← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 72

Sashe 67

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka na mike zan bar gurin, kamar wacce aka yasha a barci haka na bude idanuna akan wayata da take haske. Dauka nayi tare da sakawa a kunne.
"Aanih! Kamar yadda kike ce Habu ya amshi zoben shi da wannan igiyar, toh ku kai shi inda zai baku bayani a nutse domin kuwa yana cewa zai magana a gurin sai gawar shi, Habu yayi muku illa sosai, domin shi ya karb'owa Fulani Hasiyah maganin da matan Abba ba zasu tab'a haihuwa ba.

.... Yana da wasu abubuwan da zai fada muku, idan kuka kaishe karku ce yayi bayani zai yi da kanshi."

Kashe kiran nayi na kwanta, ina jin babu dadi, kawai na share ina kwancen har aka kira sallah, shiru nayi na wani lokaci kafin na nufi ban daki na duba jikina har yanzun da akwai jinin, madafi na wuce nayi mishi abinci, dan na san gobe zai koma dakin Husnah, wacce da muke kirki da ita, yanzun kuwa kaf kafa take dani, Bata son mu hadu ma. Uwar marasa mutunci ne dai idan ta ganni koda zata ji wani abu sai ta harare ni.

---
Ina idarwa yana shigowa gidan, a hankali na gama kome na fito na same shi ya fito wanka, a d'akina hade hannuna nayi a kirji nace mishi.
"Yallabai sarki! Baka da daki ne?"

"Ina dashi amma ana mata na nake son yin uzurina ko zaki hanani ne?" Ya kafe ni da idanu.

"Gaskiya ana shiga hakkina, kuma wallahi kayi na karshe ka zauna a dakinka duk macen da take da bukatar ka ta bika ba kai zaka bi mace ba, meye amfanin turakar, haka kawai a hanani sukuni, ni gidan ma yayi min kaÉ—an, Yawwa domin d'akina na Dafur ya ci uban wannan da nake ciki sau biyar, kar na kuma ganin kafarka, kuma ka jawa matan ka kune, wallahi na kuma ganin wata ta turo min shirme zata gayawa makotan su, Babu abin da ya dame ni.
Mata zata ji a jikinta ne, kuma kuma ka dai ja musu kunne."

Cike da Mamaki yake kallona sannan ya sauke ajiyar zuciya yace min..
"A takaice ki ce min kar na sake zuwa miki daki, bawai ki kawo dogon magana ba, tunda bani da gata shi kenan..🤦🏽‍♀� kuyi hakuri gaskiya na gama gajiya
10/23/20, 10:21 AM - Ummi Tandama: *A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye.*

"Ka kyale ni, bana son damuwa tunda ni ban ya kula da kai ba, kaje ka sami matan ka, tun...."

          Murza hannuna yayi a hankali, tare da d'ago kaina.
"Ke kam! Yaushe zaki daina kukan banza ne? Dube ki katuwa, dake kike kuka, idan kika cigaba, zan ga yadda zamu yi dake, nan gaba. Toh ba zan kuma maganar su ba, saboda karki yi min yaji na rasa inda zan fake."

Kifa kaina nayi ina jan majina,  murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Tun haduwar mu nake jin na zama magananne! Toh meye na jan majina kuma."

        Shigowar Abba da sallama, da sauri ya juya abin shi, yana murmushi. Kunya ta sani saurin kwace kaina. Na shiga ban daki da sauri. Hannun shi biyu yakai wuyar shi tare da sakala hannun, ya sake murmushi, me cike da jin wani irin farin ciki.

    Sannan ya buga min kofa yana fad'in.
"Zaki fito ko na shigo" da sauri na bude kofar ina zare idanuna, a hankali ya fincikoni, kirjin shi yana kallon yadda nake murmushi.
"Kina da matsala!"  Kiciniyar kwace kaina.
"Toh kuma! Me aka yi? Kina son kirkiran rikici."

Cikin jin haushi nace.
"Kace ina da matsala!"

Waje yayi da idanun shi, sannan yace.
"Akan wannan al'amarin shine kike fushi? Toh ranki shi dad'e, ba zan kuma ba."

              Juyawa nayi zan koma bakin kofar dan na san Abban shi yana gurin, yayi maza ya dawo dani jikin shi.
"Hala kun hada danganta da mage ko?"
    Gyara rikon yayi sannan yace.
"Tayu kece magen ba!"

"Saraki! Abba yana waje fa."
Sako kan shi yayi kafada na, tare da faÉ—in.
"Ina zan sani, kin same Yaro qarami kin sanya shi a lungu kina lugwaigwaita shi!"

   "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Allah ya shirya ka." Na saka kai na fice bayan na saka hijab dina, baya asibitin baki daya, har zan shiga wani mutum ya mika min wata jaka.
"Inji mutumin da kuke zaman jinya dashi, wai na baki." Amsa nayi sannan na duba, jakat akwai kudi sannan yar takarda.

