← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 72

Sashe 25

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda na haifeta ka rage shiga cikin mu, kawai dai kana taimaka mana da renonta, har zuwa lokacin da ta fara tafiya, Jay sai da ka shekara sha shida kafin muka san cewa kana magana kawai baka cika surutu bane, ka taso baka da kiriniya baka shiga hidimar yara, ko a makarantar ku. Malamai suna fada cewa kaina rayuwa ne kamar Basarake.

Baka son reni, kuma baka rena kowa, a shekaru sha bakwai, ka kammala sakandare. Lokacin an dawo damu nan Canada. Baban Munih yaso kayi soja kace kai likita zaka yi.

Dan haka ya kyale ka, shekara ashirin da hudu cik ka gama matakin farko na digirin ka, daga nan kuma, muka so gaya maka waye kai sai muka fahimci kana farin ciki da yadda kake rayuwarka, dan haka muka bar maganar bamu ne muka haife ka ba.

Abun da muka so shi kake mana, dan haka muka sanya ka koma mataki na biyu na digirin ka, tunda a bangaren da ka karanta, duk wannan abin da muka yi shine zaka saka mana da lalata mana Yar mu? Mun gode amma zaka iya tafiya tunda mun gaya maka waye kai zaka iya tafiya don Allah ka bar mu karka lalata mana rayuwar ta."

Ta karshen maganar cikin Kuka, da ban tausayi.
"Bani da inda yafi nan! Amma dole zan tafi naji me yasa aka min haka, nagode kuma ina baku hakuri da abinda nayi muku."

Daga haka ya fice daga gidan baki d'aya, tafiya yake da kafa. Idanun shi jajjur. A wani ƙwana suka haɗu da Najim!

Inda suke ta tafiya a tare.
"Saraki!"
Juyawa yayi tare da kallon Najim, mai da hankalin shi yayi gaban shi, har zuwa wani shagon coffee. Zama suka yi Jay yace a bashi coffee me zafi, Najim yace a'a me sanyi dai.

"Saraki! A yadda kake a tafashen nan idan ka sha ruwan sanyi, yafi na zafin da zaka sha. Ai sai ka iya tadda gari guda."

Bai ce kala ba, haka ya cigaba da shan shayi me sanyi, har suka gama Ya mike zai tafi.
Najim yace.
"Ranka shi dad'e! Idan aka cigaba da haka wallahi muna cikin wani yanayi, ka taimaka min na samu gurin fakewa."

Iska yaja sannan ya zuba mata ido, yace.
"Ina cikin damuwa!"
"Na sani, amma al'ummar daura da Mahaifinka tare da kakanni ka, suna zuba ido tare da saka tsammanin Magajin Izzah!

Ban san me yasa kowa yake dauki da son ganin ka ba, amma Shehun Borno da wasu daga cikin dangi suna maraba dakai, Sunana Brrst Najim Aswad Magaji, ni ne lauyan masarauta.

Da fatan zaka Duba alamarina. Ga takardan jirginka bazan iya zama na wasu lokuta ba, idan ka shirya jibi zamu sauka a Lagos."

Cikin hasala ya kalli Najim,
"Umarni kake bani?"
"A'ah Saraki! Abinda ya dace nake, Saraki tun ranar da ka b'ata nake tare da Abba Jaamal, dan bana son ya duba gurbin ka, ya ga baka nan, idan kayi ra'ayin tafiya shi kenan, amma zukatar mutane suna dayawa akan ka. Sa ran su yayi matukar tasiri akan zukatar su.

Ya zaka ji labarin Jarumar Uwar da ta tabbatar da kaine zaka kawo karshen rikicin masarautan da Insha Allah, faffutika tayi tare da sadaukarwa. Ko kasan ciwon da miji yake ji a lokacin da ya rasa matar da yake matukar kauna! Sannan abin da tabar mishi aka wayi gari ya b'ace, ka san nauyin da zuciyar Wannan uban yake dauke da shi.

Ka duba yadda duniya take, ka dubi yadda kowa yake tattalin abin da yake na shine.

Zaka iya rasa yau a rayuwar ka, amma gobe idan kayi ƙoƙarin gano bakin zaren zaka rike shi da daraja. Mu ahalin sarauta an san mu da tsage gaskiya,.tare da fadar ta, bama gudun abokan gaba. Domin da su aka halicce mu, abinda muka sani zartarwa.

Hukuntawa, adaltawa Dai-daiton laifin tsakanin talakawan mu da attajiran mu, don Allah idan kana son Ahalinka su kare rayuwar su cike da kunya bismillah idan zaka iya zuwa ka tsayawa mutanen da suka saka rai. Da zuwan ka, koda yaushe mafarkin su Magajin Izzah zai dawo. Ashe ba haka bane domin sarakin da nake gani a gaba na lusari ne."

A fusace ya makure wuyar Najim.
"Toh idan har zaka iya fusata kamar yadda kayi a nan. Saboda kimar ka ka bi mace har nigeria, toh lallai Jarumin da ya wurga yarinyar nan wancan ranar a cikin kashin dawakai! Ya kuma sake nasarar sanya ta cikin kashin aladu.

Wannan jarumin da ya kalli idon Sa'i yace mishi ya kiyayye harshen shi da fadar magana ga mahaifin shi, ba tare da yaji d'ar ba. Toh gobe da karfe biyu na yammaci ina jiran shi a tashar jirgin sama, nasan Saraki baya sab'a magana, amma naga isa da ikon nan da na sani a da. Ina nan ina jiran mai martaba sarkin Daura."

Daga haka ya dauki rigar shi ta sama, ya bar inda Jay yaƙe. Yana tsaye kamar bishiya. Tsigar jikin shi mik'ewa yake.

