Sashe 22
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wanda aka wurgo Asood ya shigo, ganin halin da take ciki ya sashi juyawa da sauri, yana faÉ—in.
"Jay! Me ka aikata haƙa? Ƙanwarka ciki d'aya itace ka haƙewa, haba Jay!"
.wani irin firgici ne ya kuma cika zuciyar shi, a take ya juya da sauri yana son yayi mishi bayani ya dakatar da shi, yana faÉ—in.
"Amma kasan Ni nake sonta? Shi ne É—an bakin ciki, ka raba ta da abinda nake burin samu a jikinta! Toh ka sani ban yafe maka ba! Kuma daga yau babu wata aminta a tsakanin mu!
Kuma sai na gayawa kowa ya san abinda ka aikata min."
"Don Allah ka saurare ni? Ka. Fahimci abinda zan gaya maka, bana cikin hankalina nayi a..."
"Fitar min a gida! Nan kayi ta ihu sai ka lalata min rayuwar Khatoon! Ashe ba nata zaka lalata ba, rayuwa na zaka lalata me zaka gaya min maciyi amana, haka kaje ka dawo baka rama min ba."
"Asood! Ban aikata kome ba, batun Aanih kuma ka ajiye a gefe! Wallahi ban aikata kome ba, Aanih ta fito daga cikin babban gida ne! Matukar na tab'a wani abu da yake kimarta toh kamar na tab'a kimar masarautar suce, shine masarautar ta uku mafi kafuwar tarihin musulunci a kasar hausa! Don Allah karka min haka.!"
"Kai jin ka zan zuba maka ido ne bayan ka lalata min rayuwa, wato nice mara daraja! Aanih kuma itace mace mai daraja!
Nagode da ka fada min bani da daraja! Asood kaga sonkai ko? Dake ba iyayena suka hai....."
Shiru tayi tare da rab'a gefen shi, zata wuce ya dawo da ita sa karfin bala'i!
"Me kika ce? Gaya min me kika faÉ—a? Me naji zaki ce? Wato dan ba iyayenki bane suka haife ni ba ko?"
Wani irin tsoron shi ne ya kama su dukkan su...
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!
  {CIGABA KWARKWARAH}
  *HAZAKA WRITER'S ASSO*
   (HWA)
*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*
Mallakin
 Mai_Dambu
Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺ï¸
SHA BAKWAI.
Kafe su yayi da ido, a sannu ya riko hannunta suka fita tun kafin ya isa inda motar shi take jefata yayi cikin tashin hankalin.
A da yana jin zai iya magance matsalar shi, amma jin abinda Munih ta faÉ—a ya kuma sanya mishi tashin hankali sama da wanda yake ciki, domin bai tab'a kawowa kome zai lalace mishi lokaci guda ba. Taya ma haka zai faru? Bayan shi.
Dukar motar yayi cikin tsawa.
"Ki min shiru" ya daka mata tsawa, had'iye kukan da take yayi cikin tsananin tsoro, tana kallon shi har suka isa gida.
Kuka take, ga baki daya baya cikin nutsuwar shi dan haka bai damu da halin da take ciki ba. Yazo ya fincikota tare da nufar cikin gidan da ita, Sai dai duk da wannan wulakancin ya samu.
Baban su da Maman basa nan, dakin shi ya wuce tare da barin Munih a falo, itama ta lallaba ta shige tare da fad'awa ban daki tayi wanka.
....
Tunda ya shiga cikin dakin shi, ya zauna yana nazarin abinda ya faru. Tare da girmama laifin da Munih take zargin shi ya aikata. In dai zai iya hakuri bai tab'a kusanci Fatimah Khatoon ba, toh baya jin zai iya aikata abin da Munih take zargin shi.
Tafka yake yana kuma warwara, mik'ewa yayi tare da safa da marwa.
