← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 72

Sashe 64

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni daya na a cikin gidan babu kowa, haka na gama aikina na nufi ban daki nayi wanka sannan na fito, ganin shi nayi zaune ya zuba min ido, shi kan shi yayi kewata amma tsabar shariyar ta motsa, kauda kai yayi sannan ya cigaba da latsa wayar hannu shi, ina budar da gashi kaina, kawai naji an karb'a ya shiga busar min.
"A ina ka koyi gyaran gashi?"
Na tambaye shi, daukar mai yayi yana shafa min a kaina, a sannu Yaren shi ya shiga sauyawa. Karshen shariya dai ya tafi domin kamar zautacce haka ya koma min.

Sai da ya gamsu dani sannan ya koma gefe ya rungume ni yana shafa bayana, dan ma cikin jikina ya takura shi, amma ya samu nutsuwa sosai.
"Kin san me?"
"Sai ka faÉ—a!"
Wani shiru ne ya gifta a tsakanin mu, sannsn yace min.
"Wallahi naso kara aure!"
Wani abin naji ya tsaya min, a makoshi na shiga kokuwar cire numfashina sai da ya fahimci haka ya d'agani, tare da jinginar dani a allon gadon.
"Ban fa yi auren ba! Irin wannan kishin! Don Allah rufa min asiri babu aure a yanzun tunda wancan tsohon sarkin yana raye toh baki da matsala."

"Idan ya mutu ina da matsala kenan?" A rud'e ya mike tare da rikicewa, ya ma rasa yadda zai min bayani. Kafin ya min bayan yadda na yarda.

.... Yarinyar tana zuwa tayi ta min hauka da shirme, amma ban tab'a damuwa ba, saboda yarinya ce karama, kuma tana fama da fallin balaga, kanta hayaki yake, idan ta shigo kitchen ta dinga min bude bude.

Irin dai abun da mutum zai maka ya gundure ka, haka tayi ta min, ni kuma ina jin kunyarta.

---
Yau za a saka ranar bikin su Najim, na shirya da wuri, zan tafi gidan sai gada sanye da wata fitinannen gown, ta zuba kwalliya ni kuma ina daman taimaka mishi da links yana tsaye, kawai Yarinyar nan ta danno mana d'akin.

Juyawa nayi ma watsa mata harara, nace mata.
"Dan gidan ku, haka ake zuwa cikin gidan mutane? Fita idan na gama mishi..."

Rike hannuna yayi, na d'ago kai ina kallon shi, a hankali ya zare hannun ya kai tsakanin cikina zuwa k'uguna, tare da kara janyo ni jikin shi, cike da mamaki kawai naji bakin shi a saman nawa, wata irin ajiyar zuciya na sauke tare da rike kwalar rigarshi, muna kallon idanun juna.

..... Kafin kace me yarinyar ta gudu, dama yau ina lura dashi niman hanyar da zai turmushe ni yake sai ga Inam ta kawo mishi sauki, yau naga kayan haushi kamar zanyi kuka, bayana ciwo yake tun jiya kuma na gaya mishi, sai duba ni da yayi yace wai ba Haihuwa bace da sauransu, aikuwa yana gama ikon shi ciwo na danno min kai.

A daddafe na samu na shiga ban daki nayi tsarki, har shima ya shigo, ganin ina durkushe ban tashi ba ya taimaka min mik'ewar da zanyi kawai naji abu ya tawo min baƙi daya a hankali nace mishi.
"Bari ga wani abu zai sauko min!"
A hankali ya kyale ni aikuwa, na rarrumi kafar shi na matse gam, ina kiran sunan Allah, yana son ya taimaka min amma na rike shi.
"Yawwa yi nishi," ya faÉ—a min kamar wanda ya zage ni naji kalmar. Haka ina fama yana kira min nayi nishi, karshe da ya ishe ni nace mishi.
"Fita fita! Bana son ganinka, maza waje." Ture shi, a hankali ya riko ni,.muka fito dakin sannan ya dauko matashi ya jera min a bayan, kafin ya fita zuwa dakin shi.

.... .sai da ya gama shirya duk abinda zai bukata, sannan ya dawo dakin, yana kallona. Sai nayi yunkurin zan fita ya koma, yana dawowa ya shiga duba ni a hankali, yana cikin dubawa yaji na fara nishi, lokacin su Karama sun zo kirana wai nazo inji Mamah Raihanah. Zasu shigo ya daka musu tsawa suka juya da sauri.

Suna isa Karama tace.
"Hamma yace mu tafi!"
"A'a koran mu yayi,matar shi tana nish..."
Rufe mata baki Karama tayi, cikin jin haushi. Sannan ta bangaje ta tare da barin falon, dake bata da hankali sai da ta gaya musu abin da muka mata da kuma wanda suka ji.

Ran Mamah Sarah bai yi dadi ba, kawai jikinta ya bata babu lafiya dan haka ta mike tace musu.
"Bari na duba su, ko haihu ce!".
"Maryam ki kyale su karki ga abin da zai dame ki!"

"A'ah babu komai!"
Ta fita, da sauri. Tana shigowa gidan taji ina cewa.
"Jay ba zan iya ba,.karfina ya kare ni kam ba zan iya ba,.tunda Haihuwar ta gaggara ina ga abokin tafiya ce, Jay ka yafe min,"

... Duk jikin shi ya b'aci da jini, ga haihuwa amma babu hali ga abin cikin ya matso babu yadda zai fita, da sauri ta shigo d'akin cikin tashin hankali tace.
" Baka da hankali, haihuwar fari a gida, dan kana likita, waye ya gaya maka ana daukar wannan kasadar?"
Kiran Mamah Raihanah tayi a waya, suka tawo aka kamani zuwa asibitin shi ne cikin masarautan da aka kammala ginawa, saura bikin budewa, dai gashi nice na farko da za a fara dubani.

