Sashe 65
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A sannu ya goge fuskar shi sannan ya fito daga dakin, yana kallon yadda kowa jikin shi ya mutu, fitowar wata malamar jinya da sauri ya katse musu shirun su, taje ya dawo da wani abu a hannun ta, cikin sauri. Duk sai hankalin su ya kuma tashi, cikin bayan awa daya sai ga kukan jariri, sosai kowa ya sauke ajiyar zuciya, suna jiran a gaya musu me ta samu. Fitowar Dr Fatihu. Rike da kayan aiki shi sai wata Malamar jinya rike da Jariri a farin kyalle, yazo ya tsaya a gaban su, ya mikawa Najim Hannu dan dukkan su kowa ya gama tsorata, yace musu..
"Kuyi hakuri bawa bai tab'a kaucewa kaddarar shi, tun ran gini tun ran zane Allah ya baku hakurin rashin da kuka yi Ubangiji ya...".
Sai ganin Jay akayi ya zube.....
*Kunsan ba a mutuwa a dawo 🙄🤨 Allahu Akbar! Aanih Khatoon an rigamu gidan gaskiya shi kenan ðŸ˜ðŸ˜“*
10/23/20, 10:10 AM - Ummi Tandama: *_Mai rabon ganin... Badd'i ko ana daka a turmi ne sai ya kai_*
Kallon Baba Magaji yayi sannan cikin damuwa, sannan yace.
"Ba halin na kawo ta?" Girgiza mishi kai yayi sannan shima yace mishi.
"Dole sai zuwa daren!" Da haka Jay ya hakura har zai fita Baba Magaji yace mishi.
"Ka kula fa! Karka yarda wani damuwa ya karu mata, dan kamar ita ba zata iya boye tata yanayin ba."
  Jinjina mishi kai yayi, sannan yayi tafiyar shi. Tun da ya bar gurin Baba Magaji yake jinjina al'amarin, a hankali ya nufi gida shi da Najim, tun da ya shiga d'akin shi na zaure, ya jima bai fito ba har kusan karfe ɗaya na rana, sannan ya fito jikin shi a sanyayye, zama yayi yace.
"Ku bani ruwa na sha" Matar shi ta mike ta kawo mishi, tunda ya sha ya dauke ajiyar zuciya sannan ya kalli matar yace.
  "Ziryana ta mutu bata zauna a kujeran mulkin ta ba, Jannart ta rasu bata samu damar zama haka ba, tare da burin Jannart ta kawo sauyi! Yau gashi Fatimah itace ta sami damar zama a kujeran, yau rayuwar ta, yana cikin hatsari." Ya faɗa a sanyayye,
"Allah ya kawo musu mafita!" Inji matar shi, haka ya zauna yaci abinci, kafin ya nufi masalacin, tun biyu da ya tafi bai dawo ba, sai la'asar sannan ya kuma shiga dakin shi yau ko Daliban shi bai samu lokacin su ba.
    ---
Ina idar da sallah asuba, barcie nauyi ya dauke ni ko addu'o'in ban yi ba. A hankali na bude idanuna na ganni a wani daki me dauke da wata irin gado na alfarma, cire kaina nayi daga matashin da nake kwance na tashi zaune, gadon dauke yake da wani mayafi ja. Tun kafin na sako kafana da sauri wasu yan mata masu sanye da fararr kayan sun tashi tare da bude labulen gadon, kallon su nayi dan kyau ban tab'a ganin mata masu kyan su ba, domin su hadu ne na karshe.
    A hankali na zuro da kafana, suka yi maza suka zuba min wasu kyawawan takalma, tare da wasu irin fure me kamshin dadi. Sannan suka mike, wasu yan mata uku suka kawo wani yadi suka lullube ni dashi, tare da d'aga min hannu suka zare min rigar jikina.
   Kafin suka daura min yadin, a jikina suna masu cewa.
"Sarauniyar mu! Mun gama umarnin ki muke kira!"
"Wanka" nace musu, bude min hanya suka yi sannan suka shiga min jagora har gaban wani ban daki, jan wani kujera suka yi sannan suka sani na zauna a hankali, kafin suka wuce ban É—akin. Tun daga wajen nake jiyo kamshin turaren miski, suna gamawa suka fito tare da cewa.
"Mun gama!" Kafin na mike sun rike hannuna, muka nufi ban ɗakin, muna shiga suka juya min baya a Sannu na sake zanin jikina sannan na shiga ruwan na zauna. Kafin suka juyo nan suka shiga goge min jina suna wanke min kaina, har muka gama sannan suka kuma rufe min jikina.
 "Aanih! Aanih!! Aanih!!! Tashi daga barcin ya isa haka, kinji." Ya fada tare da d'ago kaina jin kamshin tare da jekar da gashina yayi ya sashi zuba min ido, sake tab'a ni yayi na bude idanuna naga babu kowa daga ni sai shi.
"Jay ka daina tafiya kana barina! Tsoro nake ji." Daga haka na kuma bigewa da barcin, wunin yau baki daya. Zan iya kiran shi da a mafarki nayi shi. Dakyar Na samu na tashi zan yi alola da wanka ina shiga ban dakin naga har an zuba min kome, shi kanshi ban dakin kamshi yaƙe.
    A hankali na fara wanka, kafin na goga sosa zanji an goga min, tare da zuba min ruwa, ga wani irin tsoro ya kamani, a daddafe nayi wankan sannan na yi alola na fito, ina idar da sallah azahr na zauna dan yanzun bana son kwanciya kar na fara mafarkin.
