Sashe 50
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
  Zare madubin shi yayi cikin nutsuwa, sannan ya kura min ido. Duk yaga yadda na birkice da kuka yace min.
"Ranki shi dad'e, babu abin da ya dame shi, kawai dai muna zargin ya bugu ne a kan shi. Wanda bamu tabbata ba, sai zuwa nan da wani lokaci."
    A rikice na zuba mishi ido, kamar yadda yake kallona, sanan na sake kukan da nake ta hadiyewa nace.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Na zama annoba. A cikin al'umma, idan Jay ya mutu me zancewa mutane, da wani ido zan kalli iyayen shi, wato nice dai damuwa." Mik'ewa nayi na fito daga ofishin sa, na tsaya daga jikin tagar dakin da yake ina kallon yadda yake cikin halin rai kwai-kwai mutu kwai-kwai.
   "Kin shigo rayuwar shi, dan ki kashe shi, meye ribarki?....
     07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: _Kowa yaci ladan kuturu! Dole ya biya da yatsu_
Tafiya nake amma zuciyata cike da wani mugun tsoro, koda na shiga ji nake kamar zai fado kasa, haka na rike kirjina numfashina yana kaiwa da komowa, najima ina kiran sunan Allah kafin na samu sukuni, kasa kuka nayi, na zauna kwayam a dakin ina zare idanuna. Ina ji ina gani aka fara kome babu sanina.
   ... A hankali kome ya sauya, Jay bai damu dani ba, koda kuwa zamu hadu da juna kamar zamu buge juna matsawa yake ya bani hanya, wani lokaci haka zai ta kallona kamar yaga bakuwar fuska.
    .... Can fada kuwa, abin da basu tsammani ba, shine ya fara faruwa. Domin cikin iya taku tare da Najim suka shiga gwara kan mutane, musamman ajiyar da Sa'i, yayinda suka hade kan su da Sa'i, haka ya bawa Ajiyar haushi, har ta kai sun fara rigima a tsakanin su, rigimar da ta kai har a cikin fadar suna iya yi a gaban kowa.
      Idan suka yi fadawa ke musu magana tsawa su bari, sosai abin ya fara tab'a ahalin gidajen guda biyu. Yau ma Juma'a sun gama abin kunyar su a gabab Jay, yabi Sa'i har gida bayan sallar esha, bayan ya samu shiga Sa'i yace mishi.
"Jalal kai ne a gidana? ban kawo zaka zo ba, kai Nagode sosai."Â Cikin murmushi Jay yace.
"Haba Ranka shi dad'e gani nan, kawai nazo ne mu d'an zanta, na kuma baka hakuri da Abinda Ajiya yake maka ina ga zan dakatar da shi ma baki daya."
   Nan Jay ya shiga tona mishi magana a bakin shi, tare da nuna mishi yadda yake jin haushin rigimar da suke da Ajiya, sannan dole ya dakatar da Ajiya, ai wannan bayi bane. Sosai ya zage yana fada. Fir Sa'i yaki magana, sai da Jay yace mishi.
"Karka gayawa Ajiya nazo gurinka, dan wallahi zai iya jin haushinka, domin shi yaso na zama yaron shi naki yarda dashi na sabida ina Son zama da manyan masu hikima da hangen nesa."Â Nan ya shiga yabon yadda Sa'i yake, take kan shi ya fara kato yana jin shi wani ne.
"Wato idan kana niman munafuki ka sami Ajiya ka samu." Mik'ewa Jay yayi sannan yace mishi.
"Kayi hakuri zan wuce gida! Idan na sami lokaci zan kuma kawo maka ziyara." Daga haka ya fice ko dogon sallama bayi ba.
      Har ya fito daga cikin gidan, yazo gurin Najim ya ciro yar wayar shi, ya mikawa Najim sannan ya suka bar gidan. Shiru suka yi kafin Najim yace mishi.
"Kar muje gidan Ajiya! Ni na jima ina zargin su, amma dole sai ka shiga jikin su dukkan su biyun, dole ka hade kan ka dasu. Ana zaka kuma sanin abinda yake faruwa."
Sun jima suna tattaunawa, kafin suna iso gida, daga nan kowa ya kama gaban shi, dake dare yayi dan haka na yanke shawarar zama na jira shi ya gaya min meye nayi mishi ne?
Ina zaune har Allah ya kawo min shi, mik'ewa nayi tare da zuba mishi ido, murmushi nayi a raina nace.
"Abinda kake so yafi kome baka wahala." Da sauri yazo zai wuce nasha gaban shi, ina kallon shi kauda kan shi yayi sannan yace min.
"Malama bani hanya don Allah." Ya faÉ—a a uzurance!
"Jay meye nayi maka?"
"Baki min kome ba, kawai bana son ganinki ne kusa dani!" Ya faÉ—a min kwalla ne suka zubo min, nace mishi.
"Haka kawai kace min baka son gani na! Jay ko na maka wani laifin ne ban sani ba?" Saka kai yayi zai wuce na rike hannun rigar shi.
"Ka rufa min asiri kar duniya tayi min dariya! Ka gaya min meye laifina da Kuskure na!"
