← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 72

Sashe 54

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi bai bar Najim Amsa ba, sabida zasu shiga cikin gidan, bayan sun shiga cikin gidan, aka gaisa sai raba idanu yake ko zai ganta, amma babu ita babu labarin ta, nan yayi ta kame kame, yana wasa da Jannart din Ummin shi, dan ta kure shi tace mishi.
"Ina Khatoon? Da fatan tana lafiya"
Dakyar ya iya amsawa da cewa,
"Tana lafiya! Tace a gaishe ku!" Yana fadar haka ya mike tare da cewa zasu wuce dama sun zo wani abu ne suka ratso nan, suka shiga shashin Baabi suka gaida shi sannan suka fita, a waje ya hadu da Muhammad kanin Aanih nan Jay ya ja shi da hira dan yana sane da Muhammad yacewa Noorie yana son irin ipad É—inta, har take gayawa Jay, yace idan ya samu lokaci zai saya mishi irin nata, aikuwa Mutumin Najim na kallon shi ya dauki Muhammad suka nufi cikin gari, acan yayi ta latsa Muhammad bayan ya saya mishi ipad din ya gaya mishi inda Addah take, nan kuwa yaron ya sake baki ya bashi labarin abinda yake ji abakin su Ummi, amma yacewa Jay.
"Hamma don Allah karka bari a san na gaya maka domin Ammihnmu hannunta zafi idan tana zaneka wallahi."

"Babu ma wanda zai ji sirrin mu." Haka ya dawo da yaron sannan Najim ya shiga motar Jay na tuka su, sai wani gudun gangancin yake musu, tunda Najim yaga haka ya fashe da dariya yana faÉ—in..
"Hala baka san wacece Mamah Raihanah ba ko? Allah ya bada sa'a!"
"Yayar Abbana ce ita! Sai dai nima muka baka san waye ni ba, Jini Insha Allah zan dawo maka, nan da karshen wata naje na kuma dauko Matana." Ya fada yana wani jin nishadi.

"Baka ce kome ba akan Fulani?" Najim ya tambaye shi.
"Bata da wani amfani sosai, nima ina jin ba dad'i akan riketa da nayi, amma wanda nake son ya fito yaki fitowa, shi yasa na ajiye ta, kuma naji wasu bayanai na ban mamaki, ashe kafin a haife ni Ammina tasha wahala a hannun Wani wai Shamaki tare da Dan shi Abdul, shi yasa nake son datse wanda yake saka su aiki." Shiru yayi..Najim yace mishi.
"Kasan wanda yake sasu kenan?" inji Najim.
"A'ah ban ce na san shi ba, kawai ina kintatta muryan wanda ya kirani da wayar Fahad."

"Jay! Anya baka aiki da mutanen boye!?" Inji Najim,
. Dariya yayi sannan ya isa tashan jirgin saman, ya fita da komin shi, sannan suka yi musabaha da Najim, kafin suka yi sallama.

...... Jirgin Abuja ya nima kuma Allah yasa aka samu, dan haka yana shiga ya a sauke ajiyar Zuciya, tare da fadin.
"Yan matan Saraki ga sarakinki nan zuwa gare ki." Ya sake wani kad'aitaccen murmushi, yana hango yadda zai yi wasan kura da yar tsohuwar matan shi.

.......
Sosai na sake amma bawai dan Jay baya raina bane, kawai ina jinjina yadda ya iya furtawa ya sake ni ne! Sai naji abin yayi min girma, a hankali na gama abin da zanyi na fito daga cikin dakin girkin, ina fitowa na dauki yar jakata tare da hijab dina na saka, na haura zama da sauri na gayawa Mamah zan tafi inda ta biya min ina koyan girki, dan tace.
"Ni gidana ba a zama babu abin yi, dan haka ki shiga makarantar koyan girki, zaki kara kwarewa." Kuma nasan gaskiya ta faÉ—a, dan Jay yana gaya min shi yana son abincin gargajiya da rana, da dare kuma ya samu tuwo kadan sai Y'ay'an itace,

Ina shiga na zauna jin tana dan faÉ—a, tana idarwa ta kalle ni, dan waya take.
"Har zaki tafi? Toh gashi nan Baba na ya baro Sokoto, kuma da Alamu niman ki yaje." Da sauri na dube ta, sai kuma nayi kasa da kai na.

"Ki tsaya kiyi mishi girki, gobe sai ki tafi, dan bazan bashi ke ba, sai na zabga mishi rashin mutunci, dan ko Ubanshi bai isa ya wulakanta mace ba balle shi.." Ban kuma ce mata kome ba, ta gaya min abin da zan mishi, nace toh.

Tun da na fara aiki, nake jin raina babu dad'i, kawai aikin nake har na kusan kammalawa, sannan naji muryan su,shi da Khalid, nan kuwa Mamah tayi mishi wulakancin da ya damu da kan shi, sannan tace.
"Kaci abinci kayi gaba akwai abokin Khalid yace yana sonta tunda ka saketa. Dake ka ga baiwa tana binka kana wulakanta ka, ka godewa Allah da gwiwata take ciwo, da ban san haka ba wallahi sai na baka kashi ka tambayi Ubanka shima ban kyale shi ba akan Jannart da Sarah balle kai dan banzan me idanun a tsakar ka, sai anyi magana kai ta hura hanci kai gaka mara kunya, toh ba zata koma ba kuma sai ka sake min ita na nima mata mijinta gangariya wanda ya fika a kome mara kunya, maza kaci abinci kabar min gidana"

Shiru yayi tare da saukar da kan shi, yayi ta lallashinta. Tare da gaya mata shi fa dama bai sakeni ba, kawai ya fadi haka ne ba tare da sanin shi ba, amma tayi mishi Uzuri idan ya kuma ta hukunta shi.
"Don Allah Mamah karki manta ni Maraya ne! Ki taimaka ki bani ita, wallahi bazaki kuma jin kan mu ba. Wallahi ba zan kuma b'ata miki rai ba. Don Allah ki taimaki takwaran baban naki!" Daukar matashin kujera tayi ta wulla mishi, tare da nuna shi da yatsa, sannan ta share shi. Karshe ma kin kula shi tayi tare da cigaba da abin da take yi, karshe bayan na gama jera abincin nima nayi wuccewa na d'akina na fada wanka, ina fitowa na sama shi a zaune a bakin gadon, tasowa yayi zai tab'a ni na kauce mishi.

