← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 72

Sashe 5

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

              Har zuwa asuba, sai ga Baabi da Ummin suka zo, tare da zama akayi jana'izar Baraq sannan aka kai shi ina kwance ina barci me hade da mafarkin ya rasu, har ina cewa karya ne a mafarkin yanzun yanzun ya gama.

     Buɗe ido nayi ga yan uwan mu, da sauran mutanen. Tashi zan yi na tuna babu kaya a jikina cikin kunya.
"Ummi kayana!"

      Mik'ewa tayi ta bani nasaka, sannan na sauko da kafana daga gadon, kawai naga hatta bargon jini ya b'ata, shiru nayi ina nazarin abin da ya faru, su kuma ganin haka. Sai suka dauka ai jiyan, sai da yayi tarayya dani kafin ya rasu.

         Ban fahimci abinda yake faruwa ba, amma yadda naga suke kallona ya ɗan sani tsarguwa da kaina, a hankali na shige ban daki nayi wanka da alola nazo na gabatar da sallah, bayan an dawo daga kai Baraq makwancin shine Baabi ya nemi tafiya dani, sabida yadda yan uwan Baraq suke faɗa zasu kashe ni.

    Tunda na zama makara, duk wanda ya aureni mutuwar shi ya aura. Babu wanda ya gaya min abinda ya faru, sai da naga suna hada min kayana, anan na fahimci akwai wata matsala. Dan haka na shiga tambayar su, ko ya sake ni ne.

"Ba sakinki yayi ba, Allah yayi mishi rasuwa ne!"

           Kurawa Ammih ido nayi, na kama dariya dariya kamar mahaukaciya, ina nuna su da hannu, zuwa wani lokaci na zube a gurin. Na fara ihu tare da kuka, dakyar Aka fitar dani a gidan,  zuciyar Baabi ta karaya da alamarina.

      Dan haka koda muka isa gidan na kule kaina a daki, sai da Baabi ya ɓalle kofar, shi ke bani abinci a baki. Shi yake kula dani, har na sami watanin da zan gama takaba, daga nan ban kuma sha'awar fita kofar gida ba, kai ko bikin sallah ake bana fita waje.

    Balle kuma wani sha'anin bana zuwa, sabida bayan rasuwar Baraq, anta yawo dani wai mayya ce ni.

              Har takai a cikin Zuri'ar mu, ana zargin na da hakan sai na daina shi, duk da wasu na zuwa gidan mu dan ganin halin da nake ciki,sai Allah ya nuna musu bani da wani damuwa a fuskar sai a zuciyata.

    Akwai Yayar Baabi hajiya Amina,.tana auren Wazirin sokoto, dan tane ya fara nima na, kamar da gaske, dan na fara gudun shi, kawai tasaka aka kirani, koda naje gidan, ina zaune a falon kasa wasu yan mata biyar suka fito, biyu yaranta ne, daya kuma yar kawarta ce. Biyun Kawayen su ne.

       Kasancewar muna wasa dasu, suna zuwa suka zauna.
"A'ah makara kece a gidan?!"
Wani irin muzanta nayi domin a kiraka da makara ba abin dad'i bane.

                        Ciro kaina nayi ina kallon su, sai kuwa suka kwashe da dariya, sannan suka ce.
"Ban da rashin adalci! Taya kin san baki da lafiya zaki amincewa Ya Hisham! Dan ki kashe mana shi ko? Toh wallahi idan baki rabu dashi ba. Kai ku tashi muje,  ga mace har mace ta zama matar mutuwa! Kowa ya aureta sai wani bashi ba."

     Shiru nayi ina me wasa da zoben hannuna, har Yayar Baabi ta sauko Hajiya Amina, kaina a sunkuye, ta zauna.

"Da fatan su Khareema da Loloh sun miki kashedin kar na kuma jin labarin Hisham a cikin gidan ku! Idan kuma kina son a tozarta zumunci ne toh zamu yi hakan."

         Girgiza mata kai nayi, sannan na mike tare da ce mata.
"Sai an jima!"

    "Ki dai k'iyayye abinda nace miki"
     Tunda na fita, dakyar nake takawa, har na isa gidan daki na wuce na rufe kaina, duk sai naji Sokoto  tayi min girma, dan haka nayi kuka nayi kuka a ranar, kamar babu abinda zanyi bayan shi.

      A hankali rayuwata ta zama abin yayatawa, yau saurayi zai zo gobe zai gudu bani kuma ganin shi, haka ya sa. Shiga kunci sosai.

   Domin har nayi dana sanin rayuwata, bani fita bani da kowa sai kanwata Hanisah, wacce muke matukar kaunar juna da ita.

   Sai Muhammad Kabir, shi ke bin Hanisah, shi kuma yaron Ammih ce, sai Janny  ita ke bin shi, kafin Kuma Kazeem, dan Ummi da Hassan da Hussaini, duk yaran ta idan aka cire kabir, Yaran Ammih biyu ne Kabir da Husnah.

         Dan haka idan na shiga damuwa kanena, zagaye ni suke suna masu kwanciya a jikina, suna kuka, yawan damuwar da nake ciki yasa Baabi shirya min kayana zuwa Canada.

