← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 72

Sashe 45

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karki bari abokan zamanki su fahimci ma'ana fuskar ki, ya taimakawa kanki gurin, adana damuwarki, domin ita ce hanyar da zata kawo zai iya amfani dashi dan cutar dake.

.... Gidan aurenki ki zauna koda kuwa hakan yana tab'a ki, Allah yana sane dake, sau dayawa muna ganin dan ana cutar mu, zamu iya kwatar kanmu. Hmm ba haka bane, idan kika fito an cutar dake wanda zaki aura me zai miki!

Karki zama macen da bata san meye ke damunta ba, domin yin haka tankar tallata kanki kika yi, idan kika zama haka toh ko ruwa baki isa sha ba, mijinki yarone eh kar haka ya baki damar da zaki rena shi.

Domin duk wani abinda ya dace na hakkin shi yana wuyarki kuma dole ki bishi.

.zaki ga abin da ranki baya so, amma ki gani da idanunki toh ki zama makauniya, ki zama kin ji amma ki zama kurma, kar ki yarda dangin shi su zarge ki da mara hakuri, ki zauna kiyi hakuri domin su akan kansu zasu yarda kinyi rawan gani.
. masarautan cike take da kalubalen rayuwa, amma dole ki zama macen da tasan darajar kanta da kuma mijinta.

Duk abin zaki yi a rayuwa ko nime taimakon Allah, ki kuma kiyayye abinda Ubangiji yace, karki manta Allah yana sane dake, da kuma sauran mutanen baki daya, karki yarda Shi kan shi ya fahimci baki da'a domin yin haka tankar zubda kai ne.
. Rayuwar aure kamar littafi ne,har ki gama rayuwarki ba zaki tab'a karance shi.
. Kalubalen rayuwa kin gan shi, kuma har yau akwai mutanen da basu yi fatan ki zauna lafiya. Ban gaya miki don ki zaka a ranki ba a kaunar ki a'a na gaya miki ne dan ki fahimci wani abu a rayuwa.

Za a ce miki mijinki yarone! Eh kin yarda yaron ne. Akwai masu fatan niman hanyar da zasu sami irin shi ma babu.

Sau dayawa kowa yana jin yayi Sa'a, amma mafi girman Sa'a ita ce Ubangiji ya baka hakuri da juriya irinta rayuwa, Idan kika saka Allah a cikin lamurran ki, wallahi babu wanda ya isa ya cutar dake ba tare da Allah ya kawo miki É—auki ba, idan kika dauki dangin shi da iyayen shi babu abin da zai miki Allah bai saka mishi ba. Karki yarda ki cuce shi ko abokan zaman ki.

Ita Sakayya a duniya ake yinta, dan haka idan kika yarda da Allah babu wanda ya isa ya miki haushi ki kula shi, Ubangiji baki zaman lafiya! Ki ga dai yadda Allah ya tsara miki rayuwa kiyi hakuri, Allah yana tare dake.

Kuma rike wannan Alqur'anin, tare da duk wata azkar, Ubangiji zai zame kawo miki É—auki a duk halin da kike. Tashi ki tafi Allah ya miki albarka yasa kin tafi a sa'a."

Kasa tashi nayi ina kuka kamar raina zai fita, saboda ba a tab'a min nasihar da ta shiga cikin jikina da rayuwata irin na yau ba.

Ba a tab'a gaya min meye rayuwar aure da hakuri irin na yau ba, har muka fita daga falon, kuka nake ina jin wasu na kus-kus akan nasihar da Umma tayi min, wai tana gwada fifiko akan jikokinta, tafi sun Yaran Hammah Aaryaan.

...... Tunda naji haka na saka a raina, zan zauna da Jay tsakani da Allah, kuma zan bawa dangina mamaki.

... Ina jin ana wurga min magana, ban kula su ba.

Karfe shida muna sauka a Katsina, daga nan muka wuce zuwa Daura, sai magana suke gaya min, kasa kasa. Har muka isa gidan sarautan. Tun daga bakin kofar masarautan ake karban mu cikin mutumtaka, har muka shiga cikin gidan, aka fidda ni a sanyayye nake takawa.

Shashin sa dake sama aka wuce dani, yayinda Munih da Husnah suke shashin kasa.

. Bayan mun yi sallah magarib muka shirya aka nufi gurin walimar da aka shirya mana, tare da yan uwana, tare da dangin shi.

Kaina a sunkuye rufe da mayafi fari kal.

. Karfe goma aka tashi, ko ta kaina bai bi ba, ya nufi inda abokan shi ke nan, suka yi sallama.

---
Tunda muka dawo naji wasu na cewa Munih tayi musu rashin mutunci, sai mita suke Ni dai ban ce musu cikanku ba.

Washi gari.
Aka yi wuni da sannan yan uwana suka tattaro kayan su da Alkhairin da aka musu, suka dawo Sokoto suka bar ni bayan sun gama gaya min cutar dake ran su.

..... Har dare babu ango babu alamar shi, sai kusan asuba, Ina kwance naji ana buga min kofa, na tashi na bude naga fuskar Munih ya kumbura saboda kuka..
"Mayya dama an gaya mishi cewa ke din Makara ce, shine daga zuwa zaki kashe mana miji, toh Tabbas zaki bishi inda ya tafi dan bazamu cigaba da kallonki ba."

Kawai ta d'aga sabuwar wukarta zata soka min na farka tare da tashi zaune, juyawa yayi ya kalle ni tare da harara na, ya juya yace.
"Kema sai kace yarinya karama. Kin kwanta babu addu'a, ba dole ki farka da ihu ba."