 Gyara tsayuwar shi yayi sannan ya zuba min ido, kafin yace min..
"Baki da matsalar kome! Sai dai kina w...!" Shiru yayi zai wuce..
"Me nake yi Jay?" Na tambaye shi a sanyayye.
"Wari kike min! Kuma wallahi bana son ganin ki dan kamar wata dodaniya nake ganinki, don Allah ki rabu dani!" Maganar shi kamar ruwan zafi ya watsa min, kallon shi nayi, a hankali na sake Mishi hannun rigar shi.
     Kasa gayawa kowa nayi, na shiga gayawa Allah kuka na, ina yin ibada ina azumi, a hankali. Na fara lalacewa, ina addu'o'in sosai.
   Amma karshe sai na fahimci, gabaki daya ne bana cikin duniyar shi, bana cikin tunanin shi bai damu dani ba.
Baya tunani na, sai na goben shi ga cikin Husnah da ya taso Sosai, nan rikicin da Munih take dani ya koma kan Husnah, tunda nice na tsare mata mijinta...
  Ban tab'a yunkurin gayawa wani ba, haka ya sa nake cikin damuwa, domin yadda na koma ko fita nayi cikin gidan sai Mamah Sarah ta tambaye ni ko ciki ne dani.
      ---
A wannan karon bayan sati biyu, Jay ya nufi gidan Ajiya domin kuwa ya shiga jikin tsofin sun a tunanin su yana bin su ne, sabida sun fi shi,basu san cewa wannan din bom ne da kan sa...
Haka ya gama shigewa jikin su, ana haka. Gwamna ya kawo wani abun cigaba, daura dan haka da aka zo kaddamar da abun ne Jay yace ba zai samu zuwa ba ya. Wakiltasu, na, yana sane ya hadu da aikin fidda wanda zai je taron . Aikuwa Sa'i yace shi yafi dacewa da zuwa. Ajiya yace bai iya ji ba. Karshe sai gashi suna shirin komawa yara ƙanana zasu daku da juna. Budar bakin Sa'i yacewa Ajiya.
"Munafuki me fuska biyu, ince kai ne kasaka a buge shi ranar! Kace kar a kashe shi?"
Cikin fusata Ajiya yace.
"Naji amma kai ne ya dauke shi shekara ashirin d'aya da suka wuce?"
"Eh naji ai Fulani Hasiyah ce ta sani tare da cewar wani wanda bamu sani ba, ashe bani kadai bane fitinanne.". Shiru Jay yayi yana kallon su, ba iya shi ba hatta sauran mutanen da suke fadar, sai da suka gama sannan suka fahimci abinda suka aikata.
   Take kunya ta kama su, tare da mik'ewa zasu bar fadar Jay yace musu.
"Ku kama su?" Mik'ewa yayi bai tsaya ba, sai cikin gidan. Inda ya sami Umma Rumanah kakar shi, zama yayi tare da zuba mata ido.
"Wacece Fulani Hasiyah?"
Kallon shi tayi sannan ta zuba mishi abinci ya fara ci, a hankali ya fara ci tana bashi labarin abinda ya faru, da kuma yadda Zuwan Jannart kome ya zama tarihi.
   Murmushi yake yana cin abincin sannan yace mata.
"Ai kuwa za a dawo da ita! In dai har tana can tana iya shirya yadda kome zai tafi mata dai-dai toh Tabbas ina bukatar ta a raye yazo ta koya min muna kisa.".
Duk yadda taso fahimtar dashi yakasa fahimtar ta, shi kawai zai dauko Fulani Hasiyah ne. Daga nan gidan su ya wuce, yaje ya sami Mamah Sarah, sun jima suna hira har ta kawo mishi batuna.
"Jay meke Damun Aanih? Naga ta lalace ne!" Shiru yayi sannan ya mai da kan shi inda yake kallo ya tabe baki yace mata.
"Tana da mugun hali, bata son zama a waje sai zaman daki kamar daddawa, ba dole mutum yayi wari ba."
Nan ya shiga yayi ta mita, wai din nayi mishi laifi." Hakuri ta bashi dan bata zata abun ya kai inta haka ba.
    Bayan ya gama hira ya koma cikin gidan shi. Yana zuwa ya sami tashin hankali, domin kuwa Husnah ya samu suna Fada da Munih, saura kadan su kaure da dambe.
Gata dama da cikin shi, kallon su yayi yaga da gaske fadan zasu yi sai ya wuce su bai kuma bin takan su ba, har ya kusan kulewa yace musu.
"Wallahi kuka barni na sako na same ku! Sai na lahira yafiku jin dad'i, kuyi kokarin tab'a min cikina ku gani sai na lalata musu rayuwa". Daga haka yayi wucewar shi bai kuma jin ko tarin su ba.
....yana isowa bakin kofa na ya kurwa kofar ido, cikin sanyin jiki, kafin ya saka kai ya wuce abun shi, dan ji yaƙe wani irin wari yana tasowa dole ya kauce dan zai iya kwara amai.
----
Yau da gobe bai bar kome ba, an dakatar da Sa'i da Ajiya, kuma Jay ya tura da sako Masarautan kwantagora a turo mishi da Fulani Hasiyah.