← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 72

Sashe 41

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Tunda naga sakon jikina yayi sanyi, na rasa yadda zan gaya mishi abin da min bai kyau min ba. Haka nayi shiru, can naji Ummi tana magana a hankali. Tare da bawa Baabi hakuri.

       Can ta kashe wayar sannan ta juyo gare Ni tace min.
"Meye amfanin abinda kika yiwa mutumin da zaki aura? Kin ja min Bankad'a  a cikin danginki. Sunce nice nake sanya ki abubuwa saboda d'an yar uwata meye yayi zafi da Mahaifinki yake min barazana akan aurena?"

  Shiru nayi tare da sunkuyar da kai na ƙasa, har muka isa sokoto.. Ummi waya take cikin harshen kanuri, ban san meke faruwa ba, amma naji Hanisah tana ce min.

        Baabi ya haɗa Ummi da Babanta ne shi yasa take ta magana tana faɗin gaskiya.. har muka shiga cikin gidan. Inda na samu yan uwan Baabi da Saif ana jiran mu, Ummi bata tsaya ba tace zata yi sallah idan zasu iya jiran mu toh.
   Tsoto ya kamani musamman da naga dangin mu baki d'aya, har da kakata Ummi.

        Bayan mun idar muka nufi inda ake tattaunawar,.ina bayan Ummi. Dake ranta ya b'aci sosai zama tayi tana kallon kowa a wajen tarr.

          "Assalamu alaikum jama'a Barkan ku, ba wani abu ya hada mu anan ba, sai magana akan abin kunyar da Fatimah take shirin aikatawa a cikin masarautan nan! Jiya da dare Saif ya kirani yana gaya min Ya kama Fatimah da D'an Sarkin daura da ita suna masha'ar su."

Ba iya Saif ba hatta ni sai da muka kalli Bana Annuwar, jikina ya dauki rawa sosai, kamar wacce aka jona min lantarki.

          Kallon Baabi nake kam shi a sunkuye, tare da kallon Saif shima na shi a sunkuye, wani irin kuka ne ya kwace min.  Na shiga rantse rantse.

        "Wallahi babu abinda ya haɗa Ni da Jay, asalima fada suka yi Saif ka fada musu gaskiya mana"

  ..shiru yayi, sannan Baba Annuwar ya shiga fadar wasu abubuwan masu daure kai da muni, wanda sam ban aikata ba, kallon Baabi nayi tare da son ganin shin ya yarda da abin da suka ce, amma yaki kallona.

       Nan kowa ya shiga fadar albarkacin bakin shi. Daga nan suka min cin mutuncin akan Jay. Juyawa da suka yi zasu zagi Jay Ummi tace musu.
"Baku isa ba! Baku haifu ba, yar ku dai ku mata fada amma duk wanda ya Kuskura ya zaga min d'a ko ya sake kazamar bakin shi akan Jalaludeen. Toh na rantse da Allah sai masarautan nan ta tashi tsaye da kafaffunta.

     Sannan kai Annuwar da kake maganar cewa Jay da Aanih suna masha'ar su, kai meye ribar tozarta d'an uwanka a gaban jama'a?

  Meye amfanin cin fuska haka, sabida yana da hakuri ko? Sabida baya fada baya kome duk abinda zaku mishi akan ta bazai tab'a cewa kome ba.

       Toh wallahi ku kiyayye abinda zai sanya shi yayi magana, kai kuma Saifullah zaka aureta ko ba zaka aureta ba?"

    Bakin shi na rawa yace.
"Zan aureta!"

      "Tashi kar na kuma ganin me kama da kai sai ranar auren ku" da sauri ya mike, yana fita ta shiga gayawa yan uwan mu magana, tare da cin mutuncin su. Kamar yadda suka yiwa Baabi, cikin izza tace musu.

"Ban da nima a cikin nima, haramun ne da sai an nimawa Jalaludeen auren yarku muga ta karshen tsiyar ku, kuma a biya sadakin da ba'a tab'a biyan wata mace da shi ba a cikin masarautan nan ba."

Korata tayi sannan ta zauna tayi musu wankin babbar riga, sannan ta bar falon abin ta, tana zuwa ta amshi wayar hannu na, tare da kashewa.

   Bayan tafiyar ta, nan suka shiga fadan abin da yayi musu, har da cewa.
"Matukar  Aanih ta auri yaron nan babu mu babu ita. Taje can su kara ta, dan bazata  ja mana faduwar daraja ba, daga masarautan Zazzau ba."

                      "Hmm! Ban san me yasa Rahil take takama ba, ban san me yasa take jin ita wata ce ba, ko ce mata aka yi muma sakarkaru ne da zata zauna yana gaya mana magana, son ranta wato d'an Yar uwanta shine abin burgewa ta kare laifin shi.

        Toh Wallahi duk abinda take ji zata samu, dan.."

Shiru tayi sakamakon haÉ—a ido da suka yi da Ummi tazo gurin Baabi.
"Hajiya kenan! Da fatan na barki da ɓaɓatu! Duk ba laifi bane, amma kin san kome lalacewar gawar Giwa tafi kwando tara,"
Gaban Baabih taje suka yi magana sannan ta d'ago kanta. Mik'ewa yayi sannan ya basu hakuri da abinda ya faru.

......
.  Haka da yayi musu ya masifar d'aga musu hankali, nan suka fita daga gidan. Aka shiga yawo damu a cikin Zuri'ar mu.

   Su lallai Baabih ya min fada tare da Ummi, shi kuma bai ce komi ba, sai ma zuba ido da yayi.

