← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 72

Sashe 69

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shima ai ya fidda kirjin ki, Ni kam na shiga uku, wai ke dama haka kike a hanaki sata ki koma sane, toh cire rigar ki saka riga da zanin can." Kwalla ce ta zubo min, dole na cire na saka. Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya matso kusa da ni, idanu shi akan kirjina.
"Wannan ma an mutu ba a tsira bane toh amma da sauki tunda ya.. kai ina zo nan daga yau zaki daina saka rigar mama masu fitar da mama nan!" Ya faÉ—a haka tare da fita.

   Har ya isa bakin kofar yace min.
"Kuma ki saka babban mayafi irin na juya, yawwa."

   Banza nayi dashi, a hankali na gama shiryawa na fito, muka karya, muna hira har kusan karfe  goma sannan muka dawo shiryawa, ina cikin shirya kayan ya shigo, a zafaffe ya juyar dani. Tare da bina da wasu zazzafar sumbata. Kamar zai cinye ni.

Tun ina kau da kai na, har na kasa na shiga biye mishi, kamar ba zamu bar juna ba, ban da ina hutun salla da babu abin da zai hana Jay karb'an hakkin shi domin ban tab'a ganin shi  cikin damuwa da kumar bukata irin na yau ba,

       Ture ni yayi gefe, tare da rike hannu na gam, ina mamakin abin da ya kawo mishi sauyi, lokaci guda. Dan haka wuta wuta ya fitar mana da kayan mu, dan yana fama da ruwan kashe gobara ne koda kuwa ta kwata ce zai iya watsawa.

.....idan har wutar zata mutu toh bukata ta biya shi kenan, dan haka muka shirya sai filin jirgin sama. Kamar zai yi hauka. Sabida yadda yake jin shi.

              --- karfe sha biyu muka sauka a Katsina, ba tare da ya gayawa Najim mun taso ba, haka ya kira. Murad karamin yaron Sarkin Katsina ya gaya mishi isowar mu, mota biyu aka turo suka kwashe mu zuwa daura

     .......
Karfe biyu yayi mana a cikin masarautan, ko cikin gidan bai shiga, ya nufi cikin gidan shi. Wani abu naji ya tsaya min a rai. Take na fara niman taimakon Allah.

   Kafin na shiga cikin gidan, na nemi kome na rasa sai ma nutsuwar da zuciyata ta samu, shi kuwa yana zuwa.

Ya taradda Husnah tana lalle, afujajjan ya kwace kome ya cire sannan yaja ta zuwa d'akin ta.

       Anan ya gurje ta son ran shi, tare da sauke nauyin da ya kwaso baki daya akan ta, ajiyar zuciya ya sauke, lokacin da ya fahimci ya sauke gajiyar shi akanta, yana kallon yadda take sauke numfashi. Tausayi ta bashi,  duk da haka yayi fatan ina ma Da Fatimah ce zata kasance haka da yafi kowa amfana da ita, Husnah ma ba laifi dan ta haɗu.

     Ban ɗakin ta ya shiga yayi wanka sannan ya fito abin shi ya shiryawa ya barta kwance, bayan yace mata.
"Ki tashi kiyi wanka bana son kazamta."

Yana fita,ya nufi cikin gidan su anan ya taradda ana ta hira yaushe gamo, zama yayi cike da kunya, dan alamun wasu abubuwan da yayi suna bayyana, kasa magana yayi duk da tambayar shi lafiyar shi da ake, Ni Ko ban kalle shi ba, dan na san juyen bakin mai yayi, dan haka ban koma sha'awan kallon inda yake ba balle na kula shi.

            Mik'ewa nayi na Barsu a falon na shiga dakin su qarama na rufe kaina na fashe da kuka, sai da nayi me isata sannan nayi kwanciya ta a d'akin.

  A gidan na wuni,naki yarda na koma gidan shi,ina jin shi yana kaiwa da komowa, akan mu tafi nace bazan koma ba yayi tafiyar shi.

           Har dakin ya biyo ni, ina kwance, juyar dani yayi tare da zubawa fuskana ido.

"Kinyi kuka? Me aka miki?" Wani kukan ne ya tawo min, na kuma rushewa da shi, ina yi ina shasheka, nace mishi.
"Don Allah yaushe zaka kaini gurin Baabina?"

Zuba min ido yayi sannan yace min.
"Babu rana! Balle wata. Indai dan haka kike kuka toh ki shirya domin kuka yanzun kika fara, kuma babu wanda ya isa ya juya ni baki isa ba, dan haka ki taso mu tafi ko raina ya b'aci na miki abinda baki zata ba. Tun dake baki da burin kome sai na sanya Ni a b'acin rai.

       Ban san me na miki kike aikata min wannan mugun abin ba,daga ki sanya ni cikin damuwa sai ki sanya ni cikin b'acin rai, abinda kananun yaran da kika samu basa min, shine ke bari ki min, wallahi baki isa ba.

Kin kasa, kuma babu wanda ya isa ya juya min baya a wannan lokacin. Ki fito ina jiranki."

Daga haka yayi ficcewar shi, kuka nake har da shasheka, ina ji ina gani bai damu da alamarina, ba, koda na fito na same shi suna magana da Mamah Sarah, tana mika mishi wata littafi, tana faÉ—in.
"Ina ga akwai wani a hannun Kawu, kuma tun shekarun baya naso buÉ—ewa, na kasa amma tace min a wani takarda dole sai na nimo Jakadiya Sahurah, ka duba yadda zaka bude Littafin yana da amfani.

