← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 72

Sashe 23

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hmmm!Abin kasuwa, na mai ciniki ne. Wasa farin girki, a shirye nake na kutsa cikin majalisar masarautar Daura na dakatar da d'an iskan da zai kawo min iyaka da mulkin masarautar." Ta faɗa tare da sake wata ƙatuwar huci.

"Ba zaki iya ba, sabida daga ranar da ya shiga masarautar muryan kowa zai sauka kasa, sannan shi kan shi zai kasance Sarkin da ba a tab'a samun irin shi ba tsawon karnika É—arai.

Shine sarkin da yake da gamayyar halittar Mutum da aljan! Kuma shine sarkin da zai jagoranci al'ummar alkarya guda biyu, soyayya da sadaukarwa itace zata kuma dakatar da wannan matsayi biyun da zai taka.

Da a ce uwar shi ta sami damar kusantar kujeran mulkin kasar dafur, toh da babu hatsabibiya irinta, shi kuma zai kwantatta wani kuskuren da ba kowa ya tab'a aikatawa ba.

Tabbas zai aikata! Kaunar da aka yi shi domin Ziryana da Fairo zai tabbata! Zai bar mata kambun wanda haka shine abu mafi daraja a duniyar aljanun! Kuma kuskuren ga rayuwarta, idan ta saka kambun zata iya karban sadaukarwa! Kuma zata iya bin sahun Ziryana da Fairo! Matukar ya fahimci hannunki a illatar mishi da ahalin shi.

Azzabar zata rub'anya, ina jin kamshin tozarci, ina jin kamshin mutuwar ki! Dan sai kin gwammace, mutuwar sau dari sama da rayuwa sau daya!

Amma ba zaki fahimci haka ba, sabida baki ga zahiri ba, baki ga abinda yake tunkaro ki ba, Magajin Izzah yana tafe nan da wani lokaci, zaki fahimci haka ne lokacin da kika tsinci kanki a gaban shi."

Wani irin zufa ke karyo mata kamar an watsa mata ruwan zafi, tsoro da tashin hankali, sun kamata. Bata san meye mafita ba. Amma dake zuciyar ta, ta gama kangarewa daga aikata laifukan son zuciya ya sata mikewa.

"Da baƙo da tukura, duk umbutawa ne. dan haka bazan sare daga cikin tafiya ta ba, na Barka lafiya " tana fadar hakan ta bar dakin baki daya.

Dukar kasar shi yayi tare da fashewa da dariya.
"Hasiyah! Kinyi gaggawar buÉ—ewa makiyarki dama..."

---
Daura..
"Jaamal! Insha Allah yaron zai dawo! Amma shima kaddarar shi, akwai ban tausayi, dan ba lallai bane. Ya sami soyayyar shi, koda ya samu akwai yuwar ya iya rasa kome na shi.

Jalal! Sarki ne da wasu suke jiran shi, kuma muma nan muke kiran shi, ban san yadda zan maka bayani ka Fahimta ba, amma an sami gamiyyar halittar shi.

Yaro karami amma ya taso tare da kadarorin Mahaifiyarshi, kayi hakuri zai dawo da kanshi amma kafin nan ka nime Najim ya tafi niman shi, ka kuma tabbatar da ya janyo hankalin shi gida.

Mahaifiyarsa tayi iyaka kokarinta na dakatar da wasu abubuwan, daga ciki kuwa har da aikin da ba nata ba, da ta rayu da duk wannan fitinar bai wanzu ba, da tun shekaru ashirin da bakwai kome ya zama tarihi, sau uku tana zuwa nan domin ta dakatar da matsalar da take bibiyar mijinta da kuma masarautar baki daya.

Sai dai abinda na gani ya sani kin gaya mata gaskiya. Domin na fahimci bazata iya kawo karshen rikicin masarautan ba, amma Insha Allah itace zata haifi wanda zai dakatar da abubuwan da yake faruwa.

Yarinyar tayi nisa, gurin son dakatar da kome, amma Allah bai nufa ba, sannan kayi ƙoƙarin shiryawa Najim tafiyar dan haka ne zai samar maka bayanin da kake bukata."

Shiru Kawu yayi tare da goge kwallar idanu shi, sannan yace.
"Baba, shima Jalal din rasa shi zanyi ? Kamar yadda na rasa Mahaifiyarshi"

Girgiza kai yayi, cikin damuwa yace..
"Bana tunanin haka! Amma tabbas shima zai rasa nasaba da yadda ka a rasa rayukan wasu! Idan ta kama abinda yake so ne tilas zai iya rasata.

Amma muna namu, Allah yana nashi, kuma nashi ne gaskiya. Amma tabbas zanen kaddarar ku, kusan guda ce....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

   *HAZAKA WRITER'S ASSO*
     (HWA)

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA TAKWAS.

"Karka damu, kome zai zo mana da sauki Insha Allah zamu tsaya da addu'a Allah yana sane da kome."

     Magana masu dad'i da ma'ana Baba Magaji yayi mishi, tare da nuna mishi kar ya takura kan shi akan lallai sai Jay ya dawo.

           ----
Calgary....

Yau ya cika kwana bakwai da dawowa, doguwar magana bai hada shi da kowa ba, asalima zai fita da sassafe zai kuma dawo sunyi barci. Duk suna lura da shi.

       Karfe sha biyu na dare, ya tura kofar falon ya shigo a hankali, tare da rufe kofar. Sannan ya cire takalmin shi, ya fara takawa a hankali kamar mara gaskiya.

