Sashe 17
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
        Zaunar dani yayi cikin nutsuwa, yana kallon fuskana, jikin shi yayi mugun sanyi.
"Kinga ni wani abu nazo yi,"
         Shiru yayi yana kallon yadda nake kuka, sosai. Zuba gwiwar shi yayi a kasa sosai sannan ya kalle yadda nake ta kukan.
          "Toh naji idan muka je zan roki gafarar Baabi sai na tafi dake!" Ya faɗa min.
    Cak kukan ya tsaya ina kallon shi, a hankali nace.
"Da gaske kake ko kuma kana rarrashina ne, kake?!"
B'ata rai yayi tare da cewa.
"Na tab'a miki karya ne?"
  Daga haka ya bar d'akin, shiryawa nayi tsaf na fito sanye da riga da wando, sai mayafin da na rufe kaina.
       A hankali na shiga cikin gidan gurin Innaih na mata sallama, ta ɗauki da wo. Da madarar rakumi hadi da cukwai ta bani, nayi ta godiya. Jay Mugu ne.
 Farkon zuwa na gidan, sawa yayi tayi ta bani dawo da nonon raƙumi, ba suga. Ina sha ina amai daga baya da na iya sha kuwa ko ya sayo abincin Innaih ta girka bana ci sai da wo.
      Goge kwalla nayi sannan na fita da sauri ganin yana ta danna mana korototo, a hankali na shiga motar ina d'agawa Innaih hannu, a hankali yake jan motar har ya fita daga garin, dan sai yanzun na fahimci a kauye muke.
   Bai kalle ni ba, muka nufi gidan su da yake cikin Damagaram, bari na yayi a cikin motar ya shiga cikin gidan. Take yan matan dangin su tare da yan uwansa suka mishi caaa.
   Murmushi yayi sannan ya kalli kakar su yace.
"Annah! Zan koma inda na fito!"
    Tab'e baki tayi, sannan tace.
"Da fatan dai ba wani abun ka rakato ba."
Mik'ewa yayi zai fita ya ajiye mata kuÉ—i me mugun yawa, sam bai san lokacin da zai burgeta ba,da ace tare da Munih suka zo da tuni ta shiga rawan jiki dasu.
    "Ya Jay! Don Allah ka tsaya muyi hoto mana!" Inji wata yar kyakyawar budurwa.
     Tsayawa yayi suka dauki hoto, sannan ya shiga cikin gidan ya gaida matan baffanin shi, kafin ya fito.
 Motar shi ya shiga, gani na ina wasa da awarwaron hannuna, yasa shi tab'e baki, yaja motar da mugun gudu.
         Sanyin motar wanda yake hade da turare, yasa ni lumshe idanuna, gudu yake sosai, tare da kallona lokaci zuwa lokaci, sai da mukayi tafiyar awa biyu sannan ya tsaya tare da saya min abinci, kugun tsamiya tare da gashashen nama, tunda na sha, sai ga zufa na karyo min.
    Murmushi yayi tare da share abinda yayi niyyar fada, yasan shi ba mutum me yawan magana bane, amma haduwar mu tasan yashi zama me yawan magana tare da dogon magana abinda yakewa da kallon damuwa ko ciwon kai, sai gashi yakan iya tsawaita magana kamar bashi ba.
     "Shaidaniya!"
Kallon shi nayi tare da b'ata fuska,
"Ba dai ni ba?!" Na faÉ—a a hasale.
"Toh cire min kayana!"
Ya fada fuskarshi babu wasa.
Sunkuyar da kaina nayi, cikin tashin hankali.
"Kayi hakuri!"
Share ni yayi kamar bazai kuma magana ba, ya cigaba da tukin shi...Â
    Kallon shi na tsaya ina yi, kamar wata mara hankali..
"Don Allah kalli gabanki"
Â
Ajiyar zuciya na sauke sannan nace.
"Jay ince baka manta alqawarin mu ba?!"
         "Don Allah kayi min magana mana!" Janyo asusun jikin motar shi yayi tare da dauko wata yar kamar kwalba, da abin allura, yaja ruwan cikin shi.
     Sai da ya gama durawa,sannan ya rufe yana tukin gangancin, sai da yaga hankalina yayi nisa, kawai ya cakka min a damtsen hannuna, sannan ya zare ya cigaba da tafiyar shi, a hankali barci yayi gaba dani, sauke min kujeran yayi sannan ya cigaba da tafiyar shi.
  Tafiya muka yi wanda ni kaina ban san awowin da muka yi ba, sai dai naji yana shafa min ruwan sanyi, a fuskana. A hankali na bude idanuna ina kallon shi. Ganin har karfe biyar na yammaci ake nima, na kalle shi tare da cewa.
"Ban yi sallah ba."
    Fita yayi a hankali yace min.
"Muna boda! Kiyi sallah ina jiranki"
   Sauka nayi na tafi wani gidan wanka nayo tsarki da alola, sannan na dawo na yadda sallah, ina idarwa yana mika min, abinci a cikin kwalin tafi da gidanka wato (take away)
    Tunda na sami guri na zauna na fara ci, shakuwa na fara ya mika min ruwa nasha, sannan ya koma ma zauna shi. Har muka isa inda ake duba kayan mu, sannan muka wuce.