Cikin minti arba'in ya kira duk wasu masu aiki a babban asibitin daura, suka shigo aka fara duba ni, ana suka tabbatar mishi da cewa.
"Matar bazata iya Haihuwa ba, dan halittar ta irin taka ce, xata iya daukar ciki amma ba zata iya Haihuwa ba, idan na sauran matan ya kasance V ne, ita nata W ne, ka Fahimta ai tunda kai ma likitan ne shi ya janyo tsaiko amma Insha Allah yanzun zamu mata aikin."

Cikin sanyin jiki suke shiryawa, tare da niman karin kayan aiki, suna kuma tattaunawa akan aikin da zasu yi min, kafin wani lokaci yan uwan da abokan arziki sun cika asibitin, suna tattaunawa..akan aikin tare da tabbatar da dalilin da yasa a za min aikin, ina kwancen ya shigo min, zama yayi a hankali ya rike hannuna tare da sumbatar shi, yace min.
"Kamar yadda zasu shiga dake shekaru ashirin da takwas, haka suka shiga da matar arziki."

Jan hancin shi yayi, yana ƙoƙarin mai da kwallar shi, tare da jan numfashi, ya kuma rike hannun gam ya manna da fuskar shi, yana kallon yadda kwalla take zuba min, lumshe idanunshi yayi na wasu lokuta..kafin ya bude akai na, "tayi gwagwarmaya! Tayi faffutika, ta tsaya da taimakon namijin duniya, amma koda tafiyar tazo dab- da - dab, sai gashi ta sare, ta kasa."

...hawayen da yake tsarewa ne, ya shiga sauka, sosai sabida jikin shi ya gama sanyi, gani yake itama labarinta zai shafe gani yake kamar bazai kuma ganinta ba, zuciyar shi ta karaya ainun, yarda da saka ranshi ya raunana, a yau yana jin kamar ya cire rawanin sarautan da aka bashi ya ajiye musu, gani yake matukar bai gaya mata wacece ita a duniyar shi ba, ya tabbata asararre mara amfani a cikin al'ummar shi.

" Kin tab'a kallon sama? Kin tab'a tunanin yadda Ubangiji ya tsara taurarri? Da ace ina da wata dama,.na jingina ƙaddarata da na jingina na nime taki ƙaddaran ta shafe tawa, na gama sarewa daga sha'anin rayuwa! Na gama karaya daga cikin darasin rayuwa.

... A kowani mata ki, a kowani ɓangare. Rayuwata kara barazana take," yaja wani irin kuka me sanyi. Wanda sai ka matso kusa dashi zaka fahimci cewa kuka yake. Kara damke hannunta yayi cikin nashi.
"Ke baki san so ba? Baki san meye ake kira so ba! Kinyi hauka amma ni Soyayyarki anan yake!"
Ya taba kirjin shi da hannunta, yana zubda kwalla.
"Kinji yadda take bugawa,. Dama ke raine ga raina! Nasan haka ce ta sami ni, tun daga ranar da Hikmi yace min! Jay kana son Yarinyar nan, shi yasa ka hana su Abeel cutar da ita, shi yasa ka damu da kar wani ya tab'a ta! Jay marin da tayi maka hawai cikin k'iyayya bace, Akwai so da kuma sako? Ta isar maka da duniyarta..kayi ƙoƙarin gano ainiyin wacece ita? Idan kuma kayi kyakyawan katari, karka manta da wannan maganar! Kinji ko? Tun daga ranar da na ganki, kika dagula min lissafi, tun da na ganki ko rubutu nake sai an tab'a ni domin ke kawai zan ta zanawa, Ban tab'a kawowa ƙaddarar aure ta haɗa mu ba, sai da Baba sarki ya gaya min shekaru ashirin da daya, mun kasance inuwa d'aya!

Taya zan ga matar da aka bani ban da wayo na kasa kare kimarta! Taya zan bari wani ya kalli matar da aka bani tun ina shekara bakwai? Alamarin mu daga Ubangiji ne, shi ya haÉ—a mu ta hanyar da bamu zata ba, bayan iyayen mu, sun zo junan su, sai gashi muma mun. Kafa tarihi, mun kuma nunawa duniya cewa, Mu Æ´aÆ´an masoya ne! Soyayyar da iyayen mu basu gina ba, sai gashi ya ginu kan mu.

Koda na rasa A'isha da Husnah, kuka na ƙalilan ne, amma yau ina kuka ne dan kar rasa ki, Fatimah idan kika fito. Zan iya kiran kaina da Basarake, idan kika sare kamar yadda wancan matar tayi, tarihina ya shafe, duniyata ta wargaje. Mafarkina dake ya rushe, don Allah ki dawo gare ni, shirya sabon duniya sabon rayuwa."

Yana kallo aka shigo aka shirya ta, hawaye na zuba mata, bakinta amsa bututun numfashi babu halin magana, riko hannun shi tayi, sannan ya sarke karamin yatsar su, kamar masu kulla alqawari. Kallonta yayi sannan yace min.
"Alqawarin Allah gaskiya ce! Allah ya bada sa'a!"
A hankali suka turata aka fita da ita, dafe bangon dakin yayi tare da kallon tagar dake dakin kwalla na mishi wasan tsare.
Chapter 64 · 0% Book details