..... Naso baka tuntuni sai wannan hatsarin ya faru, toh yanzun kuma naga kasami lafiya kuma ina jin Kawu yace wata me zuwa zasu baka sarautar bana son abubuwa su maka yawa, ba tare da ka duba ba."

  Amsa yayi tare da kallon bangon littafin an rubuta, kundin tarihina! Me kunshe da al'ajabi. Murmushi yayi sannan yacewa Mamah Sarah.
"Rubutun Ammih na, irin nawa ne. Tun ban karanta ba, naji ina kewarta."

Murmushi Mamah Sarah tayi, sannan ta goge kwallar da ya zubo mata, tace.
"Idan kuma ka karanta, sai kaji dama zata dawo ne, sabida Jannart tayi min kome!"

                Girgiza kai yayi sannan  yace mata.
"Toh Mamah zamu tafi."

     Daga haka Yasaka kai muka fita, tunda muka nufi gidan yake duba yadda zai bude Littafin, wanda aka rubuta cewa.
*Sunan Kawu da Nawa ne, mukulin bude littafin, sunar da ya bani ranar da muka rasa junar mu! Kalmomin masu Harafi bakwai*
Har muka shiga gidan, zama yayi a falo ya mika min, tare da cewa.
"Sunan Ammih da Abba! Ki hada ya baki ma'anar kuma kalmomi masu Harafi bakwai. Tayani dubawa."

Duk da ina jin haushin sa, amma haka muka raba dare muna duba  cikakken sunan da zamu bude Littafin.

    Wasa wasa muna gurin, har kusan asuba, sanan ya jani zuwa d'akina, anan muka kwana. Da asuba muka daura har kusan karfe ɗaya na rana babu karya ba.

         Abu kamar wasa sai da muka dauki kwanaki, dan Munih bata nan, ranar da Abba ya bata kuɗin suka yi tafiya da safe da zamu sauko, ina kallon Yadda ya gama shan wahala sannan. ya ajiye Littafin.

Yana me cewa.
"Wallahi na gaji, Littafin babu wani abun da zan iya buÉ—ewa."

      "Ka dai tuna da kyau! Babu mamaki tasan zaka san sunan ne ko kuma kaje ka tambayi Abba!"

         Aikuwa ya fita zuwa gidan Abba, ya sashi a gaba ya bashi daya kundin tarihin Maman shi, sannan ya bashi ya kuma makelewa Abba sai ya gaya mishi Mabudin, ya rasa meye kalmar da Zata bude littattafan guda biyu...
_Kuyi hakuri mura ya dame Ni_
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba*

"Kai amma abin yayi kyau,Yanzun aiki ne babba a gurin ki, kiyi hakuri da halin shi da duk wani abinda zai miki,  ki daina kuka domin shima zai yi duk abinda kika yi dashi zai cigaba hakuri kawai yi kina nuna mishi abin da ya dace a rayuwar shi."

Yayi bayani sosai, sannan ya kuma yi gargadi kar a kuskura abar shi yayi wani abin da zai shafi jima'i, dan bai cikin hankalin shi, kuma matukar aka ce zai yi jima'i da mace toh akwai matsala. Domin zuciyar shi  ba zata iya sarrafa sakonni Ƙwaƙwalwar shi ba. Dan haka ayi takatsantsar dashi. Idan kuma haka ya faru.

         Toh tabbas karfin shi da lafiyar shi zasu rubayya zuwa kashi tamanin cikin dari, kuma idan hakan ta faru.

   Likitan yayi bayani sosai, kafin ya fita. Kallona Abban shi yayi a raunane yace min.
"Ina ga zaki..."
"Ina ruwanka? Meye matsalar ka dasu? Fatimah zaki iya zama da Jalal?" Inji Baba Aswad,

Gyad'a mishi kai nayi, wasu siraran hawaye na zuba min, nace..
"Don Allah ya bar kirana da Mama!"
          Murmushi Baabina yayi sannan yace min.
"Ciwo ne ya mai da shi haka, Insha Allah ya warke bazai kuma kiranki Mama ba"

  Gyad'a kai nayi, shi kuwa ganin na daina kuka, yazo ya mannu da jikina tare da saka hannun shi a bakin shi, yana kallon su Baabi.

                 
          Gani yake kamar, sune suke bata min rai dan haka ya narke a jikina, kamar wani mara lafiya, karshe haka Baabi yayi min nasiha, sannan suka tafi.
"Maamah!"

Cikin shashekar kuka, na kalle shi.  Kwantar da kanshi yayi  a kafad'a na, yana shafa cikin shi. Jan hannuna yayi tare da daurawa akan cikin shi, janyewa nayi da sauri. Sakamakon jin gargasa har saman cikin shi..

       Zamewa nayi daga gadon, zan nima mishi abinci shima kuma ya sauka daga gadon, ina d'aga kafana yana saka nashi, ina juyawa kawai muka yi karo da shi.

            Shafa cikin shi yayi, tare da kallon abincin. Zama nayi a kujeran jikin gadon shi kuma na nuna mishi bakin gado, nokewa yayi. Naga ya fara kokarin zama akan cinyata. Zubur na mike tare da zare mishi idanu, na nuna mishi bakin gado.

         Kamar yadda nayi mishi haka yazo ya zauna tare da kwaɓe fuska zai min kuka, na shiga bashi abincin yana ci yana tura min baƙi.
Chapter 69 · 0% Book details