Karshe ya zube a gadon tare da zuba tagumi yana nazarin tashin hankalin da yake ciki, idanun shi ne ya sauka akan kofin madarar da Munih ta kawo mishi, cikin nutsuwa ya isa gaban kofin ya dubi kofin da kyau. Sannan ya ajiye shi dan bai ga abin da yake nima ba.
Yana jin an buɗe kofar d'akin shi, bai kai da ya juya ba, ya cigaba da abin da yaƙe.
"Ya Jaheed!"
D'aga mata hannu yayi tare da nuna mata hanyar fita! Sannan ya cigaba da kallon madubin. Yana kuma hango iyakar kamar da suke da mutane biyun da ya gani a nigeria, indai har zasu iya samun shi a matsayin d'an su, ya ga kuma tarin soyayyar da suke mishi a kwayar idanun su, tabbas. Har abada ba zai tab'a rasa mutanen da zasu yi kuka bayan mutuwarsa ba.
"Ya Ja...."
D'ago kai yayi cikin nutsuwa, ya zuba mata rinannun idanun shi. Tunda taga haka da sauri ta juya zata fita. Bai damu ba har ta fita.
Hannu bibbiyu ya saka a kan shi, yana me jin haushin abin da tayi mishi (😒🤣 dan banza me halin gado)
---
Sokoto...
Wani irin zazzaɓi ne ya rufe ni, tun bayan fitar su Baabi. Nake kwance a kasa, ina shashekar kuka.
Ina ji ina gani, sun kasa bani abin da nake so.
Wuni nayi a d'akina ko waje naki fita, Abinci kuwa da Kan shi yake kawo min, ina kwance sai ga Aunty Aina'uh tazo.
Kanwar Mahaifiyata ce, kauda kai nayi naki kallonta, domin babu abinda zasu iya min a wannan lokaci. Kura min ido tayi na wasu lokuta kafin tace.
"Yarinya!" Yarinya suna ne da suke kirana da shi, sabida Sunar kusan kakata mace wacce ta haifi Mahaifiyata itama Fatimah ce, haka ma Umman Baabi itama Fatimah ce.
Shi yasa suka tsayar da Yarinya kawai kira na dashi dashi.
Kuma bayan haka Ita kakata da ta Haifi Mamana, Kanwar Kakata da ta Haifi Baabi ne, haka ma Dattijo Ƴaƴan kaka na ne.
Tsura mata ido nayi, sannan na juyar da kaina.
"Ki shirya kayanki, zamu koma Abuja dake"
Juya mata baya nayi tare da cewa.
"Babu inda zani, sabida na san Jay zai dawo."
"Ai kuwa, da kin cire yaron nan a ranki domin babu wanda zai bashi ke, sabida babu aure a tsakanin ku"
Mik'ewa nayi zaune ina kallon ta. Cikin jin haushi nace.
"Ba zaku ba shi ne ba? Akan me ne? Gani nai rayuwata ce, kuma ina da yadda na tsara.
Dan haka duk abinda zaku yi sai dai kuyi hakuri amma kamar na sami Jay. Kuma babu inda zani,"
Kura min ido tayi sannan ta fita ranta a b'ace, ina zaune Baabi ya shigo cikin b'acin rai yana kallona. Sunkuyar da kaina nayi.
"Shirya kayan ki, zaki tafi abuja."
Ya faÉ—a min cikin tsawa, a matukar tsora ce na hada kayana ina share kwalla.
"Baabi na!"
"Fito nace"
"Amma Baabi.... Id.."
"Fatimah bintu Zahrah." Cike da mamaki nake kallon shi, kwalla na zuba min daga Idanuna.
"Daga yau kar na kuma jin sunan Jalal a bakin ki, idan kuma na kuma jin wani abu makamancin haka! Toh Insha Allah zan baki mamaki, na fasa aurar dake ne, sabida wasu dalilai. Kije kema ki samu nutsuwar zuciya.
Idan Jalal mijinki ne, wallahi duk inda kike zai zakulo ki, idan kuma ba mijin ki bane, Allah ya baki wanda ya fishi. Bana son kina kuka akan d'a namiji, sai naga kamar na kasa amsa sunar Ubane"
A hankali na isa gaban shi, nace.