              Haka yayi min dad'i sabida inda Zani a Canada, Yan uwan mune! Aunty Fouzia, da mijinta shima Kuma Yayan Mana na ne.

   Suna zaune a jahar Calgary na kasar Canadan, sani a gaba kanena suka yi, wannan yace kaza wannan yace kaza.

   Karshe ni dai kallon su nake ina murmushi me hade da kuka, sabida zanyi kewar su. Tunda muka fito, dayawa wasu sunyi farin cikin tafiya na, saboda kar na zauna y'ay'an su. Suce suna sona.

       Cikin shekaru talatin na rayuwata, na fuskanci damuwa har nake ganin kamar dan ni matsalar take karuwa, sai dai tunda na bar sokoto naji matsalar ta ragu min.

    Baabi da kan shi, ya kaini Canada, mun isa garin Calgary da safe, tun a filin jirgin na fahimci haduwar garin, sannan muna tsaye Aunty Fouzia da mijinta suka zo daukar mu.

  Cikin farin ciki, Yanayina bani da jiki sosai, amma ina da tsayi masha Allah, sannan ina da dan karamin kyau, dai-dai gwargwado, amma ni wankar tarwada ce, bakina yana da dan fadi. Sai dogon karan hanci, bani da manyan idanu, amma yanayina ba laifi.
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

Fatan Alkhairi Fans din KWARKWARAH da MAGAJIN IZZAH ga Pagen ku nan gaisuwar taku ce😍🙈

BIYAR.

Idan nace zan baku labarin yadda garin calgary yake zamu kwana mu wuni ban gama bada labarin yadda garin yake, dan matuƙar haduwa ce, koda muka. Isa gidan wanda yake.

       Preston town, anan motar su Kawu Muddam ya tsaya,  a hankali ya karasa jikin kofar gidan ya tsaya, sannan muka fito. Ina kallon Unguwa, yayi min kyau, musamman iskar da take kad'awa.

               Cikin gida suka mana jagora shi da Umma Fouzan, tunda muka shiga nake kallon yadda tsarin gidan yake, bayan munci abinci muka yi wanka na kwanta kenan Baabi ya turo min yar Karamar yarinyar Umma Fouzan me suna.

      Ablah, da sauri na mike na fita gurin shi.
    "Baabi na gaji ne! Na kwanta na huta."

           Murmushi yayi sannan ya kalli agogon hannun shi yace.

      "Zamu shiga jami'ar Alberta ne, mu gama miki kome zuwa nan da jibi na koma gida!"

   Gyada kai nayi, sannan nace mishi.
"Baabi ko nazo muje ne?!"

       "Idan zaki iya muje mana!"
Murmushi nayi dukda na gaji sosai, amma bana son rabuwa da Baabi na ya sani shiryawa zan fita sai ga Umma tashigo.

"Ba fa inda zaki domin nace su tafi! Ko kunya baki ji ba, ƙatuwar Uwar mata, zaki bishi zokai-zokai toh sai ki kwanta ki huta"

     Tura baki nayi idanuna suna kawo ruwa nace.
"Ni wallahi mutum ba yazo ba, a hana rayuwar shi sukuni."

Dariya tayi, abinta dan mun saba fadar mu da ita. Fita tayi yanar ni, nayi kwanciya ta..

                  ---
A cikin kwanaki biyar suka gama min, kome sannan Baabi yayi min nasiha. Tare da ja min kunne kar naga bana gida nace zanyi abinda rai nake so.

      Naji nasihar shi, amma bazan iya bari a ci min mutunci na kyale ba, dan haka ranar da na cika sati daya, ya koma nima kuma a ranar zan fara zuwa makarantar. Da wuri na shirya cikin doguwar rigar, tare da nad'e kaina. Da farin mayafin.

    Sai takalmina baki shigen kayan jikina. Tare da jakar da nad'ebi abinda zanyi amfani dashi. Na nufi waje inda Kawu Muddam ke jira na, sai danna ansakuwar shi yake.

             Koda na isa waje, na kalle shi a hankali. Nace mishi.
"Kayi hakuri!"

   Kallon agogon shi yayi, na shiga tare da gyara zaman agogona, ina son agogona domin gadon Mahaifiyata ce, dan agogon ta zinari ce hadi da Lu'lu'u, Baabi yace shi ya sayawa Maaminah, lokacin zuwan su, Madina bayan auren su.

     Shi yasa nake son agogon dan yace min, na rike shi da kima. Mun isa makarantar, shi da kanshi ya kai ni har cikin ajin bayan mun biya wani ofishin mun ajiye bayyanan na fara karatu, har kofar aji ya ajiye ni tare da bani wata takarda da zata kaini unguwar da muka fito.

                    ... Bayan tafiyar shi na shiga ajin na zauna, duk da kowa harkan gaban shi yake. Nima na zauna tare da nutsuwa guri guda. Ina kallon yadda suke hidimar gaban su. Dake nima ba ma'abociyar son magana bane, ban kuma  kallon kome da suke yi ba.

Shigowar wani bature, wanda zai dauke mu a darasin lissafi. Ya gabatar da kanshi. Sannan ya fara abinda ya kawo shi, yana gamawa ya fita, a hankali naga daliban nata fita, nima daukar jakata nayi na fito.
Chapter 5 · 0% Book details