← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 72

Sashe 30

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

            Murmushi yayi sannan yace,
"Alhamdulillahi, ya gida da jikin ki da fatan kin ji sauki ko?"
"Gyada mishi kai nayi,.ina murmushin takaici.
"Toh ki shiga tana cikin"
    
A sanyayye yayi wucewa ta,.ina ji a jikina ana bina da kallo, bayan na shige ya kalli abokin shi su cigaba da hirar su, ya ga yana bin bayana da ido.
"S. Yarima! Ya dai?"
Khalid ya tambayi abokin shi, lumshe idanunshi yayi wanda suke kamar yasha wani abu na maye.
             "Kayi shiru kuma? Bayan kana bani labarin." Inji Khalid,
"Wannan yarinyar daga wata masarauta take?" Tambayar yayi tare da kafe Khalid da ido, zuciyar shi tana wani irin rawa. Lumshe idanunshi yayi na wasu lokuta kafin ya bude ya kuma mai maita tambayar da yayiwa Khalid.

       "Yar sarkin sokoto ce!" Ya bashi amsa a takaice,
     Zubawa Khalid ido yayi sannan ya taɓe baki tare da shafa kan shi, sannan yace.
"Ok wacce ta gudu  ranar aurenta?"

Yayi tambayar tare da zubawa Khalid ido.
"Ba gudu tayi ba! Sace ta aka yi."

          Basar da zancen yayi kamar bai damu ba, ya cigaba da ta daddana wayar hannun shi.

            Can ya d'ago kan shi kamar me ciwon baki yace.
"Ina fatan ban mata tsufa ba? Don Allah Khalid gaya min gaskiya."

        Gyara zama khalid yayikafin yace.
"Ka tsufa dayawa! Kuma kaga zaka ba'a mata lokaci, kyanta ta sami wanda"

    Harara ya watsawa Khalid, sannan yace.
"Meye alaƙar ku da ita?"

     Nan ya gaya mishi yadda suke tare da kuma zumuncin da ya kullu a tsakanin su.

      Murmushi yayi sannan yace.
"Yarinyar bata da kauÉ—i da rawan kai, ina son mace me kamewa haka saboda duk inda kuka shiga bazata baka kunya ba!"

Nan yayi ta bayani tare da nunawa Khalid yadda Aanih ta kwanta mishi.

.....
   A cikin gidan kuwa tunda na isa,.muka yi sallah. Muka kuma tsinke da hira tare da shiga dakin girki, muka gama abincin rana sannan muka fito tare da shirya tabirin abinci.

             Ta shiga wanka ina zaune a d'akinta, can tana fitowa nima na fito, ta kimtsa kan ta.

            ..... Tana gamawa ta fito falon inda ta kira mijinta suka shigo da abokin shi, wanda yana shigowa ya zuba min ido, kamar zai cinye ni.  Sunkuyar da kaina nayi ina wasa da  bakin mayafina, har ta min magana. Koda na isa gurin abincin nace mata.
"Kinga zuba min na koma falo zanfi sakewa."

   Zuba min ido yayi sannan yacewa Khalid.
"Kaga nima zuba min na koma falon."

     Sake baki nayi ina kallon shi, b'ata rai yayi sannan ya kuma cigaba da latsa wayar hannu shi, tana gama zuba min sai da nace mata.
"Nifa abincin yayi min yawa kuma bana cin namar kaza, sabida kiba. Ganyen ma ya ishe ni."

    "Madam nima daga yau na ajiye cin namar kaza, sabida kar nayi kiba, zuba mana ganyen zamu ci a madadin nama," ya faɗa tare da tsume fuska, tana zuba min na mike.

             Shima kuwa ya mike tare muka dawo falon, zama nayi ina kallon ikon Allah. Yadda na zauna a haka shima yazo ya zauna, haushi ya bani ban san lokacin da nace mishi.
"Kai mayye ne?"

