← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 72

Sashe 27

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          "Kana da ra'ayin aiki ne ko zaka..."

"Yallabai! Bako ne kamata yayi a bar shi ya tafi ya huta da iyayen shi sauran tambayar ya biyo baya."

    "Toh Rumanah!"
A hankali ya sallami kowa har Jay wanda Sarah da kanta ta shirya mishi abinci, bayan ya wuce dakin Kawu ya zauna Kawu ya dauko mishi hotunar Mahaifiyarshi. Tare da wasu abubuwan da yake mata hatta Littafin da ta bar Mishi.  Sannan ya kuma dawowa dashi wani daki dake can sama kusa da na Sarah ya bashi key din dakin.

       Sannan ya bude kofar ya shiga, kome na d'akin a shirye yake.... Ban daki ya shiga,

      .---
Buga cinyar shi Ajiya yayi cikin jin haushin kowa, yana huci kamar zai tashi sama.
"Amma!"

     "Me zaka ce Sa'i? Amma me? Bayan ka san Yaron nan takaddari ne, sannan mara jin magana ba ma zai tab'a kyale mu ba, bana rena kankantar allura."

     "Ajiya me kake son nayi bayan ka gaya maka nima ban san kome ba! Kawai naji labarin zai dawo ne, kuma."

"Kuma ka tura sakarkaru su tare su a hanyar zuwan su ko? Sabida an ce maka Wancan shadanin lauyan zai taso babu sanin abinda ya dace. Kaga bamu da lokacin da zamu ɓata, akan wannan al'amarin kawai kaje zan nime ka."

..jiki a mace sa'i ya mike tare da kad'e babban rigar shi, sanan  ya nufi hanyar fita.

                 ---
Abuja...
Zaune nake ina ƙoƙarin shan tea, kiran Hanisah ya shigo min.

"Ke yan mata! Ina Baabi da Ummin tare da Ammih na,"

     "Addah ba shi ya kawo ni ba, albishirinki"

     Juya ido nayi sannan nace.
"Katon farin goro!"

        "Wayyo Hamma Jay ya dawo Wallahi, yanzun haka yana daura."
           
Idanuna ne suka cika da kwalla, kamar zanyi kuka nace.
"Hanisah ina wasa dake ne?"

Dariya ta saka tare da cewa.
"Malama Addah kin fada soyayyar Hammana, ki min magana cikin da'a in ba haka ba, zan iya."

   Hawaye ne ya zubo min kashe wayar nayi tare da sake wani irin kuka, na rasa meke damuna akan shi.
            Bude data na nayi tare da duba Hanisah a Whatsp, na tura mata da cewa.
_Bani Number Ummu Rumanah!_
      *🤣🙄 akan me zan baki number ta? Kinga malama Addah kiyi hakuri kawai dan na lura*

            _😒😠 Ina wasa dake ne wai?_
Na tura mata,
               *😡😜🤭 Gayawa keya labarin! Bazan bada ba sai an bani cin hanci*

         _🙆🏽‍♀️🤦🏽‍♀� Abinda ya kashe kasar mu wannan cin amanar kasa ne! Bazan bada ba_

      *🙅🏼‍♀️Tun muna shaida juna nemi wacce zata baki ba dai Jikar Shehun Borno ba*

      _🤔🤔🤔 Yau naga abinda yafi zare tsayi, toh wallahi duk ranar da muka jone dashi Hammanki sai na gaya mishi hassadar da kike mishi dan kar ya sami kyakyawan mace irina_

           *Haba? 🙄🤣 Toh maza gaya mishi Addah ina son zoben hannunki nan, shi kawai nake so, sai na tura miki number*

    _🤦🏽‍♀� Kaico kin dage sai na baki cin hanci dai? Toh na baki amma ki duba yana nan a cikin dakina ban tawo dashi ba_

       Turo min Number tayi cikin sauri na ajiye shi a wayata, sannan na kuma kirata zuciyata tana bugawa, tana dauka murya na yana rawa nace.
"Hmm! Hmm! Dama ina son magana da Kanin ki ne"

      "Toh dan kashe bari na bashi yana falon Abban mu ne"

           Cikin sanyin jiki na kashe ina jin wani irin tsoro, yana kamani, can ta kira ki da sauri na .kashe kiran sannan na kirata,
"Gashi nan!"

      "Waye kuma Ummu?!"

        Naji muryan shi me matukar daɗi ta daki kunne na.
"Jayyyyy"
Sauke numfashi yayi, sannan yacewa Ummu.
"Kinga ban san me wayar ba jeki dashi!"

.kamar na fashe da kuka, na kashe kiran.

  Sake kirana tayi, cikin damuwa tace.
"Aanih kiyi hakuri, wai bai gane ki ba!"

     "Ba damuwa Rumah ya oga Khalid,"

  Dariya tayi sannan tace.
"Muna lafiya,kina Abuja amma baki son zuwa gidana, idan na dawo don Allah kizo"

  "Insha Allah, zan zo....
#Mai_Dambu
       
10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.....

*Kamar Kombo kamar kure!*

  "Insha Allah idan kin dawo zan shigo miki da Yardan Ubangiji."

        Haka tayi ta jana da hirar, ina kaucewa. Amma babu yadda na iya, har zuwa wani lokaci. Sannan muka yi sallama.

         Kifa fuskana nayi a tafin hannuna, na fashe da kuka, me mugun cin rai, sai da nayi ya ishe ni sannan na mike na wanke fuskana.

