← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 72

Sashe 57

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.... Kusan mutane goma, aka yi ta basu wahala, kuma sun kafe basu bane.

---
Tun ranar da ya dawo dani, nake yawan mafarkin gani cikin jajjayen kaya, hannuna da kafana cikin jini ysna zuba. Kaina kuwa wani irin kambun jan zinariya ce, me katon tagulla a gaban kambu.

Yau kam ina zaune naga suna jan wani mutum, duba shi nayi naga Jay ne, anje an saka kan shi a saman katako, wani kato ya d'aga adda zai sare shi na fasa kara na farka.

Cikin tsoro na duba naga karfe biyu na dare ne, a hankali na sauka naje nayi fitsari na dawo na kwanta, a sannu barci yayi gaba dani.

---
Washi gari ina fitowa Mamah Raihanah take gaya min abin dake faruwa. Yaki sauraron kowa . Dan haka ina son nace mata ko zamu tafi can ne ina tsoron kar ta ce na cika damuwa da shi. Juyawa nayi zan fita tace min.

"Fatimah! Jay yana bukatar me taimako, barcin da kike yaci ace kin farka, ki taimake mu mana."
.kallonta nayi sannan nace mata.
"Insha Allah, zan tsaya mishi."
Daga haka nasa kai zan fita tace min.
"Ki shirya muje."

Kaina a sunkuye na gyad'a mata kai, sannan na koma d'akina nayi wanka na shirya, bamu bar Abuja ba sai karfe hudu, koda muka iso yana can gidan horo yaki fitowa. Matsawa Najim nayi ya kai ni har bakin kofar shiga cikin gidan.

Da sauri na shiga, na same shi a tsaye ya juya musu baya, ana ta zane mutanen.
"Ku dakata!" Na faÉ—a musu.
"Ranka shi dad'e! Meye amfanin haka?" A fusace ya juyo min. Tare da zuba min ido, tattare alkyabar jikina nayi na isa gaban shi, cikin damuwa nace mishi..
"Kazo muje kaci abinci."

"Taya? Ya kike son nayi? Ya zanyi da jinin da ake zubdawa ba bisa ka'ida ba?" Ya faÉ—a min a tsawace.
"Amma bayyana fushin ka, kasawa ce! Taya zaka biyewa mutane kana aikata kuskure talakawan kane fa! Kuma mutanen ka da ka yarda dasu don Allah kazo muje, taya za'a ce babu wanda zai dakatar da Kai."

Rigima sosai muka yi kafin ya riko hannuna a fusace, ya nufi cikin gidan sarautar bai zame ko ina ba sai a fadar shi, ya juyar dani yana faÉ—in.
"Kalli kujeran da ake zubda jini sabida dashi, ki duba ki gani sabida wannan ake kashe masu yunkurin gaya min meke faruwa, ya kike so nayi?" Naushi ya kaiwa bango Ya fita hayacin sa, sai illata kan shi yake.

A tsorace na shiga ƙoƙarin rike shi, kamar mara hankali haka yayi ta jima kan shi ciwo, yana yi yana faɗin.

"Sun meye ke damun su? Meye nayi musu, da basu son a fadi gaskiya, yau sati Uku da dawowa daga gurin ki, kin san yadda nake rayuwa kuwa, abu daya ya gaggara, sun Kashe Ajiya. Sunce ni ne, jiya na shiga gurin Fulani Hasiyah sun bi sahu sun kasheta meye nayi musu da zafi?"

Ya faÉ—a da karfi, cikin wani irin tausayi shi, na mike a hankali na isa gurin da yake ta dukar bangon na riko hannun shi, zan hana shi, juyawar da zai yi ya ture ni, Allah ya takaita ban fadi akan kome ba sai akan karagar mulkin masarautan. Mik'ewa zanyi naji kamar an mai dani, cikin kujeran da karfin tsiya.

Wani abu da bazan iya cewa gashi ba, yana bin jikina da mugun gudu, wanda yafi na fitar numfashi.

A hankali mafarkan da nake yi, ya shiga dawo min. Ji wani abu nayi yana haura min saman kaina, a hankali nake jin kamar ba dai-dai nake ba, ihun mutane da Hayaniyar dawakai suna kara kusanto ni. A sannu nake jin duniyar tana juya min, kome yana zuwa min daki da daki. Tun daga wasu karni har zuwa karnin goma sha tara, izuwa yanzun da kome yake faruwa.(wato tun daga karnin Ziryana zuwa karnin kwarkwarah)

Karan bushe bushen algaitu, nake ji. Tare da ganguna, a hankali na bude idanuna da suka rine zuwa jini, wani irin dakiyar zuciya nake ji, bana jin kome akan kowa musamman da na bude idanu naga wasu irin mutane sunyi sahu a gabana. Sannan suka dunkule hannun su, suka saka a gefen kirjin su na dama.

Sannan suka zube a gabana alamun girmamawa.
"Muna maraba da Sarauniya Aanih Fatimah Khatoon! Sarauniya ta hudu daga cikin al'ummar bani Adam! Kuma Matar korarren Sarkin mu, Jalaludeen Jamaluddin! Muna jiran cewar ki, domin isar da umarnin ki! Ranki shi dad'e shekaru dari uku da ashirin muna jiranki."

Kallon su nayi, sannan na kalli yadda kayan jikina yayi ja, hannuna da kafana sun yi ja kamar an kwara min jini. A hankali aka kawo wani tire da wani abu lullube da jan mayafi, suna kawowa suka janye kambun jan zinariya ce, sannan wani dattijo ya dauki kambun da wata sandar tsafi ya daura min a kaina, a hankali kome na jikina yake komawa ja. Juyawar da zan yi naga Jay yana kallona da sauri ya tawo gani na a tsaye ya tun karo inda nake, cillar dashi suka yi zasu far mishi nace.
"Ku dakata!" Da sauri ya kuma dawowa ya rungume ni, tare da kallona yana fadin.
"Aanih lafiya kuwa?"