Ciro takardan nayi sannan na bude..
_Duk wani abun da kike bukata daga ke har shi, zaki iya amfani dashi kafin ku dawo, sannan ki gaida min shi zan koma tunda jikin yayi sauki._

          . Sarki Jaamal... Kunya ce ta kama ni, ina shiga dakin ya dauke ni cak ta baya, zuɓewa kayan yayi, na saka yar karamar kara. Dariya yayi sannan yace min.
"Matsoraciya kawai! Ina Abbana?"
       Juyawa nayi na kalle shi, kafin na sami damar bashi amsa, nace.
"Ya koma gida."
"Allah Sarki, Abbana kamar kasan Yaron ka yana son girma". Girgiza kai nayi na barci a gurin,
Hannun shi ya saka a baki, kamar me nazari kafin yace.
"Abba yace min lokacin da ban da lafiya binki nake kamar jeka"

Juyawa nayi tare da zuba mishi ido, sannan na juya na cigaba da abinda nake yi, a sannu ya tako, yana zuwa bayana kawai ya kwanta a bayan, ban san lokacin da na sake kwalbar hannuna akan kafana ba, da sauri na daka tsalle. Ina yarfe hannu na. Idanuna suna cika kwalla.

           Cak naji yayi sama dani, a bakin gadon ya ajiye ni. Sannan ya rike kafar a tafin hannun shi, yana murza min, cikin nutsuwa.  A hankali yake min tafiyar tsutsa, kallon shi nayi zan kwace kafana ya rike gam.

                     "Don Allah! Ka bari."
Na faÉ—a muryana yana rawa, sake kafar yayi a hankali ya taso inda nake, zai had'a bakin mu na kauda kaina. Sumbatar wuya na yayi na rike rigar shi, naji sakon har cikin raina. Da sauri na juya ina kallon fuskar shi, lebbena na kasa ya kama, nayi maza na rufe idanuna, ina sauke ajiyar zuciya kamar wacce nayi tsare.

             A hankali ya janye daga jikina, ya juya min baya. Nima haka ce ta faru, na rasa wani irin kunya nake ji, lokaci guda na kasa sake jikina da shi, sai da na kwashe minti goma sannan na mike daga gadon, yaki ya juyo min kawai nace.
"Wasssssh kafana!" Da sauri ya juyo gare ni, kashe mishi ido nayi tare da sake mishi dariya na shige ban daki, sai da na gama na fito.

                    A bakin kofar shiga na same shi, cikin nutsuwa na ture hannun shi zan fita ya dawo dani da hannu ɗaya. Ya hada ni da kirjin shi.
"Ina son abubuwa akanki, sai dai bazan iya ba! Ina da matukar kishi. Ina son kasancewa dake!  Ina kishin ki, bawai dan ina son ki ba, a'ah kawai ina ƙyamar abin da wani yaci ya bari ne."

Mutuwar tsaye nayi domin ban sannan zai iya gaya min magana haka ba, gyada mishi kai nayi sannan nayi wuccewa ta nayi sallah, ina zaune da yar karamar Alqur'ani, malamar jinya tazo ta bashi yace ya ajiye ni yake bukata na bashi. Ina jin shi nayi banza da shi. Da gayya baki kammala karatun dan kar ya dame Ni.

  Shiru yayi shima, ya gabatar da sallar da yake kan shi, wasa wasa har lokacin shan maganin shi ya nemi wucewa, bai ce min kome ba, ran shi ya b'aci dan haka da kan shi ya sha maganin, da gayya naki kula shi, har dare muna nan a gurin.

         Koda lokacin bashi na dare yayi sun zo bai hana matar ba, ya amsa nata, da dare ina kwance. A dogon kujerar dake cikin dakin, sai ji nayi ya d'aga ni cak, zuwa gadon. Buge hannun shi na fara ƙoƙarin yi, amma ya danne ni da kirjin shi, tare da mai damin  hannuna baya, kauda kaina nayi  raina na kara b'aci nace mishi.
"Sake ni!"
"Ba zan sake ki ba, kin zata wani abu zan nima a jikinki? Ko ce miki aka yi zan ratsa hanyar da wasu kartin maza suka bi ne, ni zaki ne, duk abin da zanci mike fara farautar shi, idan na gama na barwa sauran kananun namun daji suci, ke har kin isa kiyi fushi dani, dan na kyale ki, ina wasa dake?

     Wallahi ki shiga hankalinki, ko kuma na baki mamaki, zan miki abin da ko suna na aka kira sai kin rintsa idanun ki, dan haka ki cigaba da abinda yayi miki Bazan hanaki ba."

       Kallon shi nayi cikin wani irin kuka, na buge hannun shi da yake rike dani, na shiga ƙoƙarin ture shi, mutum sai kace bishiyar kuka. Sake danne ni yayi cikin ko in kula, yake azabtar dani. Kuka nake sosai tare da  ture hannun shi, murmushi yayi sannan yace.
"Ina jin kunyar ki sosai! Ki k'iyayye haka, kuma ki bani abinda zanci."

     "Bazan baka ba, kaje ka sami matan da kake so su baka, me zan maka ina sauran wasu." Had'iye kukan nayi sakamakon, (🙈🙊🙉) yunkurin amai nake, amma mara kirki sai da ya tura min bakin shi cikin nawa, kai....kai.. abu dai bai dad'i ba. Domin Jay ya rena ni, sai da ya tara min gajiya sannan ya kyale ni ya sauka daga gadon, ya koma saman kujeran yayi kwanciyar shi. Saboda kuka idanuna har yaji suke min.

Mai da al'amarin babba yayi dan fushi ya dauka dani, sai nima na share shi, ko ya zata bazan iya share shi bane, wasa wasa. Har muka kwana, washi gari ma muka tashi da fushi da juna.
Chapter 67 · 0% Book details