    Abun ya zama rikici da ya janyo aka hanamu shiga cikin gidan kakanmu, hatta wasu abubuwan an hanamu shigar cikin shi, balle kuma irin su Suna da wasu abun.

..... Matar kanin Mamana ta haihu dan haka nayi ta rokon Baabih ya bar ni naje, ni da Hanisah. Muka tafi mun je an karb'e mu hannu bibbiyu. Muna zaune a dakin Ayyah kakanta ta gurin Mahaifiyata.

Sabirah da Hoor, suka shigo y'ay'an maza muke dasu, Baban su ke bin Mamana, suna gani na suka fara dariya tare da faÉ—in.
"Makara! Kece a gidan sunan bayan an hanaku fita sabida ana gaya muku gaskiyar da baku so?"

      "Shi yasa naga ganku cikin sanin ya kamata, zancen manyan na manyan ne, mu yara ina ruwan mu."inji Hanisah, wata irin B'oyayyen ajiyar zuciya na sauke tunawa da nayi ita din gwana ce a masifa, gyara zama nayi tare da zuba musu ido.

         "Ke karki min rashin mutunci!" Inji Sabirah.

Budar bakin Hoor tace mata.
"Ai gado ba karambani bane, abinda aka sha a non..."

   "Ni rawa gadon mai kyau ce? Wasu tasu gadon har abada ba zasu iya sakewa da mutane ba, Ni Yanzun idan Uwata ya zo nan an santa da zafi yanayinta kenan, uwar wata kuwa sai dai kaga ana tattara kome saboda dabi'ar bera gareta."

      "Kan uban can! Ni kika zaga?"  Inji Hoor!
                "Bafa zagi nayi ba, wai ina gaya miki gadon da muka yi ne, ke baki fahimtar Yaren ne."

    Ai kuwa suka fita, can sai gasu tare da dangin Mahaifiyata, suka shigo zasu dake ta, kallon su tayi sannan ta girgiza kanta, tace musu.
"Ko kunya baku ji ba, kun dibo jiki zaku wulakantata sabida an gaya muku karya da Karerayi akan yar yar uwan ku, ko tausayin rashin uwa da bata dashi baku yi. Kun zauna akan abinda aka gaya muku sabida ranku yana sosuwa da SOYAYYA da ta samu a gurin mahaifinta.

       Da yau dukiya tana dawo da mutum tabbas Hassanah Ummina zamu bada duk abinda muka mallaka daga masarautan daura har zuwa masarautan shehun Borno, tun duniya tana kwance ahalin mu suke taka rawan gani a kasar nan.

          Dukiya mun gan shi mun kuma san shi, soyayyar da Zuri'ar mu takewa Hammah Jay, ya wuce yadda kuke tsammani..akan shi kuke tsanar Mahaifiyata? Sabida son kai da son zuciya, toh ku dake ni, sabida nice nayi magana ba mareniya ba.

Ko kunya baku ji ba, ku iyaye kuna fadan abubuwan da basu dace ba akan yan uwanku, wallahi matukar Fatima ta shiga cikin Zuri'ar mahaifiyata sai kun gane cewa shi mulki da dukiya al'amarin Ubangiji ne, yau muna kallon Hammah Jay a matsayin Mahaifiyarshi ce, sabida shi daya ta bari.

   Bamu da madadinta sai shi, mahaifiyarta ta rasu ta bar muku  ita, domin idan kun tuna da ita ga madadinta sai ku mata addu'a, amma sai gashi babu wacce kuka tsana sama da ita, da yau ana mutuwa a dawo baku ji kunyar Mameeh ta dawo ta ga abinda kukewa Yar ta ba. Burin ku sunan ta ya b'aci ace sabida rashin amana mahaifinta ya gaza bata tarbiyyar da ya dace. Ku ji tsoron Allah akan zalunci da kuka mata. Allah sai yabi mata hakkin ta, karku manta akwai rayuwa akwai mutuwa.".
Daga haka ta riko hannuna zata fita ta kalli Hoor tace mata.

"Kuskuren ki tab'a min ji kimata! Shi yasa na tab'a naki, ba kare bin damu!" Daga haka muka bar gidan. Ina kuka Allah yasa ita ke jan motar dan dukkan mu Baabi ya saka an koya mana mota.

             "Nagode kanwata Kawata." Na faɗa mata cikin kuka, girgiza kai tayi sannan ta cigaba da tuka mota tana faɗin.
"Ban san me yasa baki iya karban kanki hannun mutane ba, nifa ba zanyiwa kowa kuka ba"

       "Sabida kuka da gadon taurin zuciya ba! Kuna iya boye kaunar abinda kuke so ba! Da zaki ji yadda nake son D'an uwanki da sai kin tausaya min."

  "Mun sani mana, toh ya zamu yi da dangin Baabi? Kin san Ummi ma ba sha tayi a hannun su ba, kawai tafi su baki ne. Wallahi kaf dangin Ummi babu wanda baya mutuntaki, ana ganin darajarki fiye da yadda baki zata ba, ko jiya sai Da Kaka Bana ya tambayi Hammah Jay, akan da gaske yana sonki? Yaki bashi amsa.
.da ya bashi amsa toh ina gaya miki sisin gwal ne sadakin ki.

     .ko Ni bana tsammanin zan sami sadaki sisin gwal, amma ke naji har kowa ya gama hada kome na sadakinki.. amma mara kirkin nan ya ce baya sonki."

     Lumshe idanuna nayi sabida kalmar baya sona ba sabon kalma bace da zan ji haushinta, kalmar ta jima da zame min Alakakai. Bude idanu nayi lokacin da naji ta ja burki.
Chapter 41 · 0% Book details