Sashe 42
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
     Ikrama ne ya sha gaban mu, da sauri nace.
"Ke tadda motar mu bar nan mahaukaci ne."
Sai da ta barshi ya kusan zuwa dab damu, kawai ta finciki motar da masifar gudu, ya kuma koma cikin nashi ya rufa mana.
 Da sauri na shiga lallubar Number Saif, ban san na fada kan Number Jay ba, kawai na shiga kiran shi.....
Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....
#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari.*
 "Saif! Ikrama ya biyo mu!" Na fada a rikice, muryana yana rawa,
    "Da alamu baki duba wanda kika kira ba ko?" Yana fadar haka ya kashe wayar.
Kafin nasan abin yi ya daki motar mu, wayar ta fadi nida Hanisah muka saka salati. Sai lallubar wayar nayi cikin tashin hankali, na kuma kiran Jay. Naji yana waya.
    ---
Yana zaune a dakin shi, dan sunan yayi aure ne, amma babu abinda ya dame shi da matan shi,  suma tsoron shi suke dan Munih ta tab'a gaya mishi magana akan ya ajiye su babu abin da yake tsinana musu. Shi kuma da Iskanci yayi mata alluran fitina.
     Tayi ta hauka yana kallon ta, sai da ta gama fita hayacinta, sannan ya mata wani alluran da ya Sata barcin dole, shi yanzun burin shi a gini mishi asibitin shi ne baya son kome sama da haka.
  Ya zaune Aanih ta kira shi, kamar ba zai dauka ba, dan yasan sarai yanzun zasu raba hali, da ita tunda daga shi har ita. Basu rena abun faɗa.
 Ganin kiran yaki karewa ne ya dauka tare da mannawa a kunnen shi, jin yadda take fada mishi halin da suke ciki sai da ya sanya shi tashi ya zaune. Sannan ya gaya mata ba Saif bane.
  Katse kiran yayi, sannan ya kira  Habib, sun jima suna magana. Kafin ya sashi ya had'a shi da mai girma Gwamnan Sokoton.
   "Barka dai yallabai!" Shiru yayi sannan yace.
"Ka kira yaron ka, kace mishi ya daina bin yarinyar nan ko kuma ni nasa a kwashe mishi kayan aikin shi baki daya, idan kuma kana ganin karya ne ka bani nan da awa daya zaka sami gawar d'anka!"
   Daga haka ya kashe wayar abin shi ko ta kan Aanih bai kuma bi ba.
     ***
Gudun da muke wanda ya kusan fitar damu garin sokoto, gashi yamma ta fara yi, ganin shi muka yi ya juya da gudu, muma kuma muka juya da gudun. Gida muka nufa.
   Tunda muka shiga, a tare muka sauke ajiyer zuciya, nace mata.
"Na yafe fita ko ina, Insha Allah."
     Har zan fita Hanisah tace min.
"Addah! Ki kira Hammah Jay kiyi mishi godiya dan nasan wannan aikin shine da taimakon Allah, ya kub'utar da mu."
   Murmushi nayi sannan na fito daga motar. A raina ina kara jin son shi, Jay kenan, ga dad'i ga tsiya.
     Koda muka shiga cikin gidan, kowaccen mu daki ta wuce, muka yi alola da sallah magarib, sai bayan isha na kira shi, kamar yadda nai tsammanin zai dauka. Sai jin muryan Munih nayi Allah ya taimaka ban yi magana ba, kome ta ganin a jikin sunan wayar ta fara zagina. Kashe kiran nayi ban kuma gigin kiran shi ba.
  .......
  Lokacin da da yazo yaga wayar shi a hannun Munih, kallonta yayi sannan ya kura mata ido. Dake bata da kunya ce mishi tayi.
"Wata karuwa kasa batun?!"
   Kallonta yayi sannan yace.
"Ruhi ga ruhina! Haske ga Haskena? Ko zaki hanani kula mata ne?" Ya gaya mata,
"Toh kuwa naci Ubanta? Domin na zage ta!" Ta gaya mishi tare da wular da wayar a bisa gadon shi.
     Bai damu da ita ba, har zata fita ta juya tana faɗin.
"Wallahi tallahi billahil azim, idan ka kuma auro wata mace cikin masarautan nan, nice ajalinta. Domin zan kasheta har lahira."
  ... Sake baki murmushi yayi sannan yace.
"Insha Allah, saura kwanaki ƙalilan ki samu amarya domin zanyi kuwa."
  ..nan tafita tana banbami, kallon wayar yayi yaga batul! Tsaki yayi tare da kiran wayar aka ce ana amfani da wayar.
    ---
Bikina ya kankama, dan ana ta hididdinmu, kamar yadda ake ina can an sanya ni a daki, ana ta dirka min kayan gyara, tun ina jin haushin su, har na hakura da shan su, domin kuwa na gaji da kayan gyaran.
....ranar Laraba, aka yar ƙwarya ƙwaryan walima, ranar Alhamis. Kuwa aka mana lalle. Kin bakin nayi nace a min ja.
  Sabida lokacin da Jay ya tafi dani, abu ba abu ba, zai ce jan lalle nan tayi min kyau.
