daure fuskana tam, duk yadda naso kauce Mishi sai da ya shige min.

                  Haka muka tashi ban sake mishi fuska ba, duk yadda naso kar na shiga rayuwar shi, ina Baraq ya gama shigewa rayuwata. Shi yasa naki shi yayi juyin duniyar akan naso shi naki.

     Yakan sani a gaba yana kallon tare da ce min.
"Fatimah meye laifina?! Ko dan bamu da arziki ne?!"

     Girgiza kai nayi, sannan na zuba mishi ido, kafin na bude baki nace.
"Kawai bana jin kome akan ka ne! Kuma da zaka taimaka min ka daina damuna zai fiye maka Alkhairi."

   "Toh an tab'a kin mutum babu dalili ne? Ki gaya min meye matsalar ki da ni?!"

     Mik'ewa nayi ina duba agogon hannuna, sanan nayi wuccewa ta na barshi a gurin tsaye. Yana mamakin yadda nake gudun shi.

       ---
Baraq Nafi'u! Ya addabi rayuwata, yadda ya kai kanshi gurin Baabi ya bani mamaki, dan haka ba iya gurin Baabi ba, sai da ya gama zage dangin mu, na cikin masarautar, da nuna musu yana kaunata.

    Su kuma suka mara mishi baya da taimakon Baabi, zama nayi a gaban Baabi, ina kuka wanda tun rasuwar Muhid ban kuma haka ba, kallona yayi sannan yace.

          "Toh Mamana meye na kuka haka indai Baraq ne, zan ce me ya hakura, kuma zan nima miki wanda ranki yake so! Amma ki duba dakyau yaron yayi kokari domin kowa a cikin zuri'ar mu, ana son shi dan haka kiyi hakuri ki amince ayi abin."

Cire kaina nayi cikin kuka nace.
"Baabi! Tsoro nake ji! Ina tsoron abinda ya faru da Muhid don Allah baabi na kayi wani abu."

    Jikin shi ne yayi masifar sanyi, tare da kura min ido, yana me jinjina maganar da nayi, amma da ya tuna. An hana shi camfin abinda zai faru, dani sai ya zuba min ido na wasu lokuta kafin yace.
"Za ayi auren ki daina sakawa a ranki wani abu zai faru saboda babu kyau canfe!"

Da haka Baabi ya kashe bakin maganan ya kuma hanani cewa kome, na cigaba da zubda kwalla, ba tare da na amince ba Baraq ya shiga niman aurena, tare da goyan bayan Baabi na, sabida lokacin, na kai shekaru ashirin da biyar, dan bayan na gama bautar ƙasa, nadan zauna na shekara daya, toh yanzun fara aikina ma yana niman shekara biyu.

      ..tun ina nunawa bana so, har ta kai na hakura, sabida Baraq akwai son sanya mutum a walwala. Haka kuma Iyayen shi, suma sunyi godiya sosai da irin karb'an da aka yiwa ɗan su.

             Tunda aka fara hidimar na fara mafarkin ya mutu, har aka daura auren, a tsora ce nake, kasancewar ni bazawara ce yasa aka kayi kome a ranar, sannan aka watse.

          Bayan ya samu rakiyar abokan shi, tare da mana yar nasiha. Sannan ya raka su.

  Bayan ya dawo, ya fara nuna min wasu abubuwan da gaskiya tunanina bai kai nan ba, kunyar shi tasa na shige ban daki nayo..ina cikin ban dakin naji yana magana a waya, ina fitowa ya janyo ni, tare da matse ni a jikin bango, ga baki daya dauke wuta nayi, sabida jin yana min abinda yafi karfin tsayuwa.

    Lokaci guda naji kamar zan zube, haka ya kuma matse ni kamar zai yi kome dani a tsaye, duk da a shekaruna bai dace na razana da shi ba, amma ga baki daya sai nake ganin kamar yana wuce iyakata.

    .... Ganin kamar zan zube a kasa ya sashi mana masauki a gadon, daga nan ya nime kome ya faru, sai dai buga kofar gidan da ake yi yasa Allah ya kwace ni a hannun shi, har zai fita ya tsaya yana murmushi sannan yace.
"Da dai kin buÉ—e idanunki, domin yau zamu raya daren ne!"

         Jan bargo nayi tare da rufe fuskana, ina me juya mishi baya. dan ban san ya akayi kayan jikina suka watse ba, gidan da muke hade yake da na iyayen shi, suna dan ciki damu. Dan haka naji muryan yayar shi mace da namiji suna magana da ƙarfi.

                "Yo kwaɗayin abin duniya Yasaka auri mutuwarka ita din ba macen aure bace, sabida akwai tsinuwar  mutane da aljanu akanta kazo muje cikin gida, kaji a cikin mutanen da suka zo daga kauye iskar wata ya tashi take gaya mana, wallahi kazo."

                Koda suka shiga abinda matar tace.
"Ayya! Ina baku hakuri sabida sun kashe shi, kuma itama yasan ya mutu, tunda tana yawan ganin shi cikin barcinta an kashe shi, dan haka kuyi hakuri ku koreta a gidan dan zasu iya yin komai."

      Kawai ganin Baraq aka yi ya yanki jiki ya zube tare da anan jini, dan haka kanen shi da mugun gudu suka yi d'akina, tare da rufewa zasu dake shi, sai dai abin mamaki sunyi bugun duniyar nan yaki buɗewa karshe haka suka hakura.
Chapter 4 · 0% Book details