← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 72

Sashe 62

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          ...... Ranar da Jay ya dawo a dakin Husnah ya sauka, ban mu san meye ya faru ba, sai kawai ganin shi nayi ya hauro yana huci.
"Meye Husnah tayi muku da kuks hada ta da bayinki suka mata barazanar cewa zasu kasheta?"

Tashi nayi zan mishi magana, ya dakatar dani, haka yayi ta masifar shi, tsabar ya bani dariya, juya mishi  baya nayi, tare da fashewa da dariya. Fincikoni yayi tare da kallon fuskana.
"Ga mahaukaci nan ko?"

    Rike dariyar da nake nayi, sannan nace mishi.
"A'ah Hamma!"
Na faÉ—a ina dariya.
"Wai meye matsalar ki ne? Dariyar me kike min?"

"Dalla sake ni, kaje an baka aji garau, tare da tafiya birnin dad'i shine zaka zo kana min ihu, Ni babu abin da nayi mata, kuka babu abinda suka mata, idan baka yarda ba ka tambayi Munih!"

"Wacce Munih? Bayan an gaya min kun hade mata kai, keda Muniba, kuka ci mutuncinta."

    "Ka godewa Allah, iya mutuncinta muka ci fa." Na faɗa mishi ina kauda kaina, dan na fara jin haushin sa.
"Ni kike gayawa magana!"
"Toh kayi hakuri!"
Tsaki yayi min sannan ya bar d'akin, zan  ci qaniyar Husnah, dan  gidan su.

...... Fushi Jay ya dauka wai yazo yana magana na mai dashi dan iska, har da kai karana gurin Ummin, kirana tayi cikin fada wai na bata kunya, tayi ta min faÉ—a akan Jay. Haka bai mishi ba ya kuma hada ni da Mamah Sarah, ita kan bata bi bayan shi ba sai ma tambayar shi da tayi akan me ya faru, yana gaya mata, ta harare shi. Sannan tace masa.
'baka da hankali har yanzu, A madadin ka tara su kaji ta bakin kowa shine zaka yanke musu hukunci kai tsaye.

Ba ayin haka domin ba adalci bane, kuma zan je gidan naci mutuncin kowacce ce munafukar zan mata diban albarka."

      Fadar da tayi mishi ya sashi jin wani abu a ranshi har yake tuninanin dan ba ita ta haife shi ba, dan ko da tayi fadar sai da fuskar shi ta nuna bai gamsu da haka ba,  bayan ya bar gidan ne ya nufi namu..ya sami Munih da Husnah suna faɗa.

            Har suna tana gaya mata cewa.
"Kiyi fatan ki haihu lafiya! Sai kiyi tunanin fada akan mijin ba wai kina nan miji yana juya muku bayan.."
Shiru tayi naja hannun Munih, kawai bazata yarinyar nan ta fashe da kuka, tare da É—aukar yarta me sunan Mamah Sarah, zata fita daga gidan, kallon ta yayi. Sannan ya zuba mana ido..
"Nagode da kuka ci mutuncin Yarinyar da babu ruwanta."

"An cin kaci namu!" Inji Munih, dariya ya bani, nacewa Munih.
"Muje kici dan wanke, zan yanka miki har da gurji da ganyen latas."

    Juyawa yayi kamar wanda aka aiko shi kaina, zai mare ni. Sai kwashe shi aka yi ya zube a gurin.
"Kafin kayi fada dani, ka shirya da kyau."

Na rike hannu Munih muka haura sama, muna dariya, tun daga lokacin muka manna musu hauka, bawai na jone da Munih dan na cutar da mijina bane, a'a itama tana fada ne akan mijinta, dan haka ba wani shirin azo a gani bane, kawai abin da Bature yake fada nan ne (Fight for Survive) shine abin da muke tsakanin mu da Husnah, ita dan ta bakanta mu a gurin shi. Mu kuma sai muka hada har dashi muka bakanta musu, idan ya ga ina mishi dariya haushi yake ji yayi ta masifa kafin wani lokaci sun sussuta shi, ya zama wani mara hakuri.

Idan aka mishi a fada anan gidan kuma Husnah ta hada shi damu, ba zan mata wani mafarki da nayi ba akan shi, tun da na farka, na taka har dakin Husnah tana ganina ta fara kame kame, sawa nayi Zabba'u, ta daure min ita. Na shiga tambayar ta.
"Meye kuke mishi haka? Me ya same shi kuke sanya shi haushi."

"Ya rabu da kaka na! Idan na haka ba, iya haushi yake yi? Gaba hauka tuburan zaiyi."
" Saketa Zabba! Kika ce hauka tuburan ko?"

     Daga haka na fita a dakin hankalina a tashe, shiga d'akina nayi Zabba'u zata bini nace mata.
"Jeki!"
Juyawa tayi tare da cewa..
"Allah ya huci zuciyar ki!"

  Yana fita na zauna kamar mareniya.
"Ranki shi dad'e! Ciyar dashi suka yi, ta cikin gida can. Saboda nan an zuba nasa an kwashe, ki bamu izinin mu sanya ta tayi magana mana."

    A hankali na d'ago tare da zuba mata ido, sannan na sunkuyar da kai na kwalla na cika min ido.
"Bazlah kina ganin babu matsala."

   "A'ah akwai! Sai dai zaki yi hakuri ne, dan domin kayi nasara sai ka fadi a gaban abokan gaba! Domin ceton rayuwar shi! Dole ki fuskanci tozarci! Shine makarin...."