"Baabi, idan na tafi zaka yi farin ciki ko? Toh zan tafi. Kuma zan rufe batun Jay!"
Dafe kafad'ana yayi cikin jin yace.
"Dakyau Sarauniyar Aanih muje ku tafi."
A sannu muka fito, Baabi yana bani labarin abin da ya shirya min, murmushi nayi tare da goge jinin da yake d'iga daga hancina, dan ya zame min jiki zubar jinin daga hancina, kuma ina kan magani.
"Wallahi yau naji zafin abin da Yarinya tayi min, dan nace ta shirya kayanta zamu tafi Abuja sai ya zama laifi. A gani na wannan damuwar da kike ciki, har da rashin dumin uwa, dan da Yaya Fareedah tana raye ba zaki zauna kina hauka akan Yaron karami ba.
Kin zauna kina kuka akan shi kina asarar hawayen ki, gaki kamar babba a ido, amma shirmen ki yafi karfin ki, sakarya."
Masifa take tare da watsa hannunta kamar zata buge ni, haka ta gama jarabar ta ban kulata ba.
......
Har bakin motar da zai kai mu tashar jirgin sama,Baabi ya raka mu.
Tunda muka shiga na juyawa Aunty Aina'uh kai, naki kula ta. Tayi mita tayi masifa, kai karshe ta watsar dani bata kuma bin ta kai na ba.
Har muka isa tashar jirgin, bayan wasu mintuna muka bar garin sokoto.
---
Kwantogora...
_"gadon hari sai fana! Ramin kura sai Y'ay'an ta, wutsiyar raƙumi tayi nesa da kasa, tauraruwa me wutsiya! Ganinki babu Alkhairi! An gaida Uwar makirai! Shugabar munafukai! Ranki shi dad'e Fulani Hasiyah"_
Duk wannan kirarin wani tsohon mutum ne yakewa Fulani,, zama ta gyara cikin Izzah tare da zuba mishi ido, tayi tana watsar da hannunta.
" Fawa biu tana ɓata hankalin kuɗa"
Dariya mutumin yayi sannan ya cigaba da cewa.
" Allah ba ya ba gwanni'n tona tsaba. Dan haka dukkan ku lokacin ya karato!"
Wani irin kallo take mishi, tare da kura mishi ido.
"Me kake nufi?" Ta faÉ—a da mugun karfi.
"Idan rana tafito tafin hannun bai kare ta! Duk yadda kike tsammaci abin ya zarta haka! Shi daya jinin shi a tafashe yake."
Murmushi tayi cikin mamaki sannan tace
"Ai ba domin tsawo a kanga wata ba, Ka fahimci hak?"
Dariya ce ta kama shi sannan ya kalleta kafin yace.
" A yi, a gamma, ta fi takamma, gobe a koma."
Cikin jin haushi abinda bada yake gaya mata tace.
"A dade a nayi saikaskiya, karya fure take bata yaya, dan haka nayi da wanda suka zarta Jaamal. Balle kuma Ubanshi!"
Girgiza kai yayi sannan ya fara magana cikin budadd'yar murya yace.
"Tabbas! Gamayyar halittar shi sak take da halittar mutanen b'oye! Shi kan shi har yau bai san kan shi ba, karki kuma sakewa ya cimma matsaya akan kan shi! Matukar haka ya faru! Toh tabbas a cikin ido, ake tsawirya."
"Kana nufin akwai abin da zai razana ni ne?" Ta tambayi mutumin.
"Ashe ana tsoron inna? In ji 'ya'yan mayya! Me yasa kika razana? Bayan ke kanki baki da hanyar kare kanki, kiyi mubaya'a, domin shi ba gama garin mutane bane! Murucin kan dutse ne!" Ya gaya mata haka cikin nutsuwa ba tare da yaji kome ba.