Kawai sai na tsinci kaina da sawa a dauke ni a hoto da jan lallen na tura mishi tare da mishi godiyar da banyi ba, sannan na mishi fatan zama lafiya da matan shi.
  ..... Can ya kuma turo min sakon da cewa.
_Allah ya bada sa'a! Ya kuma baki zaman lafiya! Ya kuma tabbatar miki da auren nan jibi._
   A rikice, na kira shi yaki dauka ya turo min.
_Karki dame Ni don Allah! Kiyi aurenki mana, ni dai Allah ya tabbatar miki da Alkhairi ayi shi ranar da Saif_
   *Don Allah karka lalata min rayuwar aurena! Fatan Alkhairi kawai na tura maka da godiyar abin da kayi min*
 _Ni nace miki zan lalata miki aurenki ne? Kar ki min sharri mana_
 _ðŸ˜Don Allah kar ka min haka, wallahi zaka ja min magana a gurin dangin Mahaifina da Mahaifiyata_
  *Ai kuwa! Ni ban isa na lalata miki suna ba, kawai nayi abin da ya dace tunda gashi na miki fatan Alkhairi, amma kina zargina*
 _Nasan halinka! Na kuma san waye kai! A zamana da kai babu cutarwa! Amma kai_
  *Toh nagode daga abin arziki zaki bini da Sharri.*
Ya rufe wayar abin shi, shigowa Husnah tayi ta zauna a kusa da shi.
"Allah ya huci zuciyar Saraki!" Tace mishi,
"Don Allah jeki kaina yana ciwo! Bana son magana." Ya gaya mata.
     Bata damu ba, ta mike ta bar d'akin. Bin bayanta yayi da ido. Yarinyar tana da kawaici ba kamar Munih da take mishi kallon kamar zata cinye shi ba.
     ---
Yau Jumma'a, baƙin daga wasu sassa na jahar Najeriya suka fara zuwa, domin halartar daurin auren mu.
     Ina zaune Bayan sallar isha, ana min kwalliya, dan zamu tafi liyyafa, hankalina yana kan kwalliyar da ake min, tare da sauraron hirar da Hanisah suke da mai kwalliyar take cewa.
"Nifa turo min sako aka yi tare da kudi masu yawa, wai zanyiwa Yar Sarkin Musulmai kwalliyar bikinsu."
  "Ba kuma baki san shi ba? Zaki tawo?" Na tambayeta da sauri bayan na dakatar da.
"Gimbiya! Ni ai turo min sako aka yi ta email! Sannan aka ce na tura account dina, Ni kuma nayi kome, har da kuÉ—in jirgi aka biyan min. Kuma da na iso ya turo min da wancan kayan wai shi zaki saka. Ina ga angon ne!"
 Shiru nayi kafin na duba kayan, aikuwa munyi da Saif da na tura mishi kayan nake son sakawa yace ban fada Da wuri ba, ba zai samu saya min ba, Ni kuma ina jin kunyar Baabi, domin yana ta tambayana me nake bukata nace babu, sai gashi Saif din ya kuma cika min alqawarina."
 Kamar zan yi kuka na dubi kayan, doguwar riga ce, ruwan kore mai duhun shi wanda ake kira(royal green) sai tare yake zuwa da wasu yan kunne da sarkan su na azurfa wanda aka samu su Duwatsu masu daraja. Ji nayi kwalla ta cika min ido, lokacin da naga har da takalmin su dan iya rigar kawai na bukata, ina da wasu yan kunne da abin wuyan da zan saka.
      Dan nasan idan nace ya saya min gabaki daya zai ce a'a, kamar yadda nayi tunani haka ya faru, sai na share ban kuma cewa kome ba, ashe zai saya min.
  "Hanisah! Kin san lokacin da na gaya mishi cewa, ina son kayan ce min yayi bai da kuɗi amma kiga bazara da yayi min naji dad'i wallahi."
   "Ai kin gaya min. Ko kin manta ne. Kinga har da jakar kayan. Gaskiya Saif yayi Namijin ƙoƙari da ya saya miki kayan nan."
Haka na koma aka cigaba da min kwalliya na, sannan na tura mishi sakon.
_Nagode_
   Bayan an gama gyara min kwalliyar, aka shirya ni tsaf. Sannan muka fito, juyawa nayi naga Hanisah da Jannart karama na Katsina sun d'aga min rigar, ina saukowa daga shashin Ummi, wani irin kyau nake fitarwa, har falon kasa.
    Na samu yan uwan da kawayena na cikin masarautar suna jirana, kowa ya kalle ni sai yace masha Allah, sannan muka fita.
     A motar da Saif ya turo na shiga, ana gyara min zaman rigana. Kafin Hanisah ta shiga ya ja motar da gudu muka bar gurin..kallon shi nayi tare da lek'awa.
"Jay!!" Na daka mishi tsawa.
"Kar ki kuma min tsawa."
  Gabaki daya ya dauke ni daga inda ya dace, can wani wani otel ya kai ni. Ya kama mana daki, sannan yazo ya ja ni ya kai ni da farko naso taurin kai, kallona yayi sannnan yace min.
"Wallahi zan dauke ki cak, na shiga dake."