← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 72

Sashe 36

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    .....--
Kwanan Jay biyar a Maiduguri, har da sarautar Yariman mai Borno aka bashi, sannan ya dawo inda ya narkewa Abban shi akan gina mishi asibiti, da farko Jaamal yaki amma ganin sam Jay bai san meye ake kira da mulki ba, yasa Baba Sarki yace a barshi Nan da wani lokaci.

...... Zaune yake suna cin abinci, kamar wanda aka zage shi sai cika yake yana batsewa,  Kallon Juna Sarah da Jaamal suka yi kowa ya d'aga kafada, sanan suka ci gaba da cin abincin su rai a sake.
  Ture abincin yayi alamun ya koshi kuma ko rabi bai yi ba, ya zubawa Sarah Ido cikin nasara yace.
"Mama! Dama wancan Yarinyar aure zata yi?!" Kallon mamaki suke mishi tare da tambayar.
"Wacce Y'a kenan?"

    Shiru yayi abin shi bai kuma magana ba, har ya mike, Jaamal yace mishi.
"Ya zaka mai da kowa sa'anka!? Wannan rashin girmamawa ba daga cikin ahalin gidan mu bane ko na mahaifiyarka."

.mik'ewa Jaamal yayi yazo gaban shi ya tsaya suna fuskar ta juna.
"Jannart har ta koma ga mahaliccin ta, bata tab'a banzarta da Aminiyarta ba, duk wani abu da zata yi cikin mutunta Sarah. Jannart ta hakura da rayuwarta sabida Sarah kai har ka isa tayi maka magana kayi banza da Ita?

   Zan dauki kome amma ban da...."

        "Nagode sosai Kawu, ka nuna mishi bani ce na haife shi ba, ka nuna min cewa ba."
  D'aga mata hannu yayi sannan ya juya ya bar falon, a sanyayye ya bar falon har zai shige shashin sa, ya juya tare da cewa Jay.
"Idan har zaman ka zai janyo min fitina da Iyalina na roke ka da ka fita ka koma inda ka fito.

                 Ban haifi d'an da zai tozarta ni a gaban jama'a ba, kana da damar kayi kome, amma ban da wulakanta min mata na ba."

         Yana gama fadar haka ya wuce dakin shi, ya zauna a bakin gado tare da zubawa hoton Jannart ido, yana jin babu dadi a ran shi.

     ... Shiru Sarah tayi tana me share kwalla, sannan ta kalli yaron, tare da mika mishi hannu, dawowa yayi ya zauna a kujeran kusa da ita, yace.
"Kiyi hakuri Mama!"

"Babu komai!" Ta faÉ—a a sanyayye, dan ta lura miskilancin da Jay yake halayyar Jannart ce, rashin magana da kafiya da naci halin Jaamal ne.
"Wacce yarinya ce ake maganar ta?". Tab'e baki yayi sannan yace.
"Wancan yarinyar ta sokoto!"

     "Fatimah ce yarinyar? Jay ka cika renin hankali, Fatimah ba yarinya bace, ba kuma sa'arka bace, Sa'ar Aliyah ce, don ka ganta kamar lomar tuwo."

                   Shafa kan shi yayi kamar bai ji haushin ce mishi ba yarinya bace.
"Mamah yarinya ce ai."

"Hmm! Yayi maka kyau! Tunda ka haife ta ba?"
"Me yasa bazaki bata shawara ta hakura da auren ba."

Yana fadar haka ya mike yana dariya, sakamakon kallon da take mishi.
           "Toh bamu bata shawara ba sai ka dauki mataki ko?!" Ta gaya mishi a fusace, dan ya fara bata haushi.
"Afuwa! Amma ki duba dakyau, ta sanadin auren maza ke mutuwa me zai hana ta hakura, koda yake tsugune bata kare ba, tunda."
."amma me yasa da aka ce ka aureta kace baka sonta?" Ta tambaye shi,

    "Nifa bana da ra'ayin bazawara ce! Kawai nafi son wacce bata kai ashirin zuwa da daya, sunyi hankali, amma ita fa? Tab."

Baki sake Sarah ke kallon shi tana gyada kan ta, kafin tace mishi.
"Allah ya kawo maka sauki cikin abubuwan ka".

Dariya yayi, tare da barin shashinta, ya nufi hanyar da zata kai shi cikin gidan, haduwa suka yi da Husnah. Ta tsura mishi ido, babu kyaftawa tace.
"Yarima Jalal, Barka da maraici."
   Watsar da ita tayi tare da tsuke fuska, kamar bada shi take ba.

Shan gaban shi tayi tare da tsare hanyar da zai kai shi shi cikin gidan.

       "Yarima Jay! Meye laifina, ban fi guzuma da buzuwar da aka had'a ku b..."

Take mata kafa yayi tasaka kara me shegen karfi wanda yasaka dogaran da suke kofar farko lekowa ganin shugaban su yasa su juyawa da sauri,suna fadin.
"Hutawarka lafiya magajin garin daura!" Murmushin ban haushi yayi wanda ya kuma bashi damar mutsuke kafar Husnah tana kuka.

             "Buzuwar bata da matsala domin zata iya karban kanta."
D'ago fuskarta yayi wanda ya jike da kwalla, ya cigaba da cewa.
"Koda wasa kika tab'a Lu'lu'ah sai na baki mamaki."