D'ago kaina nayi zan mishi magana naga kamar abin da ya faru ya b'ace min daga idanuna. A hankali jikina ya sake tare da zuɓewa a jikin shi ina mai da idanuna na rufe, da sauri ya dauke ni, dakyar muka bar fadan.

Gida ya kai ni, falon Mamah Sarah, ina sume. Nan suka shiga ƙoƙarin ganin na farka, koda na farkan ma da ciwon ciki tare da yunkurin amai, basu kawo kome a ransu ba, sai ma komawa da nayi ina Barci, shida Mamah Raihanah suka kaini daki.

Daga nan ya zauna a bakin gadon yana rike da hannuna.

Magayen mafarkan da nake ya hani barci, karshe wanda yafi munin shine wanda nayi ana kashe mutane, sannan Jay shine wanda ake bi zasu kashe shi, haka sukayi ta bin shi garin gudu ya isa gaban wani katon rami, sake biyo shi suka yi na fada ramin, shine suka juyo kaina. Zasu sare ni. Wasu irin halittu, suka far musu. Gurnanin halittun ne ya sani farkawa da mugun kara tare da rike kunne na, ina niman inda zan b'oya. Rungumo ni yayi cikin nutsuwa yana cewa.
"Fatimah ni ne, ki nutsu!" Ina ganin shine na kifa kaina a kirjin shi zuciya ta tana wani irin bugawa.

"Jay na gaji kullum sai nayi wasu irin mafarkai masu mugun ban tsoro, wallahi na cigaba da haka haukacewa zanyi na gaji!" Shafa bayana yayi sannan ya shiga rarrashina, yana gaya min nayi addu'o'in Insha Allah bazan kuma ba.
Alola ya raka ni nayi, sannan muka yi sallar dare, barci ne ya sa stfffffgtfgni dole na tashi, har asuba n .. Fitan

Da ya tafi masalaci, bayan an idar da sallah ne ya samu ne Baba Magaji da sauri.

"Ranka shi dad'e! Lafiya?"
Numfashi yaja sannan yace mishi.
"Wallahi Baba Fatima ce take wasu irin abubuwan masu ban mamaki, sannan tana yawan mafarkai masu firgitarwa jiya take ce min ta kusan haukacewa, sabida abinda idanunta suke gani cikin barcinta."

Shiru Baba Magaji yayi yana jinjina al'amarin, idan ya kintatta dai dai, Tabbas abin da bai faru a baya bane ya faru jiya da Aanih toh taya?

"Kaje kuzo da ita bayan sallar isha....
10/23/20, 10:05 AM - Ummi Tandama: *Birnin kura Akuya bata dilanci*

"Me kike nufi? Me zan yi musu!" Na tambayeta muryana yana rawa, had'iye yawu tayi sannan tace min.
"Sun san cewa makarin bame wahala bace, shi yasa suka zabi bashi yaci, sunyi haka ne dan ki kalubalence su, kuma haka shine suke bukata! Idan kika yi magana ban san me zai faru ba amma tabbas abin ba zai miki dad'i ba"

  Wani shiru ne ya gifta a tsakanin mu, haka yayi matukar tasiri sosai dan ya sanya zuciyar mu cikin damuwa da nazari, d'ago kai nayi na kalleta, sannan na mike.
"Meye kuke ganin ya dace nayi?"
Na tambayeta,
Murmushi tayi sannan tace min.
"Karki damu, ba zan iya saka ki ba ke da kanki zaki aikata hakan."
Shiru tayi sannan tace min, "ranki shi dad'e. Zan tafi masarauta.". Gyada mata kai nayi, kaina a sunkuye. Kwalla na kuma cika min ido, toh meye na kuka? Lokaci ne da zan kwaci mijina, daga halin da yake ciki. Lumshe idanun nayi sannan na bude shi. A hankali na fito daga dakin ina zaga ko ina, daga nesa na hango Mamah Nana.

    Ita da Husnah, banyi mamaki ba. Amma kuma meye suke a bayan gidan, a hankali na sauko daga sama na fita. Tare da bin hanyar da ba zai hada mu dasu ba, na d'an rabe da bango ina kallon su,kamar abu suke tsara wa.
                "Mamah ni fa na gaji wallahi Aanih fa kamar ba mutum ba, wani lokaci sai kiga kwarya idanunta yayi jajjur."
Murmushi tayi sannan tace mata.
"Karki damu! Baba Galadima yana shiri akanta, fatana dai yaci abincin yau."

    Ta mika mata wani kumshe idanuna yana kansu, murmushi nayi sanan na juya tare da barin gurin, bayan wani lokaci ina zaune a falo ta shigo, kamar ba zan mata magana ba, nace mata..
"Barka dai!"
Yake tayi min sannan tayi maza ta wuce, yar karamar dariya nayi.
            ---
Ina fakon ta da zaran tayi girki zata ajiye mishi sai na san dalilin da na zub da abincin, tun tana daukar haka a matsayin tsautsayi har ta fara zargin na fahimci shirin su, ganin haka ni kuma sai na kauda kai akanta.

               A hankali fitinar Jay yayi kamari, dan abu kadan za ayi mishi ya hau fada ko yayi zuciya, gabaki daya ya kwayance mana, yau yana zaune shi da ita Munih ta je sunyi fada da shi, tazo tana kuka. Take gaya min halin da take ciki, ga rashin mutunci da ya tsiro mana, sauka nayi na zuba mishi ido ina kallon yadda yake wasa da Maryam wacce ake kiranta Saddiqah.
Chapter 57 · 0% Book details