   Bayan isha ya sani na shirya ba tare da na kalle shi ba nace mishi.
"Zaka kai ni gurin Baba Magaji ko?" Juyowa yayi cikin nutsuwa da mamaki akan fuskar shi.
"Taya kika san da haka?" Ya zuba min ido tare da tambayana na,
Sarawan da kaina ya fara ne ya sani, jin wani irin jiri zan fadi.
"Fatimah!" Ya shiga jijjiga ni, dakyar na bude idanuna nace mishi.
"Ni bazan je gidan Baba Magaji ba"
Daure fuska yayi, sannan ya dauke ya ajiye ni a gadon ya saka min hijab, kafin ya tallafo ni muka fita.
"Jay! Ka mai dani gida! Babu inda zani!" Na gaya mishi a hankali.
Banza yayi dani, na dinga rokan shi amma bai kulani ba, har muka isa gidan Baba Magaji, tun a zauren gidan nace bazan shiga ba. Da karfin gaske ya dauke ni muka shiga kokuwa da shi, har cikin gidan ya dire ni.
"Ko da ka kawo ta nan, an ce maka kome zai sauya ne? Tabbas rayuwar ta na mune! Kuma ka saka ido sai mun dauke ta" ina gama fadar haka na zube a jikin shi kuma.
Nuna mishi gurin da zai kwantar dani baba Magaji yayi sannan ya kalle shi.
"Me ka Fahimta akan ta?"
Lashe bakin shi yayi sannan ga gyara zaman shi yace.
"Ban fahimci kome sai dai na san tana fama da irin wannan matsalar, haka Baban ta ya gaya min."
Kallon shi Baba Magaji yayi sannan yace mishi.
" Matsalar daga gare ka ne! Kai ne mafarin matsalar ta, shekaru ashirin da takwas, lokacin Mahaifiyarka tazo min nan domin dakatar da matsalarta."
(Mu koma Kwarkwarah)
---
"Baba Magaji! Nazo ne akan sha'anin Ziryana da Fairo! Baba ina son a dakatar da wannan bibiyar da suke min, ina tsoron kar su juye kan cikin jikina, bana son matsalar da na samu abin da zan haifa ya fuskanta."
Ta kai aya cikin kuka, tausayin jarumar mace irinta ya sani daukar kasadar cewa.
"Ki je gida zan nime ki nan da jibi!"
Bayan tafiyar ta, na shiga dakin ibada na, na jima sosai har ta kai da mun yi magana da su wad'ancan mutanen, abun da suka gaya min ya bani tsoro.
"Magajin Malam! Zamu iya hakura da ita, amma ba zamu hakura da abun cikinta ba, ita bata da hurumi da mu, sabida abinda zata haifa shine zai zame mana abinda muke bukata.
Ai ita kan fanko ce! Koda mun dauke ta ba lallai tayi nisan kwana irinta mu ba, da ace Ziryana tana raye ba zamu bayyana kan mu ba, zamu cigaba da zama da ita, amma bata nan kuma gangan jikinta yana cikin masarautan ku, dan haka kuyi kokarin sanyawa kanku hakuri domin kuwa mu ai mun gama kome namu saura abin da zata mahaifa muke jira."
Na tausaya mata, domin tana matuƙar son abin da zata haifa, dan haka na roke su da karsu taɓa abin da yake cikin. Dan haka nayi ta faffutikar ganin cewa na dakatar da wannan matsalar amma bai samu ba, daga baya tazo min da wani batun da ya bani tsoro. Ranar da ta gaya min nima sai da nayi jinyar kwanaki sabida wahalar da nasha a hannun mutanen boyen da suke tare da ita.
Daga haka na ajiye, batun na zubawa sarautar Allah ido."
..... Shiru Jay yayi, kafin yace.
"Meye wannan abun?"
Shiru Baba Magaji yayi sannan yace.
"Dole sai an ture katangar ganuwar da take gidan bayi, tare da.."
Tari ya fara yana kakari, sabida shake shi da Aanih tayi, dakyar Jay ya kwace shi a hannunta, nan ta kuma dawowa kan shi shan gabanta yayi.
"Karki tab'a shi! Idan har ni ne zan iya kawo karshen rikicin masarautan na yarda kashe ni!"
Zuɓewa tayi a gurin, ta koma barcin ta, sannan ya koma kan Baba Magaji, ya dauke shi ya fito dashi cikin gidan, kafin ya fito gurin Aanih. Sai da yayi musu bayanin sannan ya fito gurinta. Abin mamaki babu ita babu dalilinta.
Da sauri ya leka waje, ya ganta a zaune, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya zo gurinta yaga tana kallon sama,, rike hannunta yayi yaji yayi mishi mugun sanyi. Da sauri ya sake ta, yana kallon yadda take zaune bata kalle shi ba.
"Fatimah! Muje gida!" Ya fada mata a hankali, mik'ewa tayi suka fara tafiya, a sanyayye suna isa Munih tana fitowa daga dakin ta.
Kau da kai tayi tare da jan tsaki, zata bar gurin, cak ta tsaya tayi tayi juyawa tayi, abin mamaki Aanih ce a bayan ta, "ki godewa zuciyarki da bata kai ki ga aikata shirme ga Sarauniyar mu ba, da yau sai kin haifi abin cikin ki bai isa Haihuwa ba."
.... Daga haka ta koma hanyar sama, tana ganin kulewar Aanih sannan taji kafarta an sake shi.