"Eh ni mayye ne! Amma sai da na ganki na fara maita, sabida kurwanki zata yi zaƙi"
  
Sai kuma naga rashin dacewar abinda na fada, na kuma cigaba da cin abincin ina wasa da wayata, shi kan bai iya cin abincin ba, sai ma zuba min ido da yayi yana murmushi. Kar'ar wayar Ummu yayi yana kusada ni, ina duba fuskar wayar naga tasa. Saraki!

  ... Tab'e baki nayi tare da mika mata wayar.
"Assalamun Alaikum! Barka dai Saraki"
Juyawa tayi tana kallona, kafin tace mishi.
"Bana son damuwa! Wani munafuki ne ya gaya maka tana gidana? Saraki ka raba kanka da wahala, dan qaniyarka baka ce baka yinta ba, toh ina ruwanka da ita."

               Can da taga hankalina ya fara zuwa kan ta, mik'ewa tayi ta shiga cikin dakin ta, nan suka yi ta faɗa da shi, kafin tafito ranta a b'ace, ina zaune naga sakon karta kwana.

                 _Kiyi gaggawar koran mutumin kusa dake! Domin wallahi zan dauki mataki akan shi_
  Sakon renin hankali na tura mishi kamar zai yi hauka, nace mishi.
*Ayya ban gane wake magana ba, ko Baabina kai ka canza layi*

  Nan ya shiga cikin tashin hankali tare da turo min sako yafi karfin goma, nima kuma yana isata na rufe shi baki daya, amma dake bai da zuciya ya kuma turo min sakon ta wayar Najim.

....karshe rufe wayar nayi baki daya, yayi ta kiran Ummu taki dauka karshe itama kashe wayar tayi itama tunda yace bayayi. Kuma muka rasa ta ina ne aka gaya mishi akwai wani a tare da mu.

  ...... Ban wani ci abincin ba, na  kai dakin girki, na rufe sannan nazo muka koma d'akinta nan muka shiga hira kamar ba gobe.

                  Anan take bani labarin abin da  Jay yayi mata, d'azun murmushi nayi sannan nace mata.
"Ayya ya kyautawa kan shi."

Ban kuma magana ba, har dai la'asar nayi sallah, muka d'an tab'a hira sannan na mike zan tafi.
      Nan muka fito falon, kamar wanda na ajiye shi ya jirani, ina fitowa ya mike shi ma, har waje suka rakomu, sannan ya nace min na shiga motar shi, dakyar dai na shiga.

       Kamar ba zan shiga ba, kawai Ummu tasani na shiga. Ina tuna hirar da muka yi da ita tana bani labarin wannan mayyen da ya addabi rayuwata yau ɗaya.

       ---
*Masarautar Zazzau*

Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma.

Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa, Zazzau wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci.

Zazzau Emirate

Yadda kalmar  ‘Zazzau� ta samo asali
Tushen wannan kalma ta ‘Zazzau� yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo�, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro.

A wani kaulin kuma ‘Zazzau� na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau�, wato ‘Mai Dauke da Zazzau�.

Asalin Kalmar Zariya
Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina

Bambancin Zazzau da Zariya
Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan kasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni.

Kafuwar Masarautar Zazzau

Mahaya dawakin Zazzau

A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu  ko rayuwa irin ta maguzanci. Kuma kaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin a kokarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo.

Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo�, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin musulunci.

Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Habe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama.

Kuma Zazzau na daya daga cikin kasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki.

Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi.

Wadanda suka biyo bayansa sun kafa biranen  mulkinsu ne a Kawari da Rikocci da Wuciciri da kuma Turunku, kafin su je Zariya.

Nohir ta auri wani bako, ta haifa masa da namiji, kuma aka sa wa dan suna dan Bakwa Turunku. Daga baya sunansa ya koma Bakwa Turunku, wanda ya gaji sarautar kawunsa Kawanissa a shekarar 1536.

Bakwa Turunku ya yi sarauta ne a garin Turunku, kuma har yanzu akwai sauran kufan masarautar ta Turunku a can kasan tsaunukan da suke shimfide  a yankin gabashin Zariya.

Kafuwar birnin Zariya
Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta.

Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537.  Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya.
Chapter 30 · 0% Book details