Ajiyar zuciya nayi tare da kallon agogon dakin karfe shida da arba'in da biyar komawa nayi na kwanta ina kallon shi yana gyara zaman rigar shi nace mishi.
"Shine baka shigo da wuri ba, ko farkawa ban yi ba sai yanzun."

"Baki gajiya da magana ne?"

Sauka nayi a gadon, ina kallon shi nace.
"Ina zan gaji! Wai kai ne mijina?"
Juyowa yayi hannun shi a kirjin shi, yana kallona.

"Nayi karami ko?" Juya ido nayi sannan na wuce ban daki ina ce mishi.
"Toh me zance bayan ka bawa kanka amsa"

"Famkan famka bata kilishi! Buleliya!"

Ya gaya min, ban samu bashi amsa ba, sabida na shiga ban daki.
Ina fitowa na samu yar karamar takarda.
_Mun tafi rakiya abokaina!" Kirga rubutun nayi ina murmushi, kome na shi baya wuce iya ka.

Sallah na gabatar sannan na mike na shiga gyara dakin, kafin wani lokaci gidan ya dauki saiti domin na saka turare lungu da sako na gidan.

Lokacin da na gama na shiga wanka na fito na caɓa ado cikin riga da zani na lace, bayan na zauna na buga kwalliya na fitar Hankali, ina gamawa yan Maiduguri suka zo min sallama,. Jikina yana rawa.

Na shiga kawo musu kayan Gara, tare da duk abinda hannuna ya kai kai. Na shiga d'akina na duba kayan da aka kawo min na aurena, na kwaso wasu kayan kwalliya, tare da turarruka, sai wanda Baabina yayi min na kwaso na zuba a jakar da Hanisah ta kawo min na bikin mu.

Sai da na fito dashi naji suna cewa.
"Aha ashe kunyi jaka ne, Wallahi kunyi kyau."

Duba hoton nayi ina tsaye a saman shi, na zuba hannuna a kafad'arshi ina dariya shi kuma murmushi, kasa magana. Nayi toh yaushe aka yi wannan hoton.

"Kun dace sosai! Dake da Abbalawan, gashi yafiki cika ido. Don Allah ki rike shi da amana, Maraya ne da ba a yi tsammanin zai zama mutum ba, Yaron da aka ciro shi cikin Mahaifiyarshi ta rasu, ai kinsan Allah ne ya nufa zai yi nisan kwana.

Fatimah gashi nan don Allah karki bari wasu su juya miki tunanin a kanshi idan yayi miki laifi mu zamu hukunta miki shi. Kina da daraja a cikin Zuri'ar shehun Borno, dan haka ga Maiborno ki rike mana shi da amana."

Inji dattijuwa, kunya ya sani sunkuyar da kai, koda na bawa Jannart kayan su, kasa magana suka yi sai godiya suke min, da zasu sauka na raka su, sai da suka ce min na koma cikin gidan, sannan na juya. Ina shiga cikin gidan na hango Munih tana tsaye da wasu kayan fitsara.

Ban kula ta ba, har zan wuce tace min.
"Guzuma! Ke ko kunya baki ji ba. Yaro karami kika nacewa dan bakar fitina, toh wallahi sai na hanaki zama a cikin gidan nan, dani kike zancen."

Murmushi nayi a hankali nayi wuccewa ta, sabida bani da lokacin ta.

"Tsohuwa kawai, sai da kika gama yawon dandinki kika makalewa mijina." Ko a jikina.

Fitowar Husnah sanye da doguwar rigar, ta kalle ni ina haurawa tace min.

"Addah Aanih ina kwana? Ya bakunta?"
Fuskarta cike da fara'a. Cikin jin dadi na tsaya muka gaisa nace mata.
"Alhamdulillahi, Yayar mu ya aka ji da jama'a."

Dariya tayi sannan tace min.
"A'a! Duk wacce namiji ya kwana a d'akinta itace uwar gida. Ke kuma Ya Jalal ya fara kwana a d'akin ki, dan haka kece uwargidan."

Murmushi nayi sannan nace mata, "A'ah."

"Toh munafuka, uwar shishigi kwala kai a faranti ince shekaranjiya ya kwana dake! Kuma kice itace uwar gida, bana son kinibibi, sai na zagi mata."

Wucewa nayi d'akina, Husnah ta wuce kicin domin niman abinda zata ci, kai Munih yar Bala'i ce.

Ina kwance sai ga Jannart tare da kayan abin karyawa ni da Jay, tashi nayi na amsa, sannan na ajiye a gurin cin abinci, sannan na zo na zauna ina kallon ta,sai murmusawa take nace mata.
"Mamanmu! Meke saki dariya."

"Daga karshe dai Ya Saraki ya mallake ki, ji nake kamar yafi kowa dace."

"Toh uwar yan gulma, ina abincin mijina." Babu wanda ya kulata ta nufi gurin abincin zata diba. Rumah ta shigo cikin b'acin rai tace mata.
"Wallahi kika tab'a sai na sab'a miki wato ke mara kunya ko? Sai kin sha mamaki, mara mutunci kawai idan ke aka kawowa sai ki ci yar Banza, kawai."

Dake tana tsoron Rumah kuma yayar miji dole ta hakura. Ta fita tana tsaki. Nan muka sha hira, har Husnah ta shigo muka Cigaba da hira, kafin ta fita sabida yan uwanta da suka zoe.

Ranar anan muka wuni, sai yamma likis ya shigo tun daga bakin kofar ya zuba min ido, suka zaune. A sanyayye na mike na amshi kayan hannun shi tare da ce mishi.
"Barka da dawowa, Saraki."
Chapter 45 · 0% Book details