Wani irin jin kai tare da Izzah musamman wanda yake cikin kowani jinin sarauta, cikin ƙasaitar da bai zaci yana da ita ba yake tafiya, tare da wani irin yanayi wanda yake cike da mulki tsantsar ta.

Koda ya isa gidan. Ganin kowa yayi shiru, suna ta harkokin su, sai dai Munih da take bin shi da ido, har ya shige dakin shi, bai kuma fitowa ba.

.....
Har washi gari, yana dakin ya gama had'a kome nashi, sannan ya fito da manyan jakukkunan shi, tare da kallon agogon hannun shi, karfe biyu saura minti sha biyar.

Koda ya fito ya same su, suna cin abincin rana. Zama yayi har suka idar yana yi yana kallon agogon hannun shi, tare da sake murmushin takaici, dan ya fahimci sabida shi suke kin gamawa, amma bazai iya barin su ba, zai zauna dasu. Har su gama.

Koda suka gama kowa kama gaban shi yayi zai tafi yace musu.
"Ku dakata mana!"
Cak suka tsaya, kwaso takardun shaida karatun shi yayi, sannan ya mikawa Baba furofesa, ya mika mishi, kafin yace.
"Nayi Kuskure, kayi hakuri ka amshi ban hakurina, gasu kaine ka bani so cikin so da kauna, yau na dawo maka su a matsayin tsintaccen nan.

Nasan nayi kusakurai masu yawa, amma ina rokon Allah ya baku hakuri, zan tafi naga Ahalina Insha Allah zan dawo saboda shagona da yake nan, Bama iya shi ba, sabida ku zan dawo.

Nasan nayi laifi me girma, don Allah ku yafe min."

Daga haka yaja jakunan shi zai fita, da mugun gudu Munih ta rungume shi tana faÉ—in.
"Wallahi mutuwa zan yi idan ka rabu dani, don Allah ka dawo ina sonka."

Janye jikin shi yayi bai kuma sauraronta ba, ya fita abin shi ihu take tare da cewa a dawo mata da shi, shine abokin rayuwar ta,.

.........

Karfe biyu saura minti biyu, Najim ya hango shi, yana shigowa, cikin sauri ya isa gurin shi tare da rungume shi. Mara mutunci. B'ata rai yayi kamar ba shi ba.

Har inda aka duba kayan shi, sannan ya wuce abin shi suka nufi cikin jirgin.

----
Abuja..
Tunda Aunty Aina'uh ta zo min da maganar d'an mijin kawarta, naki bata fuska. Har dai ta gama damuwarta sannan ta kyale ni, yau da wuri na tashi sabida ina Son na fita, naje na duba mai na da sabuluna, sun kusan karewa.

Sosai na shirya sai dai fuskana babu kwalliya, sai man baki da na saka, ko kallon inda Aunty Aina'uh take banyi ba, nacewa karamar yarinyar ta, dan itama Aunty bata haihu da wuri ba, kuma tsakaninta da Maama wato Mamana shekaru uku ne, sai da ta shekara sha takwas, kafin Allah ya basu Haihuwa.

Babban yaron yana makarantar king Abdul Azeez riyadh, sai kuma wacce take bin shi tana nan turkish, na abuja.

Sai wanna yar karamar wacce taci suna Mamana, suna kiranta da Hanan. Dan haka na riko hannunta tare da janta muka fita.

.....
Sahad store muka je, Nan na sayi kayan amfani na, muka nufi gurin biyan kudi.

"Kowa yafita ga dan gidan ministan Abuja zai sayi kaya!"

Lokaci guda mutanen cikin, shagon suka fara fita ban dani da na ke biyan kudi.
"Ke wacece da ba zaki fita ba, ana magana."

Mikawa matar katina nayi, sannan na kwashi kayana tare da riko hannun Hanan, zamu fita. Kamar ance na d'aga ido na, sai akan Asood. Ban yi mamaki ba.

.kawai nasaka kai zan fita ya tsare hanyar fita, cikin isa ya iso gabana.
"Karuwar mu!". Rintsa idanuna nayi tare da kawar da kai na.

"Ina abokin ciniki ki? Koda yake naji ana min tayin auren wata bazawara, amma bazan ki tayin ba. Idan na duba yadda ko ina yake cike tam!"
Ya kai hannun shi kamar zai tab'a ni nayi baya, cike da bakin ciki.

.. ..".karki damu! Zan zo har gidan na kwashi rabona abin da Jay ya bari zan tattaro na karasa"

Takowa yayi gabana, tare da min kallon kaskanci.
"Karki manta nan ba Calgary bane! Nan birnin tarayyar mu ce! Muke fada muke yadda muka so!

Kudi mulki Izzah mun gaje shi, ki kalli Asood Ahmad Buba Yaro kika mara, idan zaki iya ki fara gudu, karki tsaya karki tsaya karki tsaya, domin sai na jiyar da ke, zafin da bazaki iya kwatanta ya yake ba.

Sai na gama miki azzabar da ba zaki iya kwatar kanki ba, kina da sauran lokaci, na gudu ki nime matsirata. Sabida shi wancan da na turo ya kasa min yadda nake so!

Fatimah Khatoon fara gudun ceton rayuwarki.
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:55 AM - Ummi Tandama: Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300â‚? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar.....

*Cusa Kai*

"Ba zan tab'a gudu sabida kai ba! Ba zan nemi maboya sabida kai ba, abinda na sani Allah yana tare da mai gaskiya kai baka isa kayi min abinda bai min ba, kai ba kowa bane facce mujirimi, baka isa ka tozartani ba, sabida Allah ya kare mutanen da suka yi imani da shi.
Chapter 25 · 0% Book details