      "Bamu san laifin mu ba? ranka shi dad'e! Shi yasa muka tsaya jiranka ko zaka dawo da wuri ka gaya mana me muka yi maka da zafi haka?"

         Cak ya tsaya bai kuma juya ba, kawai tsoro ne ya dabaibaye zuciyar shi, idanun shi suna cika da kwalla.

              "Mujaheed me muka maka da zafi?"  Mamah ta tambaye shi, a sanyayye ya juya tare da zuba mata ido, kafin ya sunkuyar da kan shi.

       "Na kasa fahimtar kome, na gaza gane waye ni? Taya zan iya fuskarta ku na tambaye ku wanene Ni? Ba zan iya tuna kome na rayuwa ta ba, amma Mamah ina jin waɗancan mutanen sune Ahalina!" Ya faɗa a sanyayye kamar zai fashe da kuka.

....cikin tsananin mamaki tare da kallon Juna miji da mata suka yi tare da isa gaban shi, suka rike hannun shi, suna cewa.
"Mujaheed! Gaya mana waye ya faÉ—a maka ba mune muka haife ka ba? Waye ya gaya maka?"

      Zama yayi cikin tashin hankali, sannan ya fara basu labarin abinda ya faru! Har zuwan shi nigeria.

Shiru suka yi kafin suka mike tare da ce mishi.
"Kaje ka kwanta, zamu duba Alamarin nan da wani lokaci."

  Girgiza kai yayi tare da zama a bakin matakalar benen yace.
"Hmmm! 'Yar bori, ba ta kallon bori. Ku fidda Ni cikin duhun damina mana"

         
     Takawa baban shi yayi sannan yace.
"Ba a hana ma bada rago, fata. Dan haka kaje kamar yadda muka ce! Domin gudu da wai-waiye shi ke kawo zargi"

              Mik'ewa yayi cikin nutsuwa bai kuma magana ba, amma tabbas ya fahimci abinda Baba yake nufi ba lallai bane yaji abinda yake bukata ba.

      .... Koda ya shiga cikin dakin shi, wanka yayi tare da alola, yana fitowa ya gabatar da sallar isha tare da nafilla, sannan ya kuma jima yana addu'a.

     Allah ya kawo mishi dauki cikin duhun da yake ciki. Sannan ya kwanta. Yana ta sake sake, har barci yayi gaba da shi.

         --- 3:38am.
"Jalal! Jalal!! Jalal!!!" Yaji ana kwala mishi kira, buÉ—e ido yayi a hankali yaga wannan matar ce da baya ganin fuskarta.

      Riko hannun shi tayi suka fita, a hankali tare da barin d'akin.
"Jayyyyy! Jayyyyy!!! Yaji ana kiran shi a wani daki can da kofar shi yake rufe da katon kubba(wato katon kwad'o)

          Kallon matar yayi cikin son yin magana kafin yace wani abu ta buɗe kofar me cike da haske, da sauri ya kare fuskar shi. 

Da gudu ya koma dakin da yake jin ana ihu ya buɗe, ganinta yayi cikin jini, a kwance. Cikin tashin ya shiga ƙoƙarin daukar ta sai ji yayi an rufe kofar d'akin, duk yadda yaso ya fita ya kasa.

                   Girgiza kanta yai tare dakyar ta bude ido tana ganin shi ta sake murmushi.
"A sauran abinda ya rage min, har yanzun baka sona!"

      Cikin wani irin tausayi ya d'agota,  ganin hannunta yayi sun yi baya, alamun ta rasu.
"Fatimah!!!" Ya kwala mata kira, kallon dakin yayi tare kallon Muniba da ta makale shi kamar zata shige jikin shi.

Yakince ta yayi da karfin tsiya, tare da kifa mata mari, sauka tayi da sauri, tana kallon shi.
"Fita!"
Babu shiri ta kwashe kayanta tayi waje.
 
Tashi yayi tare da yin alola, sannan ya gabatar da sallar nafilla, sannan ya zauna har zuwa lokacin sallar asuba.

    ---
Daura...
"Zaka iya, toh gashi ka Fatimah amma bari na kira mahaifinta naji."
Wayar shi ya ciro a cikin aljuhun rigar shi, ya danna Number Aaryaan sun jima suna magana sannan ya kalli Najim ya gaya mishi kome akan Jay.

      Da inda zai sake shi.
..... Sallama Najim yayi mishi sannan ya bar gidan.

                  ---
Yau ki manin sati biyu, rabona da sokoto, kallon yadda kome ke tafiya cikin wani irin yanayi ya sani jin kewar Jay!

   Ruwa ake tsugawa, kamar da bakin kwarya. Na nutse cikin bargo ina kuma tuna kwanakin da muka yi dashi a Damagaram, wani irin son shi da kuma kaunar shi suka kamani.

        Abubuwan da suka shiga tsakanin mu, ya fara dawo min. A hankali, kafin zuwa wani lokaci kasala da bukatar abokin rayuwa ya taso min, lumshe idanuna nayi cikin jin haushin abinda ya faru. Da ya saurari abinda yake raina ince da haka bai faru ba.

           ... Shi kallon wacce maza suka gama hawa da sauka akaina yake bayan ni nasan ba haka bane hatta iyayena kallon bazawarar da tasan mu'amala da namiji suke min.

      Shi yasa ma nake kokarin b'oye yanayin da nakan tsinci kai na, sabida gudun kar su min wata irin fahimta na daban.
Chapter 23 · 0% Book details