    Daga haka yayi wucewar shi cikin gida, inda ya samu Kakar shi ta dama mishi fura tare da gasasun zabbi.

    Zama yayi ya sha sosai ya kuma ci zabbin.

    ---
Shiga shashin sa tayi taga Balkisu tana fitowa rai a b'ace.

      "Aikin banza kiba a kunne! Mun san kome, matar cushe." Inji Balkisu.

   Dariya Sarah tayi sannan tace.
"Banza ba shi kai zomo kasuwa. Ko baki fada min ba, nasan kwanan zancen Balkisu."

           "Oho dai koma me zaki ce sai dai ki fada. Kowa ya ga shamuwa da kwushinta ya ganta haka zaki ganin ki bar ni. Sannan shi Yarima da kike takama dashi ai ba d'anki bane? Dan haka ki bar ganin karenki ya kama kura, da sannu zan mai dake abin kwatance."

        "Asha Ramanme kada mai kibba. Allah daya gari banban, ranki shi dad'e, zan shige dan ina da abinyi."

               Daga haka tayi wucewarta, bata kuma tankawa ba.

          ---
"Ina lauya ne? Ban gane shi ba kwana biyu?"  Inji Baba Sarki.
Gyara zama Jay yayi sannan ya shiga matsawa kakan shi kafar shi da take ciwo.
"Wai yana da aiyuka ne."

         Daga haka ya cigaba da abin da yaƙe, har zuwa lokacin da Kakan yace Mishi ya isa.
....
"Jalal! Har yanzun kana kan bakanka baka son FaÉ—imah?"

   Lashe bakin shi yayi sannan ya zubawa kasa ido.
"Kaka Ni bana sonta ne? Kuma bazawara ce"

          Shiru falon yayi sakamakon bayanin da Jay yayi,
"Allah ya sa haka shine mafi alkhairi."

         .....
Ta same shi tsaye ya zubawa hoton Jannart.
"Kawu!" Ta kira sunan shi a hankali bayan ta rungume shi ta baya.

       Ajiyar zuciya ya sauke, tare da cewa.
"Na rasa inda Jalal ya dauko rashin hankali, Jannart bata da matsala, amma shi ga baki daya ba tarbiyyar mu yake nuna mana ba.

       Yayi min wannan rashin girmamawan a gaban mutane, naji ba dad'i, mu iyaye ne. Kome lalacewar muna bukatar mutumtaka, balle kuma yadda muka kasance ahalin babban gida."

        "Karka ga laifin shi banbancin al'adun da dabi'un mu ya sha banban da na shi, halayyar shi ba daya bane da wanda ya fito cikin babban gida.
Banda zanen kaddarar mu ta shafe shi ai da a cikin mu zai taso da irin namu AL'ADUN, toh Matsalar da aka samu ya taso da aladun wasu ne, Insha Allah bazai kuma ba."

       "Toh me yasa baya magana?" Ya tambaye ta a sanyayye.
"Amma inji ka ko? Domin kuwa ban ga wani rashin maganar shi, kai ma haka kake da wannan wulakancin, sannan kuma Janny. Itama ai ba tayar baya bace gurin miskilancin da zurfin ciki.

     Kai kuma naci da kafiya, shi yasa banyi mamaki ba da aka ce min ya sace Fatimah, domin kuwa tayi mishi laifi kuma ya rama."
     Juyawa yayi yana kallon fuskarta, tare da sake murmushi yana cewa.
"Wacce yarinya ce yake maganar ta?!"

...... Dariya tayi sannan ta gaya mishi ai da Fatimah yaƙe.

Zaro ido tayi waje, yana faÉ—in.
"Yau naga abin mamaki! Ba cewa yayi baya sonta ba??"

       Dariya tayi tana fadin.
"Kamar kumbo kamar kure!"

     .........
Yana fitowa daga cikin gidan, ya dauki wayar shi ya latsa can ya manna a kunnen shi.....
Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....
#Mai_Dambu
              
10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Kowa ya rena tsayuwar.... Wata ya hau ya gyara*

"Zan ga yadda za ayi da.."
Katse shi tayi cikin jin haushi.
"Ba zaka fita hanyata ba? Ba zaka dai min shishigi kwala kai a faranti ba"

"Ke da wa kike?".kashe wayar tayi abinta. Shafa fuskar shi yayi cikin jin dadi, ko babu kome yasa ta tayi magana, da muryanta irinta yaran nan. Tsaki yayi tare da fada a ran shi.
"Zai ga uban da zai aura mata wancan mutumin."

      Yaja tsaki tare da barin guri .

    ---
Tunda na shirya kayana, nake kallon su jikina yana kara sanyi, sabida faduwar gaban da nake ji. Haka na fito ina kallon Aunty Aina'uh, na kakaro murmushin dole.

                 "Yau kam zaki koma gida, sai murna kike kamar kin zauna akan ƙasa!" Inji Aina'uh,

Tab'e baki nayi tare da fita waje, ina faÉ—in.
"Baki kuma gani Nana gidan ki sai nazo da mijina."

     Zaro ido tayi waje, na d'aga mata gira, a hankali tayi min fatan Alkhairi, sannan na shiga mota, tunda muka isa Airport naga kamar ana bina, ban damu ba, kawai na tsinci kaina da turawa Saif sakon karta Kwana.

        _Bam san waye ba! Amma yana bina, kuma ban yarda da shi ba_
Chapter 36 · 0% Book details