           Kallona yayi, cikin ko in kula yace.
"Barka da zagayowar ranar haihuwarki, ga cake can a bayan mota, ki dauka. Amma kiyi hakuri ban cika miki sauran burinki ba."
  A hankali na juya naga wata ƙatuwar kwali.
"Taya aka yi kasan da haka?!"
      "Duk wanda ya shigo rayuwata! Ina bindidigin shi!" Ya fada min,
"Kamar Y'a?!" Tun daga lokacin da kika fara fada dani! Na shiga bin dukkan tsarin ki!"
  Shiru nayi dan Jay ya fara bani tsoro, ban ce mishi kala ba, sai ɗaukar cake din da nayi..
Naga an rubuta Barka da zagayowar Haihuwar ki 34, kwalla ce ta sauka akan cake É—in.
."taya kasan ina son chocolat cake?! Naga ban tab'a gaya maka ba, sannan."
."na gaji bani son Damuwa!".
  Shiru nayi ina kallon shi,"kalli gabanki" yace min.
       Taya zai fahimci ainihin abinda yake damuna! Taya zan fahimtar dashi yadda nake jin shi. Da Jay zai fahimci halin da nake ciki da ya sassauta min.
    Goge kwalla nayi tare da yanka cake din na sanya mishi a gefen bakin shi.
Kallon yadda nayi da fuska ya sashi bude bakin shi, sai da ya ciza da hannuna, da sauri na cire hannun tare da zabga mishi harara.
   Kallon madubin motar shi yayi yaga ana bin mu motar yan sanda tare da na sojoji.
   Karawa motar shi gudu, yayi dan yana son yau idan ya ajiye ni ya koma nijar, gudu yake sosai kamar zai tashi sama.
  Har ya b'acewa ganin su,. Ajiye min agogona yayi akan gwiwata.
"Kin tuna shi?!"
     Kallon shi nayi sake da baki, a hankali ya kuma fisgar motar kaman zai tashi sama, karfe tara yayi mana a garin sokoto, kallona yayi sannan yace.
"Ban tab'a sab'a alqawari ba, amma bazan iya cika miki naki ba, kiyi hakuri da abinda nayi yanzun haka ana jiranki a cikin gidan ku, suna bukatar ki."
     Dai-dai ya cusa hancin motar shi cikin gidan mu,kamar yadda ya dauko ni. Cincirindon yan sanda da sojoji ne..
 Â
"Akan me zaka yaudare ni da."
   A hankali ya sauko daga motar, sannan yazo ya bude min kofar, ya riko hannuna. A hankali muke takawa, tare da rakiyar jami'an tsaro, juyawa yayi cikin damuwa yace.
"Ku bar bina! Idan ba haka ba, zan iya mata wani abu."
Jin haka yasa su, suka dakata da bin mu, a nutse ya nufi cikin gidan dani, Baabi na zaune da casbi a hannun shi.
   Ganin yadda yan uwan shi, suka zuba mana ido, nayi maza na koma bayan Jay cike da tsoron abinda zai faru.
      Â
    Hannuna rike da rigar shi.
"Toh Fatimah babu wanda ya isa ya dake ki, matukar ina tsaye da kafaffuna!"
"Kai d'an ta'adda! Waye ya tsaya maka?! Ka sace yarinyar mutane kaje kayi abinda yayi maka sannan kazo zakawa mutane rashin mutunci, kai gaka mara kunya tsagera! !"
   "A.s.p! Kaga laifin shi! Da ita ƙaruwar bata bishi ba, zai samu damar tsageranci ne?!"inji Yayar Baabi,
   Dariyar Da A.s.p yayi shi ya fusata Jay yaja hannun rigar shi sama, sannnan ya juya a fusace ya kaiwa Dan sandar wani mugun naushi, sai da haƙora biyu suka zubo, ya kuma d'ago shi yana nuna mishi yatsa!
     "Ban da kana sanye da rigar hukuma! Sai na karya kashin mukamikin ka, Idan kuma wani yayi subul da baka, ya ambaci yarinya mai daraja irin Fatimah da sunan karuwanci, sai na mishi abinda bazai manta dani ba. Ficce min da gani. An san yan sanda suna kare al'umma ce akan gaskiyar su, ba dan a ci zarafin su ba. Fita nace."
   Juyawa yayi ganin yadda nake shashekar kuka, riko hannuna yayi har gaban Baabi, ya tsaya sannan ya kalli yan uwan Baabi, zama yayi saman d'aya daga cikin kujerun falon, ya daura daya akan daya.
       Sannan ya ciro wasu takardun a cikin yar jakar da take rataye a gefen shi.
      Shiru yayi, tare da nazarta mutanen da suke falon, ina tsaye har zuwa lokacin.
"Wannan takardun na shaidan lafiyarta ce! Nayi iya bincike na ban gado dalilin da yasa take zubda jini ba. Ranka shi dad'e! Ni ban yi niyyar cutar da Yarka ba, kawai na gwada mata ne idan na saka abu a gaba na, duk duniya banda iyayena bana d'agawa kome kafa.
    Kafin yau ni ban iya magana ba, amma zuwan wancan mahaukaciyar ta mai dani magananne, ban san wani irin goyan naci kayiwa yar ka, ba amma dai duk mijin da ya aureta.