"Amma dai kin san babu wanda baya kuskuren, sannan kuma da sani na bazan ce kina wari ba, wallahi haka ba zai kuma faru ba." Tab'e baki nayi na cigaba da gyara jikina, nan kuwa kamar Mayye yake manne min, kasa magana nayi bayan na ture shi.

"Don Allah ka kyale ni, ina dalilin wannan abin da kake min, kasan zaka dawo kana yar murya ka d'aga hannu zaka mare ni, ko Uban da ya haife ni bai dake ni ba, ga jaka an haifa maka. Toh don Allah ka rabu dani ai kace ka jima da sake ni don Allah ka bar ni na sami Yancina. Kaje Jay bana son ka, bana son ganin ka. Na gaji da damuwarka. Kayi min matan ka suyi min, ina zaune da kaine sabida kar Dangina su sami abin gorantawa a gare ni ashe kai da kanka zaka goranta, gaya min meye ban maka? Meye laifin na, ba zaka tab'a sona ba. Sabida ka fadi haka, don Allah ka sake min mara nayi fitsari, dan na hakura da gidanka koda zaka min kome ba zan koma ba"

Daga haka nayi wuccewa ta, na karasa shiryawa zan fita ya ci da zuci zai fita kallon shi nayi, sannan nace.
"Dama kazo rena min hankali ne, ba canzawa zaka yi ba! Dole na rabu da kai. Wallahi sai na baku mamaki da kanta zata dawo min dake kamar yadda ta dauke ko" A masifance ya juyo min jikin shi na rawa.

"Naga dan iskan da ya isa rab'anki domin kece numfashina. Wallahi zan aikata kome domin samunki a rayuwata! Ki daina gaya min abinda ya fito bakinki" ya faÉ—a min a hasale. Nima kuma na saka dariya nace..
"Sai kayi amma aure nayi shi na gama, ai bazawara sai bazawari, saurayi sai budurwa."

Sannan nayi ficewa na na bar shi a gurin. Har dare rigima muke dashi, washi gari nice na shirya musu abin karyawa ina gamawa kafin ya tashi nayi ficcewar makaranta. Amma abin dariya ina shiga motar naga ashe ba driven mu bane Jay ne.
"Tsaya na fita."
"Daga baya kenan, Yar nan. Zamu je yawon cin amarci ne, yar guzuma ta" Ya bawa motar wuta muka bar garin, bai tsaya a ko ina ba sai a suleja. Wani karamin otel ya kama duk da maganar da nake mishi tare da masifa, bai sanya ya kula ni, haka ya kama mana daki, a ciki. Ya tasani a gaba har dakin sannan ya rufe kofar.

"Ka mai dani gida! Bana son abin da kake min ka maida ni inda ka dauko ni."

Bai kula ni ba, har yayi wanka ya fito, sannan ya tawo gaba na, ya tsaya, tare da cewa..
"Yau ina son mu raba reni ne!"
Banza nayi dashi, ina cika ina batsewa, Jay ya sani a gaba tare da tsara ni, tun ina kin biye mishi, har na tafi baki É—aya, sai da muka zube a gado na fahimci, kuskuren biye mishi, domin ya shagaltar dani da Soyayyar shi ne shiga rai.

Hmmm! Wani kayan sai Amale, babban goro sai magogin karfe, gadon hari sai fana, ramin kura sai Ƴaƴanta, a yau Jay ya isa inda bai tab'a tsammanin ba, bai tab'a kawowa zai ji haka nake ba, bai tab'a tunanin cewa Ni din Casssssss nake, sai da ya dagargaje ni dan bakin mugunta ya zata bazawarar ce da gaske mutumin yayi ta wasan kura dani, bai kyale ni ba sai da ya sami nutsuwa fiyye da tunanin shi, a nan ne ya juya yana kallon fuskana, cikin tausayawa, kamar ya mai dani cikin jikin shi ya boye ni, dan wallahi tun da yake zai iya cewa, hmm! Babu wacce yaji ya dauki dogon zango da ita kamar ni, sai kallon fuskana yake wanda ya haɗa gumi sosai. Tare da wasu siraran kwalla da nake fitarwa.

"Gaya min taya haka ya kasance?" Ban bude ido ba balle Yasaka ran zan mishi magana, sai ma kauda kai da nayi, matsa min yayi da tambayoyi kuma yana makale dani, karshe da ya bani haushi na fashe da kuka, ina ture shi, da sauri ya rabu dani, tare da bani hakuri. Abun da Jay ba yayi ya baka hakuri tab, sai gashi rana daya Ubangiji ya sauya kome.

Duk da yana juna a ran shi, ya gaza furta yanayin da yake ji sai kallona da yake yi kamar zai mai dani cikin jikin, a hankali na sauko daga gadon, na nufi ban daki, ina jin abu na sauka a tsakanin kafana.
Chapter 54 · 0% Book details