😪😓😭😭😭 Alqur'an labari ya sauya ku bani shawara Oum Nass na datse musu na gudu 😜🤣  naji ance Dambuje buje 🤨🙄
10/23/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *An san da Allah bai hana damo shan sanda ba*

Tunda na shiga cikin gidan, na sami Munih a tsaye, kallona tayi a sanyayye, har zan wuce ta rike alkyaba ta, had'iye yawun b'acin rai nayi sannan na juya na kalle ta.
"Na san ba zaku dawo ku same ni ba, Aanih ga shi abin cikina bai kai na Haihuwa ba da na bar miki, don Allah ki taya ni, niman gafaran Jay, kuma ki gaya mishi ina son shi sosai, Aanih domin kawo karshen wani labari dole sai an gina wani labari."
Saukowa nayi daga matakalar, na zuba mata ido, tausayi ta bani. Rike hannunta nayi muka wuce d'akinta, na shiga hada mata kayanta. Har na gama sannan muka fito tare ban iya mata magana ba, zan haura sama tace min.
"Kina jin haushina ko? Na san da haka ai, amma idan kika yi hakuri zaki ga rayuwar duniya babu kome a cikin shi sai hakuri da nasara, kafin mutane suyi nasara dole sai sun fad'i, kiji a ranki nasarar da kike son Jay dashi ne ya zo!"

Murmushi nayi sannan nace mata,
"Babu kome! Insha Allah zan dawo na same ki, kin sauka lafiya."
Daga haka na haura sama, ina gama abin da zanyi na dawo na shiga dakin shi na zubawa hotuna na, ido "yaushe aka yi su? Ta ina ya same su?" Abin mamaki bani da mai bani amsa, wasu a Calgary, wasu a Sokoto, wasu ban masan ta ina ya same su ba, yayi yan rubuce-rubuce a jikin shi a hankali na isa jikin wani wanda nayi ana ruwan sama a Calgary, ina rike da lema.
Kasan hoton ya rubuta wata yar karamar kalama.
*SAU DAYAWA BAKA SANIN WAYE ABOKIN RAYUWAR KA, SAI DALILI ME KARFI YA GIFTA KE ALKHAIRI CE AANIH BINT AARYAAN.*
A hankali na shafa rubutun ina kallon yadda yayi wasu rubuce-rubuce a gaban wasu, dama ina haukana ashe shi yafi ni haukacewa taya? Kwalla ce ta cika min ido, a hankali na gama hada kayan, idan nace zan karance wasu kalaman soyayya shaukin soyayyar shi ba zai barni na gama ba, haka na tattaro abun da zan iya na fito muka fita da cikin gidan, juyawa Munih tayi sannan ta kalli gidan, kwalla na zuba daga idanun ta. Rike hannunta nayi sannan fadawan da suke jiran mu, suka kwashi kayan mu. Muka nufi cikin gidan. Na sami Jay kamar yadda na barshi.

Jay ya gama da kowa da renin hankali, haka Najim ya kama shi zuwa mota, muka wuce katsina.
---
Bayan kwana uku, ban fahimci shiga da fitar shi ba, sai dai na lura da yau yake son barin Maiduguri, kallon shi nayi sannan nace mishi.

"Ba dai tafiya zaka yi ka barni ba?"
"Me kika gani?" Ya dawo min da tambayana,
Jim nayi sannan na kuma kalle shi nace mishi.
"Bana ganewa jikina ne, jina nake a daudaure!"

"Alhamdulillah! Baki fara shan ruwan addu'o'in bane, kuma kin ce kina son ki haihu, shine aka baki addu'a ko zamu dace da rahamar Ubangiji."

Daga haka yaja jakar kayan shi, zai fita.
"Tafiya zaka yi?"
"Aanih!" Ya kira suna na a gajiye da tambayar da nake mishi.
"Ki zauna zan dawo."
"Shikenan!"
Nace mishi,sannan ya fita da sauri. Tunda muka shigo gidan ake yawan sauka da sadaka, tare da bani addu'o'in, ban kawo kome ba amma na fahimci kodan cikin jikina ne da nake yawan jin naushin.

.kafib zuwan su Aanih Maiduguri, Jay ya dauki Munih ya kaita gidan Baba Magaji ya bata ruwan addu'o'in, har zasu fito sai yace Jay ya tsaya. Shine ta fita,
Kallon Jay yayi sannan yace mishi.
"Na samo mafita! Amma yana da hatsari!"
Cikinr zakuwa ya kalli Baba Magaji yana jiran me zai ce mishi.
"Ka nisanta Aanih da Daura, Insha Allah za'a dace, idan akayi addu'o'in ranar jumma'a, yau Litinin, gobe ya kamata kubar garin nan, amma kuma idan ita ta rayu kai zaka mutu! Idan kuma kai ka rayu ita da abu cikin sun zama fansa daga abinda aka yiwa Ziryana!"

Wani irin zufa ke karyo mishi, kafin yacewa Baba Magaji.
"Na amince?"
Da haka ya fito, daga cikin gidan suka dawo gidan su, Jay ya kasa barci domin sintiri yake tsakanin dakin shi da falo.

Shigowar Husnah dakin Munih yasata mik'ewa, tana kallon ta. Murmushi Husnah tayi, sannan ta ajiyewa Munih wani abu tace mata.
"Ranar jumma'a, zaki yi amfani dashi, domin raba Jay da Aanih. Idan kika ki kuma kece zaki rasa shi ne na rigana da na same shi!" Daga haka ta fita, Munih bata tab'a abun ba, kawai dai ta cigaba da kallon abun har gari yawaye, daga nan ta samu ta fita da abun zuwa gidan Baba Magaji.
Ta samu bayanan, dan haka ta dawo dashi, sannan ta maidawa Nanah abinta, yawan ganin Jay yana cikin damuwa yasata bin shi har falon shi ta zauna a kusada shi.
"Jay! Nasan nayi maka laifi amma ka gaya min halin da kake ciki ko zan iya taimaka maka?"
Chapter 62 · 0% Book details