            Sannan na cigaba da zama a dakin dan nafi son zaman dakin sama da zaman waje.

  ---
Daura.
"Saraki! Baka da kirki amma kasan wacece ta kiraka, amma kake nunawa baka santa ba, Toh Aanih Fatimah!"

     Cigaba yayi da cin abincin shi ba tare da ya kalli inda take ba.
"Amma baki da hankali, mutum yana cin abinci kina cika shi da suturan banza." Inji Mama Sarah,

      "Kai Mama! Meye laifina dan na tuna mishi ita, Yau kina gani. Shine ta sanadin ta, da bata yi dalilin zuwan shi ba, da babu ku babu labarin shi.

      Mama ko da yaushe kamata yayi kina abu babu wani fifiko, sabida shi aka fasa auren ta, yau ta kira tayi mishi Jajjen ya dawo cikin dangin shi sai yaki kulata. Shegen girman kan shi nan zai janyo mishi asara wata rana."

              
    Tana gama fad'ar haka tasa kai zata fita, Mahaifin su ya shigo.
"Mamahna keda waye haka?"

 
   Cike da jin haushi, ta gaya mishi abinda ya faru.
"Amma Ni banga laifin Khatoon ba, dan yarinyar tayi kokari sosai. Kuma ina sha'awan ta shigo gidan nan a matsayin surukata!"

Da sauri ya d'ago kan shi yana kallon Abban shi kafin ya ajiye cokalin. Shiru yayi bai ce wani abu ba. Sai mik'ewar da yayi abin shi.

  ....... A cikin kwanaki ƙalilan ya saba da kowa, sannan Raihanah tazo daga Abuja ita da sauran yaranta har da Aliyah da yaran ta.
              "Yawwa Mamah don Allah kice Abban Jannart ya kara min kwanaki."

      "Ina ruwana, lokacin da kika zo kunyi shawara dani ne? Kawai kika bar min wannan janny da shegen farin idanun ta, tayi ta saka min kuka, dauketa kafin nayi mata."

      Shigowar Jay tare da Najim yasata zuba musu ido, cikin farin cikin da ta kasa b'oyewa.

Suna shigowa sai ga Jaamal da Aswad suma sun shigo, a hankali tace.
"Alhamdulillahi, naga wanan amintar yau gashi Ƴaƴan ku ma suma sun haɗe kan su. Allah ka jikan Jannart da Rahama, duk wannan aikinta ne."

    Shigowar Sarah tare da bayi mata dauke da manyan ture har uku, yasa ta zuba mata ido. Ta zauna a hankali bayan an ajiye tiren, kar'ar wayar Sarah yayi ta dauka tare da cewa.
"Alhamdulillahi barkanku da zuwa."

     Mik'ewa tayi tana gyara zaman Alkyabar ta, tana kallon Raihanah karama tace.
"Maamah tashi maza ga Ummin ku na sokoto sun iso, maza kuje ku gyara mata d'akin dake shashina, tare da ke Maman Kawa."

       Mik'ewa Aliyah tayi suka nufi shashin Sarah aka shiga gyara, duk sai jikin su yayi sanyi. Sakamakon abinda Jaamal ya faɗa.
"Yau shekaru talatin  da  bakwai, haduwa ta da Jannart! Ranar da bazan manta ba, mun fito cikin gari daga aikan Baba. Muka same su tana kuka, lokacin da muka tsaya Domin taimakon sun muka kalli juna."

   Murmushi yayi sannan ya zuba idanun shi akan kofar shigowa falon yana kallon Rahil tare da Hanisah da Jannart karama, buɗewa Jannart karama hannu yayi, ta shiga tafiya a hankali tana kallon kowa, a hankali ta shiga jikin shi.

        Ya mai da idanun shi kan Jikar shi ta fari itama Jannart ce ya kirata, ta mike da sauri. Sai Yar gurin Aliyah itama Jannart ce, ta isa jikin shi sannan ya shiga duba Jannart babba yar aurar shi.
"Aura!" Ya kira ta.
      Shigowa tayi tare da Fahad, sai nokewa take.
"Zo nan." Da sauri ta isa gare shi.

   Dukkan su, sunan mutum daya suka ci, kallon Rahil yayi cikin kulawa yace.
"Ina Yar Jannart?!"

    Murmushi tayi tana goge kwallar da ta cika mata idanu, tace.
"Tana abuja, gurin Kanwar Mahaifiyarta."

                   Da sauri ya zuba mata ido, kafin ya mai da idanun shi kan Jay wanda jikin shi yayi mugun sanyi kafin yace.
"Me yasa ta tafi can?"

       "Tun bayan fasa aurenta, Ikrama yace matukar tana Sokoto, zai ya tozarta ta."

       Da wani irin yanayi Jay ya kalle ta, bakin shi na rawa yace.
"Akan me?"
"Kan abin da kayi mata! Dauke ta da kayi ranar auren ta."

     Jan numfashi yayi tare da kau da kan shi, tare da mike yana me tauna bakin shi yace.
"Ita ce ta shirya ni kuma na gabatar." Daga haka ya bar falon.

"Kamar kumbo kamar kure! Halin uban halin d'an." Inji Mama Raihanah,

                "Toh itama tazo nan ayi bikin dawowar d'an uwanta da ita."
